0
ASHE KAINE MIJINA..?28?



Na HAUWA M. JABO.

Qofane, yana Shigowa  na miqe dan Allah uncle kayi haquri.!!! da abinda na maka dan Allah ka kaini gida, aranshi yace dama batayi bacci ba??.
Ya tsaya bakin qofa ya toge, ina tsoron in shigo ki mareni! Ko ki dakeni dan nakula bakida lafiya!! Naji xafin maganar amma na Shanye yaci gaba idan haukar taki baxata motsaba in shigo, kuuuuut dan na mareShi  xaicemin mahau kaciya, na daqo na kalle shi namai kallon raini har na hada baqar maganar da xan yaba mai, kawai na sunkuyar dakai kayi haquri uncle.....

Yashigo dakin ya zauna, ya kalleta ashe ganin da yake mata a camera ba haka bane duk  ta firgice a camera kuwa yana ganinta kaman lafiya lau,
Yana xama ta fara jero mai tambaya...

Miyasa ka ijiye ni anan??
Mi kakeso in maka??
Baka tsoron Allah ne??
Ko kai ba musulmi bane??
Baka tunanin halinda iyayena zasu shiga??
Is ok.... ya katseta, da daga mata hannu kansa na kallon qefe, ta dago ta kalleshi, ki natsu kiji mi zan gayamiki!! Na farko Idan na fara magana kada kiyi magana sai na qare, kinajina? Eh naji!! Ya juyo ya kalleta tausayinta da yanda ta bashi amsa ya kamashi , lokaci daya sonta da sha'awar kusantarta ya kamashi, ya hade yawun dole, gashi ta wani mishikyau, tufafin sa ne a jikinta top da wando, yayi sauri ya kawar da kai, ya miqe tsaye idan har ya kuSan ceta bai mata adalciba, dan kuwa yayi niyar keta mata mutunci ladar mari da ta mishi amma kuma tausayinta ya rinjaye shi, ya miqe anjima zan miki bayani, zatayi magana, mi nace miki?? Ta tuna yace kada tayi magana, ta kalleshi taga idonsa taga ya kada yayi jaa, sai taji tsoro, ya fita, mamaki ya kamata yanda ya sauya lokaci daya, taci abincin tayi sallar tana nan zaune sai gashi ya shigo, abin mamaki bai kalli ko gefenta ya zaune ya juya mata baya.....

ASHE KAINE MIJINA??29

Na HAUWA M.JABO.

Ya juya mata baya, yafara da cewa ranar assabar na dawo daga kasuwa sai naga kamar kina neman taxi, sai na tsaya in rage miki hanya dan unguwar nasan ba'acika samun taxiba, abinda ya bani mamaki yanda idonki ya rufe kika kasa banbance motana da taxi, dan ni ba dan taxi bane,har kina gayamin address dinki, bawai nagane bane nayi niyyar idan naje unguwar  naku sai ki nuna mini guri in saukeki... bayan mun isa unguwarku na miki magana nace mun kawo naji shiru ina ta magana kikayi shiru nadauka gyaleni kikayi nayi magana har na gaji sai kawai najuya kan motana na wuce gida nakai saqon baba....

Mun kama hanyar gidana in dauko wani abu bayan na iso nan sai na qara miki magana shiru,ba motsi  na tabaki naji bakya nunfashi, hankakina ya tashi matuqa, tsoro da fargabar idan kin mutu yaxanyi dake ya kamani..!!!  a haka na daukokoki na kawo ki dakina batare da na bari kowa ya ganki ba, dama ni Dr ne, na miki treatment, na qara miki ruwa har zuwa lokacin da kika farfado kika fara xagina,to kinji ataqaice yanda akayi na samoki, ni banida alaqa da wata sister khadee hasalima ko sunan ban tabajiba, kuma xan gaya miki Gaskiyar magana sonki nakeyi,taji wani dummm... aranta tace idan dai xaka kaini gida mai sauqi ne, ya qara mata mata bayanin lahinda ya sami kanshi dazu na ganinta da yayi, kuma ya nuna mata cameran da yake ganinta idan zai kawo mata abinci dan bayason ganinta, tun ranar da ta mareshi kuma yayi alqawarin horata har na kwana bakwai yama yi nufin keta mata mutunchi Allahne ya kareta sai kuma Allah ya taimaketa, nan itama tabashi haquri rashin kunyar da ta mar da taimakon da ya mata, takuma hadamai da labarin abinda ya faru daga farko har qarshe, yayi mamakin irin zuciyanta da kuma yanda take iya dukan namiji, yaga marin da tayiwa unlce din sista khadee ne ya janyo mata haka, dadewar da tayi anan ma sanadin marin da ta mishine, yanxu dai kisharya inkaiki gurin inna....
 
