MAGANA JARI LITTAFI NA DAYA
labari na goma sha tara
BANZA GIRMAN MAHAUKACI KARAMIN MAI WAYO YA FI SHI
Banza Girman Mahaukaci, Karamin Mai Wayo Ya Fi Shi
A cikin wani daji akwai wata kura wadda ke da gidanta mai kyau kwarai da gaske a wani kogo, ta kawata shi da kyau, babu abin da babu a ciki.
Sai kuran nan ta sami wani biri, ta sa shi ya rika tsaron gidan nan kullum in ba ta nan, don kada wani abu ya fasa in ba kowa, ko kuwa a zo a yi mata sata. Kullum birin nan ba ya rabuwa da gidan. Ran nan yana zaune sai wani bunsuru da mata tasa da ‘ya’yansu uku suka fado nan gidan. Dalilin zuwansu kuwa, kiwo suka tafi har dare ya yi musu, suka rasa hanyar komawa gari, suna kuwar tsoron kada su gamu da zaki ko kura.
Da biri ya gan su, sai ya ce, “Kai daga ina? Su wane ne ku? Nan fa gidan kura ne, ku rufa wa kanku asiri ku koma, in ba haka ba kuwa, in je yanzu in gaya mata ta zo ta hau doronku dai dai.”
Akuya ta dubi bunsuru, ta ce, “Maigida, yau fa abin da mu ke dangana da ciyawar da ubangijimmu ya ke zuba mana kullum dare! Ga shi kwadayin son danya ya sa mun kawo kammu a mahalaka.”
Biri ya dubi bunsuru, ya ce, “ni fa na gaya muku ku gudu, in ba haka ba, yanzu in tafi in gaya mata.”
Bunsuru ya harari biri, ya ce, “Mutumin banza, wannan gidan tun daga kakan kakana, Sarkin Masu, na gaje shi. Ba wanda zai kwace shi daga gare ni duk fadin duniyan nan. Je ka, gaya mata mana, ina nan ina jiranta.”
Biri ya zabura, ya tafi wurin kura. Bayan ya tafi akuya ta ce wa bunsuru, “Mu yi ta kammu, kafin kura ta zo!”
Bunsuru ya ce, “Ke ar, mara hankali! Ai yanzu idan muka nuna alamar mun ji tsoro mun kade, ba mu da wurin tsira ko mun gudu. Idan mun ga kura tafe, sai ki ce wa ‘ya’yammu su yi kuka gaba daya, in na tambaye ki dalilin kukansu, ki ce suna jin yunya ne, wai suna son naman kura su ci, ba su cin na jiya, ya rube.”
Akuya ta amsa ta ce, “To, amma dai ni ban sa wannan za ta fid da mu ba.”
Da biri ya isa wajen kura ya ce mata, “Ga wani abu nan da iyalinsa, ya zo ya ce wai gidan nan ba naki ba ne, wai na kakan kakansa ne, Sarkin Masu. Na ce ya gudu, kada ki zo ki cinye su. Ya ce ke din me? Ba irin zagin da bai yi miki ba.”
Kura ta ce, “Ka san shi?”
Biri ya ce, “A’a. Amma barewa ta ce wai bunsuru ne.”
Kura ta ce, “Ko da ban gan shi ba, lalle ba bunsuru ba ne, Bunsuru ba yadda zai yi wannan aiki. Yaya kamarsa ta ke? Ya kai girmana?
Biri ya ce, “Ko kusa, ni ma kadan ya fi ni. Wani irin launi gare shi ja ja, da gasusuwa zaro-zaro, da ‘yan kofati kamar na barewa.”
Kura ta ce, “In ka tabbata bai fi ni karfi ba, mu je mu gan su, Shin su nawa ne?”
Biri ya ce, “Har da ‘ya’yansu su biyar ne duka.”
Kura ta ce, “Nawa? Biyar! Ko ba su da karfi fa akwai yawa Sarkin Yawa kuwa ya fi Sarkin Karfi!”
