0
DUK DA'DINKI DA MIJI





 
DUK DA'DINKI DA MIJI 


(BASED ON A TRUE LIFE STORY). 

Fitowa ta daga band'aki hijabi na d'auka na saka sannan na hau kan sallaya don gabatar da sallan azahar, bayan idar wa nayi azkar d'ina sannan na mike don jin kirana da kanwata ke yi, "Adda!, Adda!!" na bud'e kofan sannan nace "fatima meye kike kwalamin kira?" Ta kallen tana shan ruwa sannan tace "kinyi baki na kai su babban falo, kije kiduba" na nufi hanyan gun don dama bancire hijabin jikina ba, na bud'e kofan falon ga mamakina na gansu su uku, kuma dukkansu ba wacce nasani, donhaka na nemo murmushi wa fuskata na shimfida, nayi sallama, suma suka amsa suna maidamin murmushin danayi, na zauna na kallesu sannan nace "ina wuninku?" Dukkansu suka amsamin suna murmushi tafarkon wacce zance itace karamar cikinsu, ta kallen sannan tace "kece Benaxir Omar ko?" Na gyada kai sannan nace "ni ce, Allah yasa ba laifi nayi ba" Ta kara murmushi sannan ta gyra zama tace "munzo ne dama nemanki nida kawayena, sunana Hamdiya wannan kuma Hanifa , sai wancan Hafsat" alokacin fatima tashigo da tray a hannunta, duk drinks ne aciki sai ramlat ta biyota da na snacks ta gayshesu sannan suka ajiye, Wacce tace sunanta Hamdiya tace "kannenki ne ko?" Na gyada kai nace "ae" "Kuna kama" "Anya? Tunda kince haka toh shikenan" ramlat da fatima suka fice sannan Hamdiya tacigaba da cewa "Munga d'an rubuce rubucenki shine mukazo don mu baki labarin mu, ko zaki taimaka mana ki bawa duniya labari su koyi darasi akai,tabbas rayuwanmu akwai darussa aciki wanda ke nasan zaki taimaka mana" Na kallesu sannan nace "Tabbas kunzo gida, kuma a shirye nake ko da yaushe na ji labarinku domin ni da makaranta mu amfana, barin shiga na d'auko alkalamina da littafi"


DUK DAD'INKI DA MIJI 


 (BASED ON A TRUE LIFE STORY).


 Na shiga d'aki na d'auko littafina da alkamima sannan na zauna ina rike da shi nace "Hamdiya zamu fara dake kenan ko?,saiki bani labarin, inkingama sai sauran suyi" Ta cire hijabin jikinta sannan ta sha juice din da ke cup ta gura murya sannan tafara "Sunana Hamdiya Usman, yanzu haka shekarana 28, nayi aure inada shekara 26, auren shekara biyu yayi, , nayi primary, secondry alokacin dana gama, mahaifina yarasu, kasancewar mu biyar ne agun sa, sai mahaifiyata, dukkansu ni ce karama, yayuna hudu maza, kuma kowannensu yanada aikin yi, mahaifina yana da rufin asirinshi tunda bamu rasa ci da sha ba, kuma rayuwa daidai gwargwado nayishi, sai dai randa ya fad'i ya mutu yayuna suka cigaba da kula dani, muna zaune a f.h.a lugbe abuja, nan nayi jamb nasamu admission n shiga gwagwalada, nasamu mass communication, na manta bance miki inada saurayi 
Raihan tun ina js3 ba, a anguwanmu yake,, shikuma yana gwagwalada aji daya alokacin, muna soyayya kaman zamu had'iye junanmu, bana kula kowa sai shi, komi Raihan yasamu zai kawomin,duk da baida arziki, anma yanada wadatan zuci, nasamu dai nashiga gwags, shekaran da nashiga Raihan yana service, kafin na tafi mun zauna na masa alkawari cewa ni bazan kula kowa ba saishi, namishi alkawari, raihan baiso na je nan ba, kwata kwata hankalinsa taki nutsuwa har abun ya bata min rai nace yana min hassadan zuwa makaranta,don yaga shi yagama?, da kyar ya lallabeni muka shirya na fara zuwa,babban yayana 

