Pages

12 Jun 2016

HASKEN IDANIYA episode 4 -- 17

 HASKEN IDANIYA






HASKEIDANIYA

parts 4

Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo

Duk da Sumayya ta san cewa wa iita suke ihu da sowan,ko a jikin ta wai an mintsili kakkausa,in da sabo ta saba da wannan,shi ya sa ba ta fiya san shiga mutane ba saboda halittar da Allah ya ma ta, na daukan idan jama'a,musammam in ta na zaune ko tsaye,amma da ta taka sai ka ji reactions iri-iri wajan mutane,ita ta ma kasa gane dalili,ko kanta aka fara nakasa sai haka.

***********

Sumayya kenan,! budurwa mai kyawun halitta da sura,diyar Alhaji Hashim da Huwaila. Alhaji Hashim be da arziki na kudi sai na 'ya'ya,Allah ya arzuta shi da 'ya'ya mata har hudu ma su kyawun burgewa kasancewar sa fulben kan dutse,cirani ya kawo shi birni,nan ya yada zango shi da matar shi Huwaila cikin birnin kano a wata unguwa da ake kira unguwa uku.
Sumayya ce diyar su ta fari,sai kanan ta Bilkisu,Maryam da kuma autar su mai suna Habiba suna kiranta da lele.

Tsabar kyan su da kyar Bilkisu da Maryam su ka karasa secondry sch aka mu su aure, saboda yanda maxa suke kali a gofar gidansu kuma maxa masu karba sunan Maxa masu kudi yaran su da manyan su ke mu su aringizo wajen neman auren su,amma fa banda Sumayya,wanda har ta shiga jami'a ba tsayayye kuma itama gata kyakyawa ce ta qarshe, sai samarin iska,ko kuma talakawa,gashi kannan ta biyu sun yi aure,ko lele ma da ke SS3 yanzu samarin ta ma su hali ne,kuma kullum cikin yi ma ta hidima da kashe ma ta kudi su ke.

Hakan ya sa Huwaila " mamansu " wacce su ke kira Gwaggo tsangwamar Sumayya,gani ta ke Sumayyar ta fita dabam cikin yan uwanta,gashi indai kyau da diri ne duk ta fisu,tsabar diri da kyan jiki irin na Sumayya ya sa ba ta iya fita sai da hijabin ta har kasa,dan ta gane shi hijabi sutura ne,daraja ne kuma girma ne ga diya mace..!! in ka dauke cilla kafa da rashin kwalliya na fuska kanen ta ba su fita da komai ba,amma Gwaggo gani ta ke ba ta da kashin arziki,gashi sai tsufa ta ke ba mashinshini,kowa za ka gan shi da abun zamani a gidan  nasu amma banda Sumayya, wajan Baban su wanda su ke kira Abbu ne kawai ta ke samin sauki,wanda tin da ralural kafa ta sameta asanadiyar allura da wata Nurse din bogi ta ma ta sanda ta ke da shekaru goma a duniya kafar ta na dama ya  sami matsala,ba ta iya taka shi,sai dai ta dan cilla qafar har xuwa Yanxu......
 
 HASKEN DANIYA

parts  5

Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo

Sumayya ma Northwest ta ke,ta na karanta B.SC. ACCOUNTING,200level,ita ce kwaruwar su,dan wajan kwakwalwa kowa yana sarara mata,guruwa ce by nature.

***********

Suna tafiya har suka qurewa ganin Moh... Wanda lokaci daya ya dawo hayyacinsa yadan kallesu james yaga basu kula dashii da yanayin kallon da yake mataba, sai kawai ya gyara xamansa  ya fuske abinsa Moh... Kenan !  tafe ta ke tare da idi dan ajin su,dan dama shi ta ke jira a joint din,  in ba dan ya karbi note din ta ba ya je yayi  photocopy, sai  sukayi dashi akan za ta jira shi a wajan, da nan gurin sam ba wajan zaman ta ba ne. Duk da dai ba ta dade da fara ganin Idi a ajin su ba,shi ne mutum daya da ta ke magana da shi,shi ma din shisshigin sa ya sa dan dole ta dan sake da shi. Kuma ya ce da ita ya shigo ta D.E ne so daga 200level din ya fara kenan.!

Wajan da dalibai ke hawa motar haya su ka karasa,dalibai an taru amma ba mota,Idi ya kalle ta tare da fadin Sumayya anya kuwa ma jira?ki ga yawan ma su jiran motar nan,ko ta zo ba za ta kwashe mu duka ba. Sumayya ta murmusa tare da fadin ai dama wajan nan kullum haka ya ke a cike,amma da mun yi hakuri mota ta zo da kadan da kadan za ka ga ana raguwa,dan dai kawai
ba ka saba ba ne amma ka jira kadan motan xaixo,  Idi ya ce gaskiya dai,gobe dan dole na dauko lifan dina wannan jiran haka ai sai mukai dare a nan gurin hmmm. Kawai tace masa.!

Nan suka tsaya jiran mota,Idi dai yanata mata hira,da ke Sumayya ba da ganan ba wajan surutu,ita sai ta taya shi,amma da ta kawo ma sa zancen karatu ko ya shafi makarantar sai ya kauce,sam ba ta kawo komai cikin ranta ba.