Biri ya ce, “Ai duk kanana ne, babban ma da tsawon kafa kadai ya fi ni. Kuma a nan duniya ai babu naman dajin da ya fi ki karfi, in ba zaki da giwa ba.”
Kura ta ce, “Kai, yi mini shiru! Namun dajin da suka fi ni karfi nan duniya wa ya san iyakarsu? Kai dai mu tafi mu gani, in da riba mu fafata, in kuwa babu mu yi ta kammu.”
Ko da bunsuru ya hango su sai ya ce wa matarsa, “Tura ‘ya’yanki cikin kogo, in sun shige kuma su yi ta kuka baki daya.”
Da suka shige duk suka barke da kuka baki daya, “Ba-a-a-a-a-a-a-a! Bunsuru ya ce, “kai, me ya sami yaran nan?”
Akuya ta ce, “Wai sun ce duk cikin naman da ke gidan nan ba su cin naman kowa sai na kura kadai, wai ya fi dadi.”
Bunsuru ya ce, “To, a ba su sauran na kuran nan da na kasha jiya mana su karasa.”
Akuya ta ce, “Na ba su, sun ce ba su cin naman da ya fara bashi, wai sai sabo su ko so.”
Bunsuru ya ce, “To, su hakura kadan su bar motsi, don na ji biri ya ce wai kura yau tana tafe, za mu yi fada, in Allah ya kawo mana ita ai kin ga yau sa wadata in dai don nama ne, don na ji an ce ta yi mai kwarai.”
Kura ta dubi biri, ta ce, “Ka ji ko, gaskiyata ce da na ce lalle abin nan ya fi ni karfi, ka ji jiya ma sai da ya kasha wani kura. Na san lalle bunsuru ba ya yia daurewa ya yi mini haka ba, ko daji ma ba ya yarda ya fito ba, wanda kullum yana can boye cikin gari. Ni zan koma tun bai rigaya ya gan ni ba!”
Biri ya ce, “Kada ki lura da zancensa, fankama kawai ya ke yi miki da karairayi, na gan shi dan karamin abu ne, kuma da ganin tafiyarsa ka ga raggo.
Da kura ta ji haka zuciyarta ta yi dan karfi, ta ce, “To, mu tafi.” Ko da bunsuru ya hango ta, sai ya tura ‘ya’yansa a cikin kogonkura, suka soma kuka gaba daya. Ya ce wa akuya, “Don Allah gaya musu su yi shiru, biri ya yi mini alwashin zai yi dabara ya kawao mini kura har nan gidana, in sun yi hayaniya yaya za ta yarda ta iso, balle mu samu mu kasha ta mu sami abin kalacin? Kun gani fa yau saboda ita ba mu yi tanajin kome ba, a gare ta muka dogara.”
Da kura ta ji haka sai ta kama biri, ta ce, “Ashe da munafunci aka kulla da kai, don ka sa a kasha ni a banza? To Allah ya tona asirinka, dan banza!” Zai yi magana ta sa kafa ta taka shi, ta kasha. Ita kuwa ta yi baya da gudu tana zawo.
Da bunsuru ya ga sun sami sa’a haka sai suka kwashe duk kayan da ke gidan suka kama hanya suka koma gari gidansu.
Aku ya dubi Musa, ya ce, “To, mu tafi, kyaun dan halas duk kayan da ke gidan suka kama hanya suka koma gari digansu.
Aku ya dubi Musa, ya ce “To, mu tafi, kyaun dan halas duk abin da ya yi niyya ya cika. Abin da ke aukuwa ga mai yin alkawari ba ya cikawa, in ka ji ai sai ka yi kurum.”
Musa ya ce, “Me ke farua ga mai saba aksawari. Don mutum ya yi niyyar abu, ya koma ya fasa, sai wani abu ya same shi?”
Aku ya ce, “Babban mugun abi kuwa zai same shi.”

Post a Comment