MAGAN JARI CE LITTAFI NA DAYA
labari na ashirin da 1
Kowa Ya Yi Kokarin Ya Sami Fiye Da Abin Da Allah Ya Nufe Shi Da Shi
Kowa Ya Yi Kokarin Ya Sami Fiye Da Abin Da Allah Ya Nufe Shi Da Shi, Ya Ja Wa Kansa Lalacewa
Domin wai akwai wani masassaki a Katako, yana da ‘yarsa mai shekara biyar da haihuwa, sunanta Halima. Ko da ya ke an san yaro a kan son tambayar kome ya ji ko ya gani, duk da haka son tambaye-tambayen Halima sun wuce kima.
Wata rana da safe uban na zaune na sasakar wata kujera sai Halima ta shigo, ta ce masa “Baba, inna ta ga mussa ta ce mata kyanwa, ashe ba ta san sunanta ba, ko ta sani ke nan?”
Kafin uban ya bayyana mata da mussa a kyanwa duk daya ne, sai ta sake masa wata tambaya, ta ce, “Baba, kawu ya ce wai akwai giwa na yawo nan sama, ita ce ke yin fitsari da damina muna cewa ruwan sama, gaskiya ne?
Uban ya fashe da dariya, zai bayyana mata ba gaskiya ba ne, sai ta ce, “Baba, wai kai ma inna ce ta haife ka?”
Uban ya ga za ta hana shi aiki da surutu, sai ya ce mata, “Fita waje can ki yi wasa da yara, sai in na kare ki dawo.”
Sai ta tashi ta ruga. Tana fita, sai ta ji yara na bin wani wada, suna cewa, “Malam Dogo, Malam Dogo!”
Halima kuwa ko wane karambani ya ja ta, da ganinsa sai ta tsaya daga kofar zaurensu, ta ce, “Malam Dogo, Malam Dogo, ka zo, baba na kira.”
Malam Dogo da ya ji haka sai ya nufo zauren. Halima ko ta ruga zaure wajen ubanta, ta rungume shi tana kuka. Tsammaninta wani dan sanho da wadan ke rataye a bayansa duk ba kome ciki sai ‘yan yara kamarta. Malam Dogo ya zo, ya durkusa gaban masassaki, ya ce, “Ga ni, ‘yar matan nan tawa ta ce kana kirana.”
Masassaki ya kawo sadakar abinci da goro da kwabo, ya ba shi, ya ce, “Tun da Halima ta kira ka, ai lalle in sallame ka.” Malam Dogo ya yi godiya, ya bude sanho ya fitad da wata ‘yar nakiya da aka ba shi sadaka, ya mika mata, ta ki karba, don ita ce gamuwarsu ta fari.
Daga ran nan kullum kuma in zai wuce sai ya biyo ta zauren gidan, in ya ga Halima a waje ya ba ta dan wani abin da ya samo sadaka. Tun tana gudu, yau da gobe har ta saba da shi, ta rika tsayawa tana karba.
Da ya gan ta dai saiya zauna, ta hau bias kafarsa suna wasa. In ta fara irin ‘yan tambayoyin nan nata na yara, sai shi kuma ya rika ba ta amsa irin yadda ya kamata. In ta tamyabe shi, “Me ke cikin sanhonka?” Sai ya amsa mata, “Tuwo da nama da sukar.” In ta ce, “Ina innarka?” Sai ya nuna ungulu ko shirwa, ya ce, “Ga ta nan tana tashi.” Sai su bushe da dariya. Duk sa’ad da yarinyan nan ta ga ungulu ko shirwa sai ta ce, “A! Ga innar Malam Dogo.” Ta dubi uwarta, ta ce, “Inna, ke ba ki iya tashi kamar innar Malam Dogo?” Uwar ba ta ko kulawa da ita in ta fara tambayarta.
Suna nan haka, ashe wadan nan wani mai sihiri ne, ba a sani ba. Ran nan sai ya zo wurin masassaki dauke da ‘yan kayansa Halima ta tambaye ka inda na ke, ka ce ni ma na yi fiffike na tashi kamar innata, don kada ta yi kuka. Kullum ku ce mata zan dawo gobe.”