A gaban idan su motoci biyu su na zuwa suna tafiya amma ba sa samin hawa,Idi ya ce kin ga Sumayya zo mu ta ka zuwa gate kawai,in mu ka tsaya jiran mota za mu kusa kwana anan. Koya kikagani!?  Zuciyar Sumayya daya ta ce Idi rana akwai rana fa!!,ina jin tsoran zafin rana, kuma kaga daga nan xuwa gate da nisa.!

Idi ya ce kar ta damu,ta dan cikin jeji za su yanka,ba rana sosai kuma tafi kusa.! Sumayya ta ruke baki,jeji?ana bi ne?ya ce eh ma na,kin ga wasu ma can sun nufa gate din ta jeji,ai kuwa Sumayya ta hango wasu su hudu sun yi nisa,dan haka sai ta yarda su ka mike kafa,suma su ka yanki hanya,tana dan cilla kafar ta.

Tafiya su ke,tin Sumayya ta na hango na gaban su har su ka bace mu su,tin ba ta jin komai har ta fara tsorata,shi kuwa Idi sam be lura ba,sai labaran sa na kanzan kurage yakebata,can da sukayi nisa sosai sai cewa ya yi wai ya gaji su huta. Mu huta?Sumayya ta tambaye shi cike da haushin kan ta da dana sanin biyo shi da ta yi,dan ba ta san ta yi wauta ba sai yanzu,ya tsakiyar jeji zai ce su huta!ina ka ga wajan hutu anan  Idi? bare ma menene na hutun da  son hutun na ke na yi ai dana xauna a bus stop mana in ta hutawa har mota ta zo.....
ta na magana ne ta na tafiyar ta..

HASKEN DANIYA

parts  6

Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.

Idi da ya dan tsaya,ya bita da kallo zuciyar sa na raya ma sa wani abu. Ta waiga gefanta bata ganshi ba,sai ita ma din ta tsaya ta juyo ta na haba Idi ba dai tsayawa ka yi ba? Koni mace ban gajiba sai kai, dan Allah kaxo muje mana.!!! wani murmushi mai wuyar fahimta ya sakar ma ta,sannan ya taho ba tare da ya tanka ma ta ba,tin daga nan Sumayya ta sha jinin jikin ta. Jerawa su ka yi ba tare da wani ya sake tankawa ba,kowa da abun da ya ke sakawa cikin ran sa.

Ba ta ankara ba sai ji ta yi idi ya ruku mata hannun,gaban ta yayi mugun faduwa,ta fizge da sauri tare da fadin Auzubillahi!idi menene haka? kan ka daya kuwa? idunun sa wuki wuki,ya na sosa kyeya ya na fadin yi hakuri gani nayi zaki taka kusa!a fusace ta ce idan  zan taka kusa ai sai ka fada min ma na!har sai ka taba ni? Waima tsaya ina kusan ya ke? Ya fara kame kame,eh ashe ido na ne be gani da kyau ba,eh gizo ya min....kallan banza ta watsa ma sa,ta ce ya kamata idanun ka su na gani da kyau! Dan ni bansan shashanci!ta juya za ta ci gaba da tafiya,dan Allah Allah ta ke ta bulle titi, gashi bata iya sauri sosai yanda take cilla qafarta. Dan kuwa idi ya fara firgita ta. Me za ta gani?idi ne ya sha gaban ta,tare da fadin Sumayya tsaya ki ji,iya kan sani na da ke,ban da burin da ya wuce na ga abunda ki ke boyewa cikin hijabin ki,ma'ana na gan ki ba hijabi,dan gaskiya har mafarkin ki na ke wai kin cire wannan xunbulelen hijabi gaba na!!!!Baki bude ta yi kamar an kwarara mata ruwan kankara,da kyar ta ji muryar ta na fadin Idi!dan Allah Idi  idan wasa ka ke dan Allah ba na so,ka dena dan Allah.......Idi ya ce wani wasa kuma!wallahi da gaske na ke,kin ga dai daga ni sai ke,ba wani abu,kawai dan abubuwa za mu yi.....ji ka ke tas!Sumayya ta wanke shi da mari,ta kara da shashasha,dan iska kawai....Allah sai ya saka min!ta juya da sauri ta na hawaye ta na tafiya,so ta ke ta zura a guje,amma ta na gudun kar Idi ya gane ta tsorata ya sami lasisin ci ma ta fuska,dan tsaye ta bar shi,hannun sa bisa kuncin sa fuskarsa cike da mamaki..

Idi ya ga Sumayya Sauri ta ke sose,dan haka sai shi ma ya bita da sauri,ba ta ankara ba sai ga mutum a gaban ta,ta yi saurin juyawa za ta koma baya a guje ya wafco ta ya na kokarin fizge hijabin jikin ta,gaba daya ya sauya kama,yayi daban da Idin da ta sani cikin kwanakin nan!nan Summayya ta shiga kokarin kwatar kanta ta,hannun ta gam ta ruke hijab din ta a jikin ta,wani mari ya sakar ma ta sai da ta ga wuta a idon ta dan rikicewa ba ta san sanda ta saki hijabin ba,Idi ya sami damar fuzgewa.tuni ta durkushe a kasa ta na fadin Innalillahi wainnailaihi raji'un.....

HASKEN IDANIYA 

parts 7

Na Hauwa M. Jabo & khadija sidi.

