0
ASHE KAINE MIJINA ?





ASHE KAINE MIJINA ?? 49

Na HAUWA m. JABO. ..

Itama ta amince da sharadin sa duk a SMS suke maganar,
Nan take nura ya rubuta takardar saki ya ijiye ma naziah a hanyar dakinta,
murna kamar ta kasheta yau xata kai ga burinta,ya deen dinta xaiji idan yaji ta karbo takardar saki,murna ba'a magana,
kamar ta wuce gida amma sai tace bari dai ta cika alqawari kuma taga wannan nihal da akeji da ita,kowa xancenta yakeyi xata dawo karatu canada, kuma tace gidansu xata sauka...

Naziah na Kwance tana yan tunane tunanenta, yanda aurenta da deen xai Kasan ce tunda yanxu ta xama baxawara, a bikin Su tayi kaxa tayi kaxa, a wannan tunanin ta gangaro wani tunani..
Sai yau nake tuna cewa fa...
tunda nayi aure banyi al'adaba ko sau dayaba..
Sai yau nake tuna dan ciwon dane da yawan xaxxabin da nakeyi..
Yanxu nake fahimtar inajin cikin cikina kamar ana min motsi..
Sai yau na tuna duk kwanciyar da nake da deen dina a jikina yake xube min.....din bai taba amfani da condom ba!!!
Lokaci daya hankalina ya tashi lallai ni lafiyayyace kuma komai xai iya faruwa dani,
Kardai ciki nake dashi???

Wai ma idan nayi ciki ya xan kalli inna, gashi na kashe aurena  rana ta farko da naziah ta fara nadamar abinda ta aikata gashi ta karbi takardar  rabuwa da nuraya xatayi???

Ta Shiga kogin tunani Lallai mafita itace taje asibiti Dr ya dubata, ba shiri tadauki key Sai wani prvt hospital,  ta fara yima Dr bayani abinda ya kawota,
Bayan bincike bincike Dr ya gane cikine da ita Dr yaxo yana fada, ke kinsan kinada ciki amma bakixo aka dubaki ba sai yau, to lallai jaririnki yan......

Batamaji abinda Dr yace ba ta fadi sumammiya....


ASHE KAINE MIJINA ??50

NA HAUWA M. JABO..

Sumammiya, likitoci sukayo kaina aka samu ta farfado ta fara sun batu,
Dr dan Allah kataimakeni Dr ka rufamin asiri ya xanyi da rayuwata...!! shi Dr yadauka taji abinda ya fada ne na cewa yaron cikinta na cikin matsala kuma cikin xai iya xubewa ko wane lokaci.. hakan yasa yake bata haquri da magana tare da alqawarin kasan cewa Dr ta har ta Sami sauqi, ya rubuta maganguna da allurai da kuma abincin da xata riqaci...

Ta dawo gida cike da xullumi,da tunani, shin xata fara fadama deen labarin cikin da take dashi ne?? ko kuma ta fara da maganar sakin da aka matane,?? "Nima dai jabo sai kallonta nakeyi" tadai yanke shawaran Sanar dashi xancen cikin b4 sakin....

  dama bata tafi phone dinta ba,
Ta kira deen dinta, koda taxo ya kira har 8,ta kira
He'll hulwatiy ya kike ina kika shiga inata kira baki dauka ba.??
Hello ko baki jinane?? har xai kashe sai yaji maganarta a hankali,
Inajinka deen!!!
Lafiyan ki kuwa??
Naje hospital ne...!!

Subhanallahi hulwatiy mi yake damunki??
Waye bashi da lafiya??
Kimin bayani mana kinyi shiru...
Na fara magaba ka katseni shi yasa nayi shiru..!!
Sorry hulwatiy kinsan Banason abinda xai taba min lafiyar kine ko kadan, kece jina kece ganina.. kece duk wani buri na rayuwata...!!!
Talk to me please m hulwatiy.!!
Tayi ajiyar numfashi,
Daxu Dr y dubani...
Eh inajinki ci gaba, miyake damunki mi Dr yace??
Yace wai inada juna biyu...
What..!!????


ASHE KAINE MIJINA ??..515?1?

NA HAUWA M. JABO..

WHAT...!!!!???????????
Eh yace ciki nake dashi, haba hulwatiy,
Kidaina min irin wannan wasan mana!!
Kamar ya Wasa
Wallahi deen da gaske nakeyi.

Hankalin deen ya tashi matuqa, ya Rasa abin cewa,
Ok ki bari anjima xan kiraki yanxu inajin maganar wannan shasha shar tana zuwa kada taji mi muke fada!!
Amma ai yau Monday deen daxu kace min kana office ne!!!
Eh ina office inaga tanada buqatar kudine taxo gurina!!
Amma kace min baka taba ganinta ba ya akayi har kake gane muryarta.??
Anya deen!!!!
No kingane ai......

Sai taji sallamar mace a wayar kuma taji an kashe aranta tace ee naji muryar mace inaga ta biyo shine, sai bata gane komai, kuma bata taba tunanin yaudara a gurin deen ba.
Da farko kuma har taji tsoro,
Amma fa ita dole deen yaxo a xubar da cikin nan kamin tayi yun qurin barin gidan aurenta, aranta ta riqa saqe saqe har bacci ya dauketa

A bangareen deen kuwa yanata saqe aran shi yanda xa'ayi da ckin nan, shikam bai San yanda xaiyi da itaba, kuma yasan illar xubar da ciki dan xata iya mutuwa, kuma dole Shi xaikaita hospital kuma shi xaiyi sign Lallai baxai iyaba...!! idan ta mutufa??
Miye mafita??

Mafita dayace kawai ka rabu da matar mutane kaje ka rungumi matarka!!!
Idan nayi haka anya na mata adalci???
Lallai nayi kuskure nayi jahilci tarayya da matar aure,
Haka ya qare tunanensa qarke ya yanke cewa xai rabu da ita kawai taSan yanda xatayi da cikin......

Kinji mugu dan iska kadan daga cikin halayen sheguuuu..??

bata farka ba sai guraren maqreeb, tasan ma deen ya kira, a gurguje tayi sallah bata qareba aka kira maqreeb tayi maqreeb tayi addu'a ta janyo waya..
Ta duba wayam ba miss call ko daya abin ya bata mamaki matuqa. Ta daure ta kira shi sai na uku ya dauka,
Hello deen....

Post a Comment

 
Top