Masassaki ya yi bakin ciki, don ‘yarsa ta rasa abokin wasa. Ya shiga gida ya dauko wata tsumman riga, ya ba Halima ya ce ta kawo wa Malam Dogo a zaure. Yariyna ta jawo riga da gudu, ta kawo masa. Ta fada jikinsa tana murna.
Malam Dogo ya dube ta, duk idonsa suka cika da hawaye domin sabo. Ya zauna nan har margariba. Da suka yi salla, ya ci abinci, sai ya kira masassaki, suka fita bayan gari, suka yi tafiyar kamar loko guda cikin daji, sai suka kai ga wani dutse. Da suka isa, wada ya dubi masassaki, ya ce, “Ka san an ce soyayya gamon jinni ce, ko ba haka ba?”
Masassaki ya ce, “Hakannan ne.”
Wada ya ce, “To, tun da na zo garin nan, ban ga wanda jinina ya hadu da shi kamar ‘yarka ba, Halima. Tun da tana tsorona, har ka ga yanzu ba wanda ta ke so da gani irina. Kome ta ci ta rage mini. Kai kuma kana yi mini alheri iyakar gwargwado. Saboda haka ni kuma zan saka maka. Ko da ya ke kana ganina haka a wulakance, don in jarrabi mutane shi ya sa na wulakanta kaina. Nan kasar duk kafin ka sami wanda ya ke al’amari da aljanu kamata, ka dada.” Ya tsuguna ya tara ‘yan hakukkuwa, ya debi ganyayen kan dutse, ya yi turare.
Masassaki ya rike baki ya ga al’ajibi. Da hayaki ya tashi, sai Malam Dogo ya dubi dutse, ya ce, “Fayau, bude dutsen kudi!” Nan da nan sai dutse ya bude. Da budewarsa sai Malam Dogo ya dauki wata ‘yar fitila nan rataye cikin dutsen, ya kunna. Masassaki ya duba cikin kogon dutsen nan, ba abin da ke ciki sai karfe ja wur cikin wata katuwar randa. Ya bude baki yana mamaki.
Malam Dogo ya ce, “Na ba ka abin da ke cikin dutsen nan duka, amma da sharadi guda. Duk sa’ad da ka zo, kada ka debi abin da ya fi fam guda kowance zuaa. Na san fam guda dai ya ishe ka kashewa yini guda. Daga nan har ka mutu ba ka ganin kudin nan na raguwa. Ka lura in Halima ta isa aure ka yi mata kaya masu kyau, ga dai gudummuwata nan na bayar.”
Masassaki ya fadi yana godiya, yana rokon Malam Dogo gafara in ya yi masa wani laifi da. Suka gafarta wa juna. Malam Dogo ya ce, “Ko da rana ka zo sai ka diba, in dai ba ka gudun kada mutane su gan ka. In ko da dare za ka zo, in ka fita, ka yi turare da ganyen nan, ka tabbata ba wani abin firgita da zai dame ka. In ko ka zo, ka ga abin da na yi ba wani abu ba ne mai wuya. Sai ka debi ganyen nan na bias dutse, ka yi turare da shi a gidin dutsen, ka ce, ‘Fayau, bude dutsen kudi.’ In ka shigo, ga fitila ka kunna, in da dare ka zo. In da rana ne ko, ba ruwanka da ita. Ka kuma amince, ba kayan aljannu ne ka ke sata ba, balle ma ka ce za ka ji tsoro. Kai dai ban da dibar abin da ya fi fam guda kullum.”
Ya dubi masassaki ya ce, “Fara daga yau.” Masassaki ya duka ya kidaya fam guda, suka fito. Malam Dogo ya ce, “Garam, kulle dutsen kudi!” Dutse ya koma ya rufe.
Malam Dogo ya dubi masassaki ya ce, “To, sai mu yi ban kwana, ni zan wuce.” Suka yi sallama. Malam Dogo ya wuce, masassaki ya koma gida yana tsalle-tsalle don murna. Ya kwashe duk labari ya gaya wa matar, amma bai gaya mata abin da za a ce da dutsen ya bude ba. Suka yi ta murna.
Gari na wayewa, ko da magariba ta yi sai ya koma ya debo fam guda. Ya I ta yin haka kullum. Nan da nan kafin wata takwas ya sa aka debe dannin gidansa, aka gina masa na kasa. Aka yi zauruka kamar goma sha biyu kafin a shiga gidan. Aka ta da soraye. Ya kwashi kayan sassaka duk ya kona.