Moh tafe bisa bike din shi ya na shalla gudu,Su Shamo biye da shi,ya mu su nisa sosai,amma ina sai ya ji bike din na sa na ba shi wani irin kara,a dole ya dan yi slow down,dan ya gasgata zaton sa....Shamo,James,Moh,Mike duka da dai dai su ka wuce shi yayin da shi kuma ya dan ja gefe ya sauka ya fadin Damn it!kamar daga sama ya ke jiyo ihu,mtsw ya ja tsaki,ya na mamakin me ya sa mata su ka fiya san ihu a rayuwar su!

Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un.!Haka ta riqa fada ta toshe kunnuwan ta da idonta tana ihuuu iya qarfin ta, tana jiran hukuncin Allah..!
Iya kar kulewa Idi ya kule,ya daga magana sai ihu,ya ce ke dallah kar ki taran jama'a,dallah ki min shiru!!gaba daya ya rude, ganin ba ta da niyyar sauraran sa yayi kanta yana kokarin dago fuskar ta ya toshe bakin ya huta,nan ta saki saban ihun....fizgar idi aka yi,sai ga shi hannun maza,ba jira ya ji saukar tafi ba sassautawa a fuskar sa,tuni idanun sa sun kumbura,ya daga ido dan duban wanda ya ma sa dirar mikiya,lokaci daya Sumayya ta tsaya da ihun ta jin sautin marin,a hankali ta bude idanun ta ta dago,nan su ka sauka kan Moh,da be ma san ta na kallan sa ba,in ran sa yayi dubu ya baci,ihun Sumayya ya hana shi samin nutsuwa ya duba bike din shi,tin ya na jurewa har ya nufo in da sautin ihun ke tashi rai bace ba da san ran sa ba, da kudirin tsawatarwa mai ihun dan ya tabbata ko ma wacece kan ne ba dadi,da kyar ya iya bullewa inda su ke ga mamakin sa ya ga mace durkushe ta na ihu ga wani gaja ya sa iya karfin sa ya kokarin dago da fuskar ta,be San da ya fizgo shi ba ya hau dukansa kamar Allah ya aiko shi.

Moh yadan tsaqaita dukan sa,  ya tambayi idi waye shi?
Waye ubanshi ?
Kuma miya hadinshi da ita?.
Idi yayi shiru sai mar mar yake da Ido baki duk ya kunbura.!
Haka Moh ya fara laluben jikin idi qarshe yayi karo da ID Card dinsa yaga Ashe ma idi ba student bane,  Moh ya mishi wani kallon da sai da Idi ya saki fitsari ya na fadin wlh na tuba,yasin na tuba.... Wani irin ihu Sumayya ta saki,Moh be san sanda ya saki Idi ba....ya nufi inda Sumayya ta a hanzarce,shi kuwa Idi ya sami damar cika rigar sa da iska.
Sumayya ta tashi da sauri ta na cilla kafa,ta ma manta da batun hijab,ta yo wajan Moh da ya yo gun ta cikin hanzari ya na menene?menene kuma?ganin fuskar ta da kuma yanda ta ke dan cilla kafar ta ta ya gane yarinyar nan ce ta joint.
Bayan sa ta buya,ta nuna mishi dan yatsa, ya yi jeem nadan lokaci yana kallon abinda ya sakata wannan ihu. kurbace fa tabi ta gefen ta ta wuce, lallai mata mata ne.! Cike da takaicin rasa Idi ya durkusa tare da dauko hijabin na ta,ba tare da ya  kalle ta ba ya jefa ma ta,ya yi gaba abun sa. Jiki na rawa ta sanya hijabin,gami da kamkame jakar ta,ta bi bayan sa da sauri,abun ku da dogon namiji har ya ma ta nisa.

Ya na zuwa gun bike din sa be yi wata wata ba ya haye,
dan tsabar haushin Sumayya da ya ke ji, aranshi yake saqawa, dama haka mata suke so careless!? Ya xa'ayi ta kula mutumin da bata masan koshi waye ba!?  Ga baqin cikin idi ya kubce masa sabida tsoron kulba, wani tsaki yaja, ya tada bike din ya tafi da gudun sa kamar zai tashi sama!ina duk saurin Sumayya hayaki ta tadda. Ta bi bayan shi da kallo ta so ace ta same shi ta ma sa godiya, aranta tace dama wannan yasan Allah har yasan wani abu wai taimako?. Ita kam abun da ya same ta yau kar Allah ya sa ya sami wata diya mace......bakin gate ya tadda su Son suna jiran sa,amma mai makon ya nuna ya gan su sai ma ya yi gaba abun sa,duk yanda su ka so su kamo shi ya gagara,ya mu su fintinkau,dole su ka hakura su ka kyale shi,ba shakka ran maza ya baci,amma ba su san dalili ba. Karo na farko da Moh ya dau hanyar gida shi kadai kullum da gang dinsa suke dawowa.!

Ita dai Sumy jiki na rawa sai sauri take tunda sun bullo titi, tana xuwa bada dadewa ba ta sami mota sai gida. Dama yunwa da kishin ruwa sun addabeta.
Tana isa gidan su gidan ba wani gida bane na azo a gani, kunsan dai gidan talaka mai rufin asirin Allah.!
Ta tura kyauren gidan raqaqaqaqa ta wuce cikin tana cilla yar qafarta,
Goggo ce tsakar gida xaune tana goge wasu takalmi tama Goggo sannu Goggo ta amsa mata sama sama.! Dama ta saba da yanda Goggon take mata....


