0
AMINAN JUNA



AMINNAN JUNA

Na Xarah~B~B

AMINAN JUNA

~191-195~



Washe gari tun safe suka hau hada kayan zuwa Sokoto banda Amrah da tayi jugum duk ta fita hayyacinta, Futha kam ta fita batunta dan ba kadan take tsananin jin haushin Amrah ba.
Jin shiru har sun fito parlour amma babu amrah yasa ammi ta shiga dakinsu, ta sameta kamar mahaukaciya sai sabbatu take ita daya tana fadin "ni Zarah! Ni kikaiwa kwacen saurayi? Hubby na wanda nake burin aure, yake kiranki da swty, kin cuce ni, bazan taba yafe miki ba a cikin babin soyayya".
Ammi taita magana amma shiru bata ma san tanayi ba, saida ta tafa hannu da qarfi sannan ta zabura hawaye nabi mata kumatu tace "na'am ammi, ina kwana?".

"Ba wannan ba, me kike da har yanxu baki shirya ba? Kuma kin san ke muke jira",
Cikin kalar tausayi tace "ammi ai ban ma san har garin ya waye ba, tunda nayi sallah nake anan, barin hada kayan yanxu dama komai a shirye yake", Ammi tace "tou barin turo futha sai ta tayaki harhadawa", "noo ki barshi ammi ai daman duk a hade suke, gyrane kawai zanyi nasan yanxu zan gama" tayi saurin fadi.

Cikin qanqanin lokaci amrah ta hada komai nata, da qyar take jan trolly dinta ta fito dashi parlour, ta samu Ammi, futha da yaa affan zaune kowa yayi tagumi, kowan su da abnda yake tunani a ranshi, miqewa ammi tayi lokacinda Amrah ta fito tace "Affan karbi akwatinta ka kai a mota", cikin rashin kuzari ya karba ba tare da yace mata uffan ba, bin bayanshi sukayi ya bude masu motar futha a gaba sai Ammi da amrah a baya..........

Urs Zarah~B~B


AMINAN JUNA

~ 196-200~

Tafiya suke cikin natsuwa babu gudu dan ammi bata son ana gudu da ita a mota, qarfe 1:40 suka isa babban birnin Sokoto. Basu zarce ko ina ba sai gidansu Amrah.


"Ahh lale marhaban da mutanen katsina, tafiya haka babu sanarwa, sannunku sannku", momy ce ke fadin haka fuskarta sake tare da faraa.
Ammi tace "wlh kuwa maman Amrah, yauwa yauwa, mun sameku lafiya?"
"Lafiya lau ya hanya?"
"Alhamdulillah" Ammi ta fada.


Bayan sun samu natsuwa sunci abinci sunci, Amrah ta koma daki taci gaba da jimami. Futha kuwa qaramin parlour ta koma ta kunna kallo. Yaa Affan ya tafi masallaci sallar jumu'ah dan a ranar jumu'ah ne.
Ya rage saura Ammi da momy kawai a dakin. Ammi tace "nasan zakiyi mamakin ganin mu kwatsam ba tare da kun san da zuwan mu ba"

Momy tace "gaskiya ne, wannan xuwan bazatar ya daure min kai",
Ammi ta nisa tukuna tace "wata 'yar matsala ce ke tafe damu, inda kin kula zakiga yanda Amrah ta canza duk babu walwala a tare da ita",
"Ehh na kula da haka kam, me yake faruwa ne?"
Nan Ammi ta kwashe duk abnda ta sani tun farko har qarshe ta fadwa momy, harda tafiyarda Zarah tayi ma ta fada mata.
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN" kawai momy ke fadi, "tou ai ammi bamuga ta zamaba, dole a bincika Zarah idan gida ta dawo, Allah dai ya rufa mana asiri yasa tana gida",
Ammi tace "amin".

Sallamar yaa affan ce ta katse masu zancen da suke, momy tace Affan ko kai zaka kaimu gidansu Zarah? Sai na ringa gwada maka hanya tunda babu nisa ma daga nan, wlh drivern mu yayi tafiya ne, dady kuma yana office bai dawo ba".