Cikin mako guda ya auri ‘yam mata uku, ya gama da matarsa, suka yi hudu. Duniya ta komo sabuwa, sai katta ke ta kaiwa suna komowa cikin gida. Aka manta da kiransa Maikujera, sai aka lakaba masa Maigida. Da ya yi magana sai zabura a gama abin da ya ce, kome ya fadi sai ka ji barori na cewa, “Allah ya kyauta yin maigida.”
Bai cika shekara ba sai da ya daure doki goma sha biyu a bargarsa suna harbin iska. Da ya hau sai a bi shi tii, kamar Sarki. Mutane suka yi ta al’ajibin yadda ya yi arziki haka. Suka ga ko ba ya saye ba ya sayarwa, amma kullum abin nasa gaba gaba ya ke ci. Da mai garin da wadansu sun fara hassadar abin, suna kushewa. Amma daga baya, da suka ga hassadarsu ta zama taki, sai suka saki, suka mika kai neman abin sutura.
Da ba ya girman kai da wannan abu, amma daga bisani mutane da makada da maroka suka kumbura shi, har ya fara hura hanci da makada da maroka suka kumbura shi, har ya fara hura hanci yana alfahari, tun ba in ya je dutsen kudi ya ga abin kamar ba alamar karewa.
Ran nan yana zaune bias kujera, sai ya ce a ransa, “Kai, ni fa wahalar zuwa dutsen kudin nan kullum ta dame ni. Kullum, gemai-gemai da ni, a ga na nufi daji saboda fam guda. To, ni ba abin in ki zuwa ba, don ina so in kwashe kudin duka inda yana yiwuwa. Gobe dai fam biyu zan debo gaba daya in gani. Watakila dai Malam Dogo ya ki barina ne, don kada in huta wa raina. Amma fa ina amfanin a ga kamata ya tashi ya shiga daji don fam guda?”
Ko da magariba ta yi, sai ya tafi dutsen kudi, ya debo fam biyu, ya fito. Sai ya ce, “Haba, na san da ma abin nan na Malam Dogo ya rufe ni ne. Tun da ya ke dai nawa ne, mene ne na yi mini haka?”
Ya yi kamar wata guda yana diban fam biyu biyu kullum. Sai wata rana ya ce, “Shin me ya sa ne zan rika wahala da kaina don ‘yam fam biyu tak? An ce ba sata na ke yi ba. To, ba na kawo abina diga, kowa ya huta, ni ma ko in sami hankalina ya kwanta in yi kiba, da wannan wahalar shiga daji kullum, sai ka ce talaka?”
Sai ya sami buhunan gishiri ya ajiye, ya ce, “Gobe da wadannan za ni, in rika cika su ina kawowa gida har in kwashe sarai, in huta da shan dari kullum magariba.”
Gari na wayewa, ko da magariba ta yi sai ya kwashi buhunan ya nufi dutsen, yana takawa sai ka ce namijin agwagwa, don cikin ‘yar shekaran nan guda da rabi ya zama sai ke ce taiki don kiba. Ni’ima da cin dadi duk sun sa har furfurarsa ta koma baka. Ya yi tsar, shuni ya huda shi, jikinsa sai kalli ya ke yi.
Da ya isa sai ya zauna ya huta, yana kulla abin da zai yi a ransa sake wani. Matansa kuma duk ya kamata ya sake su, don tun da suka kai ga shekara guda da rabi a dakunansu ai sun tsufa.
Da ya gama kulle-kullen abin da zai yi, ya tashi ya shiga kogo da buhuna. Ya ajiye su gefe guda, ya dauki daya don ya cika sa hannu zai diba, sai ya ga randar kudin ta yi kasa, ta bace. Dutsen kuma ko kasa ko bias, sai aka bar Usuman jikan Usuman nan tsugune yana sallallami, yana da na sani sa’ad da ba ta da amfani. Ya kwashe ‘yam buhunansa, ya nufi gida yana bakin ciki.
Da ma ai irin bukatarsa ka san ba tari ya ke yi ba. Kafin wata uku dan abin hannunsa duk ya kare, ya sayad da dawakinsa, barorinsa da suka ga abin na lalacewa suka watse. Da wadannan kudi na dawaki suka kare, ya karyar wa mai garin da gidansa araha, ya yi awo da kudin.