HASKEN IDANIYA

parts  8.

Na khadija sidi & Hauwa M.Jabo

Goggo ba tama kula da yanda Sumayyah ta shigo biji biji ba sai tattalin goge takalmi ta ke yi, Sumy  ta bude baki xatayi magana kenan, sai ta ji kirarin Goggo, auta jaja Manya! Auta shalelen mata.! Auta alkhairin Allah.!  xoga takalmin ki na goge miki,  lele ta kalli Goggo, no Goggo basu xan sakaba wayanchan xan saka, ta nuna wasu takalmi da yatsan ta, jiki na rawa Goggo ta daukosu tana guga ta chi gaba da mata kirari Sumayya xaune tayi tagumi, tana kallon su idan da sabo ta saba ta goge ta dora mata gabanta ta saka. Goggo ta kalleta Daga sama har qasa, ta saka wasu damammun kaya duk yana nuna jikinta, tace lelen Goggo yar cas dake kingan ki kuwa!? Kin ga yanda kika hadu!? Lelena mai farin jini! Lele na yar albarka! Daga nan sai ina kenan? Lele tayi murmushi,  za mu restaurant ni da boi, inane haka ma?rastaran gun chin abinchi ko!?
To a dawo lafiya! Ai boi yaron arziki ne! Kizo min da mai dan  maiqo maiqo
Lele ta kalli yayarta a hantare,  tace Goggo irin kaxar ranar nan ta miki!?
Tace tayi autana lelena! Kinci kin gama, Ta fita tana yanga.!
Chan Sumy ta miqe tana cilla yar qafarta ta shiga kitchen  dauko abinci amma koda taje taga wayam. Tabi kwanuka da tukwane amma ko ina babu duk wayam.
Ta fito Goggo banga abinci na ba! Goggo ta tabe baki, da yake yau su lamin gangare taxo sai naba yaranta suka cinye abincin ki, sai ki jiga gari ko kuma ki jira na dare,
Goggo ta kalleta a yatsine, keba saurayi mai Dan damshi damshi ba bare kiyi waya a kawo miki mai dadi ki lasa, amfanin samari kenan, gaki nan kullum cikin balakayar hijabi kina share gari dashi.! Uwa uba ga nakasa wazai taya a haka.??
Wallahi ko nice gaba xanyi.!
Anya nidai Sumayya ban taba taka bakin jaba ba lokacinda nake da cikin ki ba kuwa? Shi yasa kike da wannan baqin jini ace mace ba mashinshini!.
Wai yauma haka kika dawo ba wanda ya biyo ki??.
Sumayya ta yi rau da ido ta ce wlh Goggo makaranta kawai na je, Goggo tace, da gidan uban ki nace kin je? ai kam sai ki ta zama haka ke kuwa, ga dai lele nan ki na ji ki na gani za ta tafi ta barki a gidan nan, sai mi ta zama mutane na tunanin ko kishiya ta kike, duk yarinyar dake unguwarnan kin qirmeta. sokuwa kawai..! ta shige daki ta barta, abin Duniya ya ishi Sumayya ko yunwar da takeji ta bace mata sai kawai ta shige daki tai ta kuka,!¡ gwanin ban tausayi,  ko ita ta daurawa kanta Wannan lalurar iyakar tsanar kenan!  bare kuma Allah ne ya daura mata,  dama ga bakin cikin abun da Idi yai mata Abu biyu suka bi suka dameta......

HASKEN IDANIYA

parts  9

Na khadija sidi & Hauwa M jabo.

********.

A bangaren Moh kuwa yana isa gida koda yaje sunyi baqi amma baiyi ta kansuba dama baxai wuce yace musu sannu ba. Amma yau ko sannun basu samuba, ya shige sashensa kawai ya fada saman gadon sa, baqin ciki ya isheshi, yayi ta juyi, farko a tunanin sa kubcewar idi ce take damun sa da kuma sakaci irin na mata.!
Sai daga baya ya gano cewa  hawayen Sumayyah ne daya gani suna zuba yafi damun sa, haka yayi ta juyi har guraren asuba..  baci, basha dagyar ya samu ya kora lemu "naga dai ya xuba wani abu fari a cikin lemun, nima jabo ban hangoba saida abokiyar ganin kwakwaf dina wato Khadija Sidi ta nuna min sannan na hango"

Su James kuwa sin ta kiran Moh a waya yaqi dauka saida suka kira zainab qanwar Moh sannan ta gaya musu cewa Moh yana gida.
Sannan hankalinsu ya kwanta dama  sunsan halin kayan su.