ASHE KAINE MIJINA?? 30

Na HAUWA M. JABO..

Ki shirya inkaiki gurin inna, wani sanyi naji araina,nayi tsalle da ihu, inata dariya murna... "nima jabo na matsu inga yanda xata kaya gaba",tace ai ashirye nake, ya juyo ya kalleni karo na farko daya kalleni tunda ya shigo dakinnan, kin cire mini tufafina? Eh yanzu zan cire, shine kike cewa kin sharya? Murmushin da tayi ya qara  daga mishi hankali, yasa kai idan kin shirya ina waje ki fito muje, yana fita na cire kayanshi na maida wayanda ya siyomin koda sunyi datti amma su na saka hakanan nafito na sameshi, abin mamaki gidan da nake qaton qaskene kuma part part ne ga mutane a ciki suna kai da kawo, a raina nace dana sani da na riqa dukan qofa tun Lokacin ai da xa'a jiyoni a bude min da yanzu na tsufa gida.

Mun isa unguwar mu da misalin qarfe tara na yamma, na rangada sallama inna tana ganina ta fara salati Sai kawai ta fashe da kuka nima na fashe da kuka, tana kuka ina inayi tayi wa yaya waya ko minti biyar ba'ayiba ya iso, yana zuwa naje na rungumeshi ina kuka,  araina nace ni ban rameba su suka rame, duk sai suka qara bani tausayi, nan aka fara tambayar ya akayi? Na koro musu bayani daga farko har qarshe, sun tausayamin kuma mamaki ya kama su, suka gayamin rashin mutuncin da sista khadee ta musu, anan dai wanda ya kawoni shima yayi bayani nashi, sai dai yayi qarya sabida ce musu yayi sai jiya da dare na farfado kuma yace tsoro yaji ganin lalacewar qasa kada yakaini gurin yan sanda ya janyo wa kanshi wani abin daban, to hakadai a ka jajantawa juna akayi waya qauye aka sanar dasu an ganni iyayen nura sunji dadi Sosai inna tace gobe sai ayi sadaka......

ASHE KAINE MIJINA?? 31

Na HAUWA M.JABO...

Sai ayi sadaka tunda Allah ya mayar dani gida, yaya sai kallona yakeyi kamar wata baquwa na tashi naje na haye shi ina dariya sai naga uncle habeeb ya daure fuska na rasa dalili,anyi hira sosai inna tana bada labarin yanda yaya yayi shima yana bada labarin yanda tayi cikana kamar ya qulle dan dariya," nima jabo na dara??"munchi mun qoshi  yaya yace sai na warware zan koma makaranta uncle habeeb dai ya qara gaba abinshi ya karbi number yy data inna.....

Yy ya Siyo min siyomin sabuwar wayah da sabon sim, sabon gata da kulawa wajen inna da yaya ba'a magana, kusan kullum sai unle habeeb yazo gidan mu har dai ya shaqu da inna ya zama kamar dan gida tun da inna ta fahimci sona yakeyi kamin ma ya furta take bashi labarin nura kuma ta gaya mishi Lallai wasiyar mahaifinane in auri nura, baiji dadin rasani da yayiba hakan kuma baisa mun daina zumunci dashiba, amma ya rasa wani farin cikin sa, yan gidan su sun sammu muma munsansu har xumunci mukeyi.......