Kafin shekara wannan dan hatsin ya kare, sai matan nan yara suka fita, suka bar shi da tsohuwar matarsa. Da ma an ce tsohon doki sai mai shi.
In gajarce maka labari dai, na rantse har da rawaninka, Allah ya be ka nasara, ba a yi shekara biyu ba, sai da ungulu ta koma gidanta na tsamiya. Ka ji aikin zari. Kowa ya I kokarin wai ya sami fiye da abin da Allah ya ba shi, ya lalace.
[insert picture here—middle right page 92]
Kafin aku ya kare ba da labarin nan gari ya wayer. Musa ya dubi Barakai, ya ce, “Kin ga irin halin nasa ba?”
Barakai ya ce, “A’a! Ashe kana da gaskiya, ka ji abu kamar na magani! Wallahi ko da ya fara labarin sai na ji na manta abin da ya kawo ni. Amma ba kome na dawo da magariba.” Ya fusata, ya ce, “har kai ma watau tatsuniyoyinsa sun rude ka ko? To, gobe ka fito ba da shi ba, ka ga abin da zai same ka.”
Da magariba ta yi sai ya Barakai ya yiwo shiri ya dawo, ya ce wa Musa, “Zan sake kwana nan gunka, yau lalle mu fita. Suka zauna suka yi ta hira. Da suka ji bayin nan sun yi shiru suka iske aku, Musa ya ce, “Zan tafi, ga shi har na sami ‘yar rakiya kuma.”
Aku ya duba ta taga sai ya ga hadari ya taso, ya ce wa Musa, “Haba, ko kuna hauka kwa fita yanzu cikin wannan ruwa?”
Barakai ya ce, “Ai ba a fara ruwa ba, ma tafi hakannan.” Aku ya yi ta jansu da ‘yan tade-tade, har ruwa ya goce. Suka zauna suna jira a dauke.
Aku ya dube su, ya ce, “Da zaman banza bari in gaya maku dan labari.”
Musa ya dubi Barakai, ya ce, “Ai ko kin san gaskiyarsa, ya fada mana dan gajere.”
Barakai ya ce, “Kyale shi, ba mu so. Kullum sai ka rika tsai da shi a kan surutun wofi, kai ba hadisi ka ke masa ba, kai ba labaran Annabawa ka ke gaya masa ba, balle a san kara shi ka ke yi.”
Aku ya ce, “Abin da ya sa ba na ba da labaran Annabawa, tsoron jahilai na ke. Kun san yanzu akwai mutane da yawa wadanda su ba malamai ba na sosai, amma da sun ji mutum ya yi wata ‘yar magana game da irin wadannan, sai ka ga suna neman daukar kafarsa, wai ya yi sabo. Amma fa im ba don gudun haka su tabbata a gare shi—har zuwa ga Shugaban Ma’aika, akwai wanda ba sani ba?”
Musa ya ce, “To, in haka ne fara gaya mana labarin Annabi Sulaimanu, wanda aka ce ya mallaki mutane da aljannu har da tsuntsaye.”
Aku ya ce, “Wannan ai sananne ne har yanzu ba ka ji shi ba?”
Musa ya ce, “I, na ji cikin dukan mutanen duniya babu wanda ya fi shi arziki”
Aku ya ce, “Ai wannan daga baya ne. Domin sa’ad da aka nufe shi da annabci aka ce ya zabi dukan abin da ya ke so a ba shi. Shi ko ya ce tun da ya ke an ba shi mulkin jama’ar Allah, shi ba abin da ya fi so sai hikima, don ya san yadda zai rike su a kan adalci. To, tun da ya zabi wannan bai zabi dukiya ba, ko tsawon rai, ko mutanen zamaninsa, ya kuma kara masa har da abubuwan nan da bai roka ba.”
Musa ya ce, “Habe, tun da na ke ban taba samun wanda ya bayyana mini asalin wannan a;’amari ba, sai fa kai yau.”
Aku ya ce, “Ko labarin yadda ya yi hukunci tsakinin wadansu mata biyu ba ka taba ji ba?”
Musa ya ce, “Wallahi ban taba ji ba. Wane irin huknci ya yi?” Aku ya matso kusa da Musa, ya kishingida a bias hannun rigarsa, ya fara.
Post a Comment