********

Yauma kamar kullum, Sumy ta shigo skull tana cillira yar qafarta,  tazo gun wani joint xata wuce sai wani shaqiyi ya taso da gudu tun kamin ta kawo, ya riqa jefa qafa kamar dai yanda Sumy take cillira tata qafar kuma ya iya yanda takeyi, har yanda takeyi da idonta ya iya,
Habawa tuni Guyz suka dau ihu..... Anan ne Moh shima da gang dinsa sunxo wucewa suka gani, Moh da ko shi  kayiwa abu saidai yasa a maka saiti..
yawani jaa burki da qarfi yaxo gurin yaga mi yake faruwa, ganin yanda ake ma Sumayya isgilanci,ta tsaya kamar sokuwa ta na kallan su ya dada kular da shi,ya rasa dalilin da ya sa yarinyar ke yawan tsirgawa a rayuwar sa,nd shez soo naive!  tsawa ya daka ma guy din,ya kamo shi ya gaura masa mari, wani guy dake gefen sa yace kai.! Shima Moh ya kwasheshi da mari,  tuni kowa a gurin ya shiga taitayin sa, ya juyo ya kalli  sumayyah ido cikin ido ya fara mata masifa, ba kya magana ne?ke bebiya ce or what?ba kya iya kare kan ki?dan me ya sa za ki bari a rai na ki? Saboda me ya sa?damn it lady!you ar driving me nuts!!ban san mace sokuwa!!!!!
Su james sunyi mamaki kwarai da gaske, dama ba su san ya taimaka ma ta akan Idi ba, sun dai ga kawai ran sa a bace tunda suka shigo skull din.
wannan ne karo na farko da sukaga Moh yake kare mace, bama karewa ba, shida ko  shiga harkar mace bayayi,  Dan Sam mata basa gaban sa kuma ba sa cikin tsarin rayuwar sa,
Haka sauran jama'a, suke mamaki, Moh mara magana na tada jijiyoyin wuya kan wata, wasu sun shekara uku a skull din but basu taba jin muryar Moh ba sai yau,  gashi har ya mari biyu daga cikin masu raina mata wayo!.
Matsawa ya yi kusa da Sumayyah ya tsaya,  yana  kalonta ido cikin ido yace;
Tunda baxaki iya kare kanki ba, as far as kina cikin skull dinnan u are mine.!
Ya juyo ya kalli mutanen da suke joint din da wayan da su ka zo kallo, da yan matan da suke son suji muryar Moh, ya Daga muryar sa da qarfi dama  Moh akwai loin voice saidai mai dadi ne voice dinsa.
Yace kowa ya saurare ni,nd you listen to me good,Wannan yarinyar kaya ta ce,  duk wanda ya haura gidan Moh... Xaiji makamai.! Wanda su ke nan su fadawa wanda ba sa nan!!!!!!!!!!
Sumy ta wani dare ido dajin xancen Moh......


HASKEN IDANIYA

parts 10

NA Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.

Kallan sa ta ke cike da mamaki,yau ga karfin hali barawo da sallama.... Moh kuwa cike da tunkaho juya ya bar wajan,su Shamu su ka rufa ma sa baya suma cike da mamakin abinda Moh yafada, bare ita Sumayya da mamaki ya daskarar da ita a tsaye,wannan dai ba shakka ya sha ta fada ma sa karya,aiko da ta zama....me ma ya ce? wai kayan sa fa!ai gwara duk makarantar su taru su ta takura ma ta akan ta xama kayansa!!abun da ta ke fada cikin ran ta kenan tayi dan tsaki ta zunbura baki ta juya abinta, Sai da su Moh su ka bar wajan tukun maganganu su ka fara tashi,kowa sai bin Sumy ya ke da kallo,ma su nuna ta na yi,amma fa daga nesa nesa,tin da dai Moh ya ce kayan sa ce wa ya isa ya tinkare ta???

Sumayya ta ja jikin ta,ta na cilla kafa,daga gefe wata kyakkyawar budurwa ta ce kut!ashe ma gurguwa ce!!!!!!su cillere an sami matsayi....ta gefan ta zungure ta tare da fadin wlh Humaida ki iya bakin ki,kin dai san halin Moh!!Humaida ta dubi kawar ta da ake kira Aseeya,ta ce Aseey ba bu abun da ya shafe ni da maganar Moh,shi ya kira ta kayan sa,ni kuma shi ne kaya na.!! wlh ba zan saurara ma ta ba,duk kyau na da kudin baba na wannan gurguwar ce ta isa ta zama min matsala? Tana fada tana kallon sumy na cilla qafa, Aseeya ta girgiza kai,ashe dai iska na wahalar da mai kayan kara,kin ga tafiya ta!Aseeya ta juya,dama zaune suke cikin wani restaurant, jin an kira wasu yan mata a waya,wai Moh na fada saboda wata ya sa su fitowa da sauri suga sarauniyar da ake fada akanta, dan a xatonta wata hadaddiyar mace xasu gani sai kawai sukaga gurguwa na cillira qafa.
Humaida Ta na mita ta bi bayan Aseeya,fadi ta ke Aseey tsaya ki gani,sai na baki baki mamaki akan Moh wallahi komai xan iya yi......!

Sumayya kuwa sai da aka sami wata yar jin kwakwaf ta biyo ta,ta na tambayar dan Allah menene dangatar ki da Moh?Sumayya ba ta yi mamaki ba,dan ta san dalilin tambayar na ta,dan haka sai ce mata tayi ki tambaye shi ma na....ta yi tafiyar ta. Sumy Sai nanata maganar Moh ta ke cikin ran ta,wai be san mace sokuwa!!!!wato ita ce ma sokowa,da ma uban wa ya ce ya so ta!!!!!amma har ga Allah ita ma shakkar Moh ta ke.