Saida nayi wata biyu chur a gida sannan aka fara maganar komawata makaranta, yaya habeeb yace a chanzamin skull, haka kuwa akayi aka chanza skull, ban qara jin labarin sister khadee ba,

Ranan munje bakin auren qanwar uncle habeeb nida inna muna dawowa a hanya mota tayi tsayinta na kunna na kunna taqi tashi munanan tsaye saiga wasu
Guys sun wuce sai inna ta musu hannu har sun wuce Sosai sai suka dawo, da yake ina cikin motar ne, ki fito ga wasu yan samari nan na tsayar kinsan ba jin maganata zasuyiba, nafito suna zuwa suka fito motar su, sai dayan guyx din yace kace kamar kasan matar kuma kace tsohuwace, eh Wallahi kafa San yau tin safe nakejin faduwar gaba, qirjina sai dukan 3..3 yakeyi i don't know y!!! Yanxu ma Sai naji ya qaru, ita tsohuwar fa?? Share Ashe ba tsohuwa bace manyan kayace, suka kwashe da dariya, suna qoqarin tsallakowa, amma fa daga farko tsaHowar dana gani kamar na santa amma na manta inda nasan ta, any how tunda munzo 

mutaimaka musu kawai,  inna dama tana ganin sun dawo ta ta shige mota abinta, abokin deen ya shiga motar yayi danne danne sai kawai motar ta tashi, tunda suka xo naji jikina ya chanxa na Kasa dago kai in kalle gefen da nakejin ana kallona, muje ko deen dayan abokin ya fada amma ina deen yayi Nisa,Na dago da gyar na kalle mai maganar nayi godiya zan zaga yace idan ba damuwa ki bamu number ki, murna kamar ta kashe deen, Lallai yayi dacen aboki da yake gane duk wata matsala tashi, na bashi number bada son raina ba dan kawai mutunchin da suka mana ne.....

ASHE KAINE MIJINA?? 32

Na HAUWA M. JABO...

Har ya juya xai tafi sai yaga bari dai yayi ta maxa yaji sunanta,.!!

Ehem, am, inn, duk ya dabirce, dagyar ya iya furta kalma biyu M deen  by name, what of u please??
,
Na kalleshi a raina nace wannan kamar wani gaula daga kallon mutane kuma sai Kasa magana!!
Nace bari in fada mar Sunan da inna tace babana yana kirana dashi,
M hulwah, wawoo nice name, yamin wani murmushi bansan dalilin da yasa naji rass ba,nima na maida mai, owk hulwatiy sai kinjimu, yana murmushi yana sosa qeya kamar mara gaskiya, suka wuce nashiga mota inna tace da ace sun ganni ko taimakon ma bazasuyiba, na kyalkyale da daria wallahi inna akwi ki da zance akanme bazasu taimakamikiba,? To Sunga tsohuwa,  Haka mukayi ta hira har muka isa gida, muna isa naji saqo a whtasapp, na duba naga sabuwar number kawai sai nayi blocking din number, dan Banason shirme, kuma nasan ban bama kowa number naba,

sam na manta da na hadu da wani wai shi deen har na bashi number,  sai da dare na kwanta bacci amma ina bacci yaqi zuwa, sai juyi nake, karo na farko a tarihin rayuwata da na taba tsayawa  tunanin Wani namiji, sai karanto fuskarshi nake,murmushin da ya mun yake min gixo bacci yavqaura cemin, araina nace wallahi guy din ya hadu sosai, Nasami kaina da qara yin murmushi na janwo pillow na matse gamm!!  lokaci daya na tuna an mini magana ta whatasapp my be ma shine nayi blocking dinsa ai kuwa dana chuchi kaina, na je neman phone din, na janyo ta qasan dadduma naga 8 miss call, na tabbatarda cewa shine, yayo sms  hudu, na budeshi,
Na duba number sai naga d Same number da aka kirani da ita aka mun magana ta whatasapp akamin sms, na bude nace salam,
Kamar yana jira dama, ya fara surutuai...
Haba hulwaty, ya zan kiraki kiki dauka kinsan kuwa abinda nakeji araina......???

Post a Comment

 
Top