Dad'I sosai Affan yaji dan an ambaci Zarah, rabonshi da samun natsuwa yau kwana uku kenan tun barin Zarah katsina.
"Muje momy a shirye nake", ya fada tare da fita daga dakin. Caraf futha ta fito tace "dan allah aje dani ammi", Ammi tace "ya za'ayi a tafi dake bayan kuma ga yar uwarki? Ki zauna ki jira mu bazamu dade ba, kedai kiyi mana fatan samun nasarah kawai".
Momy tace "aahh baza'ayi haka ba, jeki sako hijabinki mu tafi, itma Amrah ai ba wani ya hanata ba",
Kaman daga sama sukaji Amrah tace "Allah ma ya kyauta min inje gidansu maciyya amana, ni wlh ko sunanta ma bana son jin an ambata".

Ammi tace "rufewa mutane baki daallah can", a fusace ta fita tabi bayan yaa affan dake tsaye bakin mota yana jiransu.........

Urs Zarah~B~B


AMINAN JUNA

~ 181-185~


Futha tace "amin yaya, amma kam gaskiya Amrah na cikin rudin soyayya kuma......", bata qarasa maganar ba taji Amrah na fadin "sannu magulmaciya, wato gulmata kika kawo gurin yaa Affan ko? Tou wlh koma me zaku fada sai dai ku fada, nace babu ni babu Zarah, na yanke duk wata alaqa dake tsakanin mu, kuma ma da kike fad'in haka, shin wai ni na kori Zarah ne? A gabanki fa akayi komai, ban koreta ba ita ta kori kanta", Futha ranta bace tace "amma ko baki furta kora ba ai kin furta me kama da haka, kin mata gori Amrah, wanda ya kamata ace kinfi qarfin nan, an daina yayin gori fa, an barwa qananan yara, ke kuma yanzu kin wuce minzalin qananan yara", cikin masifa Amrah tace "well! Ki fadi duk abnda kike so Futha, nasan a gidanku nake dole na dauki duk wata baqar maganar...", saukar marin da taji ne ya hana ta qaraaasa maganar da take, yaa affan ne ya mareta ta dafe kumcinta, bata ankara ba ta qara jin saukar wani marin, ba shiri ta fadi qasa tana kuka kamar ranta zai fita........

Urs Zarah~B~B

AMINAN JUNA

~186-190~



Da sauri ammi ta fito jin sautin kuka na tashi, cin burki tayi a lokacin da taga amrah kwance a qasa shame shame tana kuka, da hanzari ta isa inda Amrah take, ta dafata tace "daughter! Me ya sameki kike kuka?", Amrah ido rufe ko kallon ammi batayi ba, ganin bata da niyyar bata ansa ne yasa tace "kai Affan me kayiwa Amrah? Futha meke faruwa ne? Answer me mana, am asking youh, tell me what happened with my daughter?", kasa bata ansa sukayi su duka, sun dauki kamar munti 15 a haka, ganin ammi na kuka hawayen ta na ta fita yasa Affan gurfanawa a gabanta, ya dafa kafadarta yace "ammi kuka kike? Me ya saka ki kuka? Rabo na da ganin kukanki tun rasuwar abbah, pls kiyi haquri", 

sai a lokacin ammi tace "ba dole nayi kuka ba Affan, nayi nayi daku kunqi fada mun abnda yake faruwa, ga yarinya nata faman kuka kuma nasan kun san komai", cikin rashin son fada mata yace "Ammi lafi na ne, nine na mareta" nan ya kwashe komai daya faru ya fada ma ammi, yasha fada sosai shida futha, da qyar ta samu ta rarrashi Amrah tayi shiru amma da sharadi, wai dole sai ta koma Sokoto gobe, ammi tace babu komai tare ma zasu tafi daga nan har su bincika labarin Zarah, ranar haka suka kwana kowa cikin takaici, ita Amrah babban haushinta ma idan ta kira Farouk baya dauka, daga qarshe ma sai yayi off na layinshi.............

Urs Zarah~B~B

Post a Comment

 
Top