Su Son suna san yi ma Moh maganar Sumayya,dan kuwa ya mu su ba zata,amma sam ya ki ba su room,da an dauko maganar sai ya mu su banza,su yi su gama,har su ka gaji su ma su ka basar....


HASKEIDANIYA

parts 11

Na Hauwa M. Jabo & Khadija Sidi.

***********

Washagari bayan Sumayya ta fito daga lecture ta ke jin lbryn assignment din da lecturer din Econs prof Abdulrahman ya bayar,kuma group assignment.   ne,presention za su yi,kuma ya ce shi da kan sa zai zabi wanda zai yi,gashi gobe goben nan zai fara zabar group din da za su yi. Tuni Sumayya ta garzaya in da aka kafe domin duba inda sunan ta ya afka. !

Da kayar ta iya gano sunan ta,gashi ko wanda su ke course daya ba ta sani ba,uwa uba Economics da Subsiding ta ke. Ta duba ba suna daya da ta sani a ciki,tayi jeeem a kasan takardar idonta suka fada qasan takardar taga ansa num da alama numbar group leader din ne,dan haka jiki na rawa ta dauka,ta fito da wayar ta Nokia rakani kashi da ta rabe biyu sai kyauro aka dauro yanda za ta na iya amfani da shi. Numbar ta dauka,ta ja gefe dan ta na da dan canji a wayar,bugu daya biyu,uku.....sannan ya daga.

Yanda ya ke maganar ma ka san dan zafin kai ne,cikin nutsuwa Sumayya ta ce dan Allah group leader din group C ne?ya ce eh ya aka yine?ta ce ni ma a group din na ke,sai yanzu na gani......toh sai me???ya rufe ta da fada,tintini da aka ba da assignment din ba ki neme ni ba sai yanzu da gobe za a yi submitting!!!! Cikin saukin kai ta ce dan Allah ka yi hakuri,wlh ban san da shi ba ne......kar ki fada min ba ki san da shi ba......ONE MINUTE REMAIN....wayar Sumy ce ta gargade ta,jin haka Sumayya ta ce dan girman Allah kudin waya na ne zai kare fada min inda ka ke sai na zo na ma ka bayani. Mtsw!ya ja tsaki,ki zo ki same ni village nan wajan masu photocopy, ba dadewa zan yi ba a gurin kiyi sauri.....

Sumayya ta yi saurin cewa to idan naxo gurin ta yaya zan gane ka?,ka ga wayana ba kudi......ya ce za ki ganni da red top, kuma in ba ki yi sauri ba....sai din din din....kudi ya kare MTN sun yi tsiya.

Da ke Sumayya ba ta wasa da harkar karatu,tuni ta nufi village,gashi ta yi ragon azanci ba ta tambayi sunan wajan me photocopy din ba,kuma duk duniya naira hamsin ce ta rage ma ta idan aka cire kudin mortar da zai kai ta gida.

Duk nisar da ke tsakanin Village da Economics dpmnt,a kankanin lokaci ta isa,ta yi neman duniya ta rasa wani mai red top,sai duba wayar ta take ko zai kira ta,nan fa wata dabara ta fado ma ta,MTN sun yi recharge card na #50,bari kawai ta kundige ta siya,hakan ko ta yi,amma ba ta sami guda ba sai ya bata yan #10 guda biyar,ganin haka sai ta rage biyu aka ba ta canji #20 ko ta rage zafi dan balain yunwa ta ke ji.


HASKE IDANIYA 

parts 12

Na Hauwa M. Jabo & Khadija Sidi.

Sai da ta kira kusan sau hudu ba ya dagawa,sai a na biyar din ya daga,sai ce ma ta yayi ya gaji da jira ya koma dpmnt,ta yi jiran sa anan yana xuwa,  Dan takaici ma kasa magana ta yi,ta yi shiru ta na tunanin rayuwa har yan kudin suka qare......

Tayi tsaki irin yaran nanne yan kauye ma su shigowa sch da awara, Sumayya ta hango,da saurin ta har ta na tuntube ta nufe su......

Moh tare da gang din sa na shirin fita da ga village Mike ya hanqii Sumayya gaban mai awara ta na cinikin awarar ishirin,dama tin shigowar su karbar wani handout Moh ya ishe su da mita,wai ya tsani wajen,it is too local,kar wanda ya kara sawa sanadin shi ya shigo wajan,wajan is disgusting!!!!!

Ganin Sumy sai abun ya yiwa Mike dadi,ya tabo Shamo gami da ma sa nuni da Sumayya,idanun sa na sauka kan ta ya saki dariya mugunta tare da fadin Moh na ga kayan ka!!! Cikin isa Moh ya waiga da sauri  ya na fadin kai gida na ka haura????? Shamo ya daga ma sa gira,kallan sa ya isa ga Sumayya,wacce ta gama cinikin awarar ta na #15 ta siyi pure wata na #5,ta ma sa cikin hijib zuciyar ta daya ta fara waige waige ta na neman Inda za ta samu ta buya ta danci ko cikin ta zai daina ma ta kugi.

