0
ILIYA DAN MAI KARFI



GAMUWAR  ILIYA DA WARGAJI

Iliya ya mika cikin daji yana ta tafiya, bai san inda ya ke nufa ba, har dare yayi masa.  Ga gajiya da yunwa, ga kishirwa, kuma ga dokinsa ya gaji, yana dai ta tafiya ne kurum.  Kwamfa sai ga wani lambu a gabansa, cike da ya yan itatuwa da huranni masu ban sha awa.  Daga tsakiyar lambun kuma akwai wata alfarwa watau tanti, ta farin alharini, a kafe.  Iliya ya sauka ya daure dokinsa, ya je ya leka cikin alfarwar bai ga kowa ba, sai gado na karfe, da shimfidu, da matasan kai.  Bai yi wata wata ba, sai ya haye gadon ya yi kwanciyarsa, ya yi ta sharar barci, har gari ya waye.  Rana ta sake faduwa, dare ya yi, gare ya sake wayewa, har dai wajen kwana uku, bai farka ba.  A ranar daren ukun, Iliya yana tsakar barci, sai Kwalele ra rika jin wani irin motsi da rugumniya an nufo wajen alfarwan nan.  Kamar dai hadari ya taso, kasa na motsi kamar za ta tsage.  Itatuwa suna ta faduwa, har koguna suna fantsamad da ruwa cikin daji.  Sai Kwalele ya yi haniniya da karfi, don Iliya ya farka.  Ya yi masa ishara da cewar ya tashi maza ga wani abin firgici nan tafe.  Ashe wurin shan iskar Wargaji ne, wanda aka fada wa Iliya kada ya yarda su yi fada da shi.

            Can, sai Iliya ya yi firgigi ya tashi.  Kwalele ya yi masa ishara da ya hau sama ya boye.  Nan da nan Iliya ya haye bisa wani dogon ice, na cikin lambun, ya make.  Kwalele kuma ya sami wuri ya boye shi ma.

            Zuwa can, sai Wargaji ya iso, yana bisa wani doki kato, daga nesa kamar tsauni.  Ya sauka abakin kofar alfarwar.  Iliya ya dube shi da kyau, ya ga lalle ya isa abin tsoro, don bai taba ganin mutum da girma kamar sa ba.  Shi mutum ne mai fadi, ga tsawo, har ya kere itatuwan da ke wurin.  Sai ya ga ya jawo mani dogon akwati daga bayan dokinsa, ya dauko wani irin mabudi na zinariys, ya bude akwatin.  Sai ga wata kyakkyawar ya, ja wur da ita, kamar aljana ta fito.  Ta ci adi da kaya iri iri na zinari, da lu ulu u, da jauhar.  Tana saye da wadansu irin takalma na sakakken jan alharini.  Fuska tata sai kyalli ta ke yi kamar madubi.  Tana da dogon wuya, ga idanu dara-dara, hanci har baka, gashin kanta sai ta sa hannu ta tattara shi don kar ya zuba kasa.

            Wargaji ya kama hannun matan nan suka shiga cikin alfarwa.  Ta bude wata jaka, ta fito da teburi ta girke, ta fito da abinci da abin sha.  Suka zauna suka ci, suka sha, suka koshi.  Sa an nan Wargaji ya hau gado ya kwanta, ta rika yi masa fita.  Nan da nan barci ys kwashe shi.  Da ta ga ya yi barci, sai ta fito don ta nike kafa, ta kuma debe kewa, cikin lambu.  Tana tafe tana rera wata irin waka a hankali, mai dadin gaske, wadda ke jirkita hankalin mai saurarenta.  Can sai ta daga ido sama, ta hangi Iliya bisa itace make.  Ta dube shi da kyau ta ce, Ya kai wannan kyakkyawan saurayi, sauko.

            Nan da nan Iliya ya sauko da rawar jiki.  Ta kama hannunsa suka shiga cikin alfarwar.  Wargaji yana ta sharar barci.  Ta bude bakin aljihunsa, ta saka Iliya ciki.  Iliya ya yi kamar an saka shi cikin wata rijiya mai zurfi.

            Bayan an jima kadan Wargaji ya tashi daga barci, ya shisshirya, ya dauki yarinyan nan ya saka akwati, ya kulle, ya sarkafa akwatin a kucciyar sirdi.  Ya kama haryar gida.  Ya doshi madansu dogwayen tsaunuka da a ke kira Tsarkakkun Duwatsu.    Wannan wuri ba mahalukin da ya taba zuwa gare shi.  Babu kuwa mai iya zuwa wurin.  Nan ne fadar Gijigiji uban Wargaji.  Akwai gine gine masu kawa iri iri a wurin.  Akwai dukiya da samun duniya kowane iri a wurin.

            Shi Gijigiji ya fi Wargaji girma, da cika, da kasaita, da kwarjini, da cika huska.  Amma ya tsufa ainun, har ya kai ga makancewa.  Suna cikin tafiya sai Wargaji ya ga dokinsa ba ya sauri sosai kamar yadda ya saba.  Kuma yana tafe yana sassarfa kamar zai fadi.  Wargaji ya yi hushi ya buge shi.  Sai dokin ya yi ishara, ya ce, Yi hakuri, ya shugabana.  Karfina na in dauke ka kai da uwargidanka ne kadai, amma ba ni da karfin da zan dauki halitta uku.

            Wargaji ya dudduba ko ina bai ga kowa ba, sai ya ji aljihunsa da dan nauyi.  Ya sa hannu, ya dauko Iliya.  Ya dube shi da kyau, ya ce, Kai Bil adama, yaya aka yi har ka zo nan, har kuma ka shiga cikin aljihuna?    Iliya ko yaushe mai tawakkali ne ga Ubangiji, kuma ba ya da tsoro, ya dubi Wargaji sosai, ba da wani tsoro ko razana ba, ya ce, Shugabana, uwargidanka ce ta saka ni cikin aljihunka, ya shugabana.    Nan da nan Wargaji ya cika da hushi, ya dauki akwatin nan da matar ke ciki, ya yi jifa da shi bisa wadansu duwatsu a tsakiyar wani kogi, ya ce, Zauna nan mutuniyar banza, aljanaba.  Nan za ki yi tazama har ranar tashin kiyama.

            Wargaji ya dauki Iliya ya rungume a gabansa kan doki, suka ci gaba.  Zuwa can Wargaji ya huce, ya tambayi Iliya kasarsu, da garinsu, da labarinsa duka dai.  Iliya kuma ya kwashe labainsa tun daaga farko har karshe ya fada masa.  Nan take sai soyayya ta kullu tsakaninsu.  Suka ci gaba da tafiya suna ta labari kamar abokai.

            Amma kafin sun isa gida, sai Wargaji ya fada wa Iliya cewa idan sun isa gida, zai kai shi don ya gai da Gijigiji, watau ubansa.  Ya fada masa idan Gijigiji ya miko hanny don su gaisa kada Iliya ya mika masa hannu.  Ya ce masa da sum isa, akwai makera a kofar gidan, Iliya ya yi maza ya saka karfe a wuta, idan Gijigiji ya miko hannu su gaisa, ya mika masa karfen nan a maimakon hannunsa.  Iliya ya ce, to, suka ci gaba da tafiya, har suka kawo kofar fada.  Iliya ya cika da mamakin irin ginin wurin, watau yadda aka yi shi da farin dutse, aka yi masa zane iri iri.  Daga ciki kuma ko ina ka duba sai kujeri da shimfidu.  Hatta tagogin gidan na madubi ne ga labule launi iri dabam dabam, ga fitilu ko ina.  Da dai sauran kayan daula da ni imomin duniya.

            Zuwa can Gijigiji ya fito ya tsaya a kofar zaure don ya yi wa Wargaji barka da zuwa.  Ya tambaye shi garuruwan da ya je.  Wargaji ya fada masa ya je kasashen Gabas ne.  Har daga can ya samo aboki.  Gijigiji ya ce a kawo Iliya su gaisa.

            Da ma da isarsu Iliya ya sa wani katon karfe cikin wuta ya hyi ta zuga ya yi ja wur, yana jira ne a kira shi.  Wargaji ya zo suka tafi.  Gijgiji ya miko was Iliya hannu don su gaisa, sai Iliya ya mika masa karfen nan.  Gijigiji ya rushe karfen kamar wanda ke gaisawa da wani.  Zuwa can ya saki karfen ya yi sanyi, ya ce, Lalle Wargaji ka samo aboki wanda ya kamace ka.  Ya cancanci ya zama abokinka sosai.

            Kashegari da suka fito kofar gida, suka tsaya suna hangen filin karkara da itatuwa.  Iliya ya duba haka ya hangi dokinsa Kwalele yana kiwo kusa da gidan.  Murna ta kama Iliya ya ruga ya kamo shi.  Wargaji ya yi ta mamakin wannan irin doki.  Nan da nan suka daure shi a turke, aka zuba masa abinci aka ba shi ruwa ya sha.

            Marece na yi su Wargaji suka hau dawakansu suka tafi shan iska.  Suka bi ta gefen tsaunin nan totar, suna tadi, suna annashuwa.  Suka yi ta tafiya har suka kai ga wani wuri mai duwatsu.  A kusa da duwatsun sai suka ga wani akwati a bude, an rubuta Wannan akwati an yi shi ne domin mai shi, ba kuwa zai yi daidai da kowa ba cikin duniyan nan sai mai shi.    Ashe da ma wannan akwati saboda Wargaji aka yi shi.  Sai Iliya ya ce,  Bari in gwada in gani ko nawa ne.    Ya hau ya shiga cikin akwati, amma bai yi masa daidai ba,  ya fito.  Wargaji kuma ya ce,  Lalle nawa ne, bari mu gani.    Sai shi kima ya sauka ya shiga ciki, ya kawu yi daidai da shi, kamar da dai sai aka gwada shi sa an nan aka yi shi.  Ya cika shi har ba ya iya motsawa.  Daga ciki, ya miko hannunsa ya rufe bakin akwatin.  Shi ke nan sai akwati ya kulle kam, ba ko yar kofar da haki zai iya shiga.

            Amma Wargaji bai yi wa Iliya ban kwana ba, bai kuma bar masa wata wasiyya zuwa ga ubansa ba.  Saboda haka ya ce Iliya ya bude shi, zai yi masa wasiyya, kuma su yi ban kwana da juna.  Iliya ya sa hannu, ya yi, ya yi ya bude akwatin, amma ya kasa motsa ko da murfin.  Ransa ya baci, hankalinsa ya dugunzuma, ya ce wa Wargaji da karfi,  Ba na iya bude akwatin?    Wargaji ya ce, Dauki takobina na yaki, ka sari gefen akwatin.    Iliya ya sa hannu zai dauki takobi, amma ya kasa cira shi saboda nauyi.  Ya fada wa Wargaji ba zai iya daukar takobin ba.  Wargaji ya ce, Matso kusa da ni.    Iliya ya matsa.  Wargaji ya feso wa Iliya dukan karfinsa.  Nan da nan Iliya ya dauki takobin da sauri, kamar wanda ya dauki kara.  Ya sari akwatin da karfi.  Karar saran ta cika daji, tsaunuka suka kama wuta, duk wurin ya rude kamar sama da kasa za su hadu don firgita.  Tartsatsub wuta ya watsu ko ina.  Maimakon murfin akwatin ya bude, sai ya kara kullewa da karfi.

            Wargaji ya ce wa Iliya,  Kara sarawa dai da karfi.    Iliya ya sake saran akwati.  Amma saboda tsananin karar, har Iliya da kansa ya gigice.  Wuta ta kama, hayaki ya murtuke wurin.  Akwatin kuwa ys kara kullewa.

            Can da karar ta kwanta, Wargaji ya ce, Iliya, matso in kara maka karfi.  Zam ba ka dukan karfin da ke gare ni.    Iliya ya ce,  Ya shugabana, idan karfin da ke gare ni a yanzu ya fi haka, ko kasa ba za ta iya dauka ta ba.  Na gode kwarai.  Ina so ka fadi dukan abin da ka ke bukata, idan ina iyawa zan yi maka.

            Wargaji ya ce,  Ba sauran abin da za ka iya yi mini.  Ni dai tawa ta kare.  Ka ga akwatin nan, kabarina ke nan.  Na gode maka, Allah ya yi maka albarka.  Allah ya fid da kai daga sharrin mutane.  Idan ka sami damar komawa, ka yi mini ban kwana ga mahaifina.  Ka fada masa irin kaddarar da ta same ni a wannan wuri.  Allah ya kaddara saduwarmu a Darassalamu.

            Wannan magana ta Wargaji ta sa hankalin Iliya ya tashi kwarai, ransa ya baci, ya rasa abin da ke masa dadi cikin duniya.  Ya kuma rasa abin da zai yi.  Sai ya fashe da kuka.  Ya roki Wargaji gafara, ya yi masa kyakkyawar addu a.  Ya dade nan gefen akwatin, yana kuka.  Can da hankalinsa ya komo, ya tuna kome kaddara ce ta Ubangiji, saboda haka, sai ya yi tunaniu a ransa, ya ce, Ni Iliya, yanzu in koma im fadawa Gijigiji me?  Ai ba zai yiwu in koma wrin nan ba.    Sai ya taka dokinsa ya hau, ya yi ta tafiya, bai san wajen da ya ke nufa ba.  Ya bi gangaren tsaunin nan ya yi ta tafiya har ya yi nisa, sa an nan ya waiwayo, sai ya hangi hawayen Wargaji suna zuba ta kafar akwatin.  Tausayi ya kara kama shi, ya sake fashewa da kuka.  Sai ya sauka ya zauna yana ta tunani, bakin ciki ya rufe shi.  Bayan ya dade a zaune, sai kuma ya tashi ya ci gaba da tafiya.

Post a Comment

 
Top