Yaa umar yaki yarda na zauna a hostel, yace ya gwammaci duk nisa yakaini,, umma na ne ta lallabashi da kyar ya yarda aka kaini kasuwa nayi siyayya sannan ran asabar aka kaini jamia, inda dama banyi bacci ba tsabar murna da gand'oki, aka bani bedspace dina a daki, d'akin mutane uku ne, basa nan don haka na shirya kayana na zauna don sai monday zamu fara lectures, ina zauna suka shigo su biyu, dafarko zama sukayi suna tambayata sunana na gaya musu, har course dina dakuma inda nake, dayansu tace sunanta hanen, dayan tace ceecee na zare ido don gabana ne yafadi jin ba musulmai bane, 


DUK DAD'INKI DA MIJI NA


(BASED ON A TRUE LIFE STORY) 


D'ayan wacce tace sunanta hanen tace "kinga kinshigo skul wannan katon hijabin fa?" Tacire min ina kokuwa taki yarda saidata cire, gashin kaina ne ya zubo "Laahhh ceecee zokiga gashi God'" suka fara jamin kai, domim daga ceecee har hanen jan attarchment ne akansu, sai da suka lugwigwita min kai sannan suka sakeni, ina zaune a gefe atleast dai tunda tashin abuja ne ykamata ace wannan rayuwar ba bare bane aguna ae, anma a yanayin tarbiyan dana taso a takure na tashi, gidanmu babu wasa gun tarbiya, suka barni kowa ta nufi kan gadonta, na zauna har magrib tayi nayi sallah, suna nan suna chatting awayansu, can suka mike suka saka ruwa a kettle suka tafasa ruwa kowa tanufi toilet tayi wanka, ceecee ce ta janyo sallaya na bude baki tare da cewa daaa ku musulmai ne?, 


dukka suka zaro ido hanen tace "dan kinji munce ceecee da hanen?, ni sunana hanifa anan nadawo hanen, itakuma hafsat ta dawo ceecee, dukkanmu muna aji biyu, sannan muna karanta mass comm" nayi shiru inda suka yi ta dariyansu , tsaf suka shirya cikin riga da wando hanen iya cibi yayinda cecee yakai ciki saidai hannun ves, duk suka zuba gashin dokinsu suka fesa turare sannan suka fice, sunban sallahun cewa na rife dakin bazasu dawo adaren ba, shiru nayi nikam na d'auko wayata na kira Raihan muka sha soyayyan mu nayi sallahn ishai sannan na bi lafiyar gado. 

Washegari da asuba natashi nayi sallah nayi zikirin safe na, sannan na koma, cecee basu dawo ba sai karfe goma na safe, suna zuwa suka baje kan gado, alokacin na girka indomie na naci nayi wanka na hau kan gado ina karanta littafin hausa wanda nakeso sosai, basu tashiba sai bayan karfe biyar ina kallonsu sukayi brush ba wacce tabi kan sallah, suka dafa indomie suka ci, ceecee tafita hira hanen ma tabita sai karfe goma na dare suka dawo kowacce da ledodi a hannuta inajinsu suyi tad'in wannan suyi na wancan duk na maza, kuma ga mamakina masu kudi suke kira wadanda nasani, inaji suna ambaton hotels wanda ni kaina bazan iya misalaawa ba, nayi tunanin wannan wani irin rayuwa sukeyi?, 

Ran monday nafara zuwa lectures, bana dawowa d'aki sai yamma idan na gama, kuma bana fita sai washegari, a sannu ahankali na fahimci rayuwar makarantan, gurine bariki kowa yanada abunda yakeso, musamman matan bazakayi tsammanin wasunsu akwai iyayensu ba, manyan yan matan sune masu shiga da fita da motoccin su dasuka mallaka, sannu ahankali na gane cewa hanen da ceecee na shaye shye idan nacire bin maza wato karuwanci da sukeyi da manya manyan attajirai, idan sunsamo dukiyarsu sukan bani na ki yarda, kowaccensu tanada kyau daidai gwargwado, hanen tafi ceecee haske don itace take dibin fulani yayin da ceecee bahaushiyar kano ce, duk kyansu ni nasan abaya na suke saidai alkawarin danayi da raihan kullum yana raina, inzan fita nasaka hijabi na, na suturce jikina kamar yadda nakeyi a gidanmu, duk fita idan sunfita akalla kowacce takan shigo da dubu dari biyu zuwa uku, wataran kuma suje party, shaye shaye kuwa nakan fice nabar musu d'akin idan sunayi, hanen tayi tayi tajani a jiki na ki yarda donhaka ta bi hanyar da tafi komi hatsari, hanyan da har yau ni da ita muna nadama, gatanan duk kinganmu agabanki.

Post a Comment

 
Top