God shez too local!!!Son ne ya fada ya na yamutsa, fuska,James ya kara da like seriously wannan abuncin kudan ne za ta ci.......kai wlh har ciki na ya murda!Shamo ya ruke ciki cikin zolaya. Kayan Moh kenan!!!!!Mike ne ke ma sa irin kallan is dat what u called urs?kafada Moh ya daga mu su,ba zato su ka ji ya ce kuna so Ku haura gida nafa, amma na mu ku uziri tin da Ku ne, na tafi wajan kaya na,you guys can get going...... Ya na magana ya na kallan in da Sumayya ta shiga,sannan shi ma ya biyo ta ba tare da ya sake kallan su ba. Moh is full of surprise indeed,dan kuwa ya firgita su Shamoo. Shi da ya ke ta mita shi ne ya koma cikin village da kan sa,wai wacece Sumayya ne da har ta isa haka???

Ganin wani dan lungu da shogo amma shagon a kulle da alama ma su shagon ba su fito ba ya sa Sumayya ta shiga,ta zauna kan dan dakali dan ba shakka wajan akwai surru,Allah Allah ta ke ta ci ta koma sarari kar group leader ya dawo,dan yunwa hannun ta har rawa ya ke ,ta dauko awarar ta daya,ta danna a baki kenan,ta ga kafafu biyu sanye da bakin takalmi mai bala'in kyau da tambarin prada tsaye gaban ta,baki cike da awara,ita ba ta tauna ba ita ba ta tofar ba,ita ba ta hadiye ba ta dago kan ta a hankali,manyan idanun ta ta sauke bisa fuskar Moh....gaban ta ya yi mummunar faduwa....

Ku biyo yar gidan Muhammad jabo & khadija sidi Dan jin ya xata qare Moh da summy dinsa a gurin.


HASKEN IDANIYA

parts  13

Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo

Ta qumsa Wara a baki ta mayar dashi gefe daya tsoro ne ya hanata koda motsi,
Yandama ya ke kallan na ta ne ya dada kular da ita, yayi tsaye gabanta ya bude qafafuwa hannun sa cikin aljihu ya tsura ma ta ido kamar me neman wani abunsa daya bata a bisa fuskar ta.! Ba shiri ta hadiye awarar bakin ta ba tare da tauna wara kuwa haka ya tsaya mata qebebe a maqoqaronta, ba ta san sanda ta bude pure wata ta shiga durawwba  ba kakkatawa, nan fa sai ta kware tana tari har da hawaye....duka kan idan sa, shi be tanka ba,be kuma ba ta wuri ba,ya dai zuba ma ta na mujiya. Sai da ta dan nutsu,ta na kokarin boye sauran awarar cikin hijabinta, ta dago fuskanceshi. ta ta ce lfy?ko na ma ka wani abu ne?dan Allah ka yi hakuri wlh ko na yi ba da sani na ba ne.....

Karo na fari da yaji maganar ta sosai idan aka dauke ihun da ta kurma rannan da ta shiga hannun Idi.... ba shakka ya na son yanayin  maganar ta, muryanta akwai sanyi ga tausayi, sai dai kash wanda ta ke a yanzu kular da shi ta ke!!wannan wata irin mace ce wai? mata da yawa idan aka mu su haka fada zasuyi!? ,dan me ya sa za a shiga gonar ta,amma ban da wannan sokuwar macen!!! abun da ya ke fada cikin ran sa kenan,ita kuma ganin ya ma ta shiru,ta dada rudewa,ita dai kam ta banu......tsoran sa ya dada lullube ta har ya kai ga da jin karar wayar ta da ke aje bisa cinyar ta,ta yi firgit ta tashi,wayar ta yi gefe,ta rabe biyu kyauran ya fita,ga ba3 a kasa,kallan da ya mata ya sa ta koma ta zauna da sauri ta na duban wayan.!

Sun kuyawa yayi,ya hado ma ta wayar,kyauran ya tsinke,dan haka be damu da ya hado da shi ba,ta na karba ta tashi da sauri,dan ta tabbatar group leader ne ke kiran ta,ta kallo Moh a tsorace  sai kawai  ta fita sarari ta na kokarin kunna wayar,ganin wani da red top ya na danna waya ya sa ta yi saurin karasawa ta na salama alaikum,dan Allah kai ne grp leader na grp C? T.......malama ya ina kiran ki za ki kashe waya!? ya hau ta bambami,da na tafi kinma kanki walhy, bawai nemoki xanyiba, kuma yanxu  an riga an gama typn sai dai ki sa sunan ki da biro a kasa, ya mika ma ta assignment din wulaqance,kan ta karba ta ji an yi caraf an karbe.....ta bi shi da kallo,shi kuma assignment din da ya karbe ya ke dubawa,ya toshe idanun sa da bakin shade.....wayyo har ta kusa mantawa da Moh ta yi zatan ya kama hanyar sa..shi kuwa group leader tuni ya sha jinin jikin sa,tin da ya hango Sumayya ya ga Moh,amma be yi zatan tare su ke ba,me ma zai hada shi da mace mai cilla kafa kamar Sumayya?da leader har Sumayya aka rasa mai magana.


HASKEN IDANIYA 

parts 14

Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.

Ko da Moh ya gama dan dube dubensa a takardar,sai ya daga assignment din da hannu daya a wulaqancce,ji ka ke kyeeeet!!!!! Ya raba biyu,Sumayya ta dora hannu biyu saman kanta,shi kuwa G Leader idanu ya fidda hankali a tashe.
Moh ya watsa ma sa assignment din,sannan ya sa hannu a aljihu,ya fidda kudi ya watsa ma sa,tare da fadin ka tabbatar ka sa sunan ta barobaro a takardar, & yanxu maxa maxa ka sake sabon typn, sannan ka ba ta copy din ta da na wa!nd never talk to her in dat manner again!!!mark words na gane ka!!!!!! jiki na rawa kamar ba shi ne ke ma ta tsawa ba ya durkusa ya na hade kudi da assignment din da Moh ya watsa ma sa ya tattara jiki na rawa yabar gurin, har ya tafi ya juyo ya sunankima!? Kamin ta bashi amsa Moh ya dage shade dinsa ya masa wani kallo mai cike da ma'ana tuni group leader ya kama gabansa.!!


************


Moh ya dubi Sumayya cikin natsuwa gami da mika ma ta wani abu,ko da ta duba sai ta ga sauran awarar ta ne, lokacinda aka kirata ta xubarr kamar baxata karbaba sai kawai ta karba a kunya ce,tama kasa cema sa komai,koda tacedin tasan ba xata sami amsa ba,har ya juya zai tafi ya dada juyowa,ya dan zare shade din yanda za ta iya ganin kwayar idanun sa,wani kallo ya ma ta da ita kan ta ba ta san fassarar sa ba,ta ji lion voice din shi ya ce,eat well nd healthy,you too skinny out of your hijab......ya mayar da shade din sa, ya juya ya na wannan tafiyarshi cike da takama ya na budawa, ya bar Sumayya da bin shi da kallo,ta ce Allah ya isa Idi ka cuce ni wallahi gashi sanadiyar ka  Moh ya ga jikin ta!!.....Hajia idan kin shirya muje ki gaya mun sunan naki a kara da sunan naki ko, group leader ne dayaga Moh ya wuce shine ya dawo tambayar sunan ta. Yana muemushi yace, Allah ya so ina da sauran copies din.... Muryar group Leader ne ya sa ta dauke idanun ta daga kallan Moh,cike da mamaki  take kallon group leader din sai ka ce ba shi ke ma ta tsawa ba dazu, gaba daya ya shiga hayyacin sa,dama ance karan ba na shi ke maganin zoman bana ba shakka.!

Cikin kankani lokaci ya sa aka sa sunan ta,ya ba ta copies biyu. Duk da ba ta da kudi ta ce nawa ake hadawa ne?cike da nutsuwa ya ce ahh ba komai,ai Moh ya rufe wannan maganar,ta kara da cewa biyu fa ka bani?ya ce eh haka ya ce na baki,ko ba ki ji shi ba ne?,amma dan Allah menene gamin ki da shi?Ba tare da damuwa ba Sumayya ta ce ba komai fa. Leader ya gyada kai,tare da fadin ki de bi a hankali,ki kuma san da wa ki ke harka,idan kunne ya ji jiki ya tsira.!.
Ya wuce ya bar Sumayya ta na oho dai,can ma sa,ni ina ruwa na da shi,menene gamin wake da gari ma?

***********

HASKEN IDANIYA

parts 15

Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.

Wajan shabiyun dare,Sumayya zaune a dakin su mai dauke da katifa guda daya,wajan kwanan ta ita da lele. A kasa ta ke zaune,ga fitala gaban ta,assigment din su ta sa a gaba ta na kokarin gane komai,sai da ta fara gane tambayar wanda aka ce kamar haka"Analyse the concept of inflation and its negative effects on Economy, especially a developing country like Nigeria?"( Gudanar da tsargaggen bayani akan tashin farashi tare da illar sa akan arzikin kasa,musammam kasashe ma su tasowa kamar Nigeria?).

Burin Sumayya ta ga ta fahimce komai duk da de ba lalle ita ce za ta yi ba,amma ta na tsoran Prof Abdulrahman yanda yake titsiye student itama ya titsiyeta, sai dai kash,maganar Moh ta dame ta,ta yi wa Idi Allah ya isa ba adadi, in shi be gan ta ba hijab din ba ai ya jawo wani katan banza ya ganta a bagas!!har ya na ba da sharhi akai....gashi gaba daya wayar da lele ta ke ya ishe ta,da ma da mutum daya ne da sauki,ta kira wannan ta ce ya zo su je shoping,sai kuma ta ce wane zo mu je shan ice cream....sai kuma hirarra ki mara sa kai. tin ta na hakuri,har ta ka sa,ta  ce lele?lele ki na ji na fa....Lele ta dan aje wayar tare da fadin ayya ma na Adda waya  fa na ke. Sumayya ta ce na sani,ki aje wayar haka sai kuma da safe,gobe ma rana ce,ko kin manta za ki sch?ba WAEC Ku ke ba? Lele ta ma ta banza,ta cigaba da wayar ta,sai da aka dan jima ta kashe wayar ta,ta ce da Sumayya Adda wai me ya sa ki san takurawa mutum ne?

Cike da takaici Sumayya ta ce ke ba ki da lokacin kan ki ne sai na waya lele?kullum ace mutum waya,2,4,7 in ba kya amsa waya ki na dannawa,yaushe raban da ki daga Qur'ani ki karanta saboda Allah lele?ke ko tabara(suratul Mulk)da ake so dan adam ya ke karantawa duk dare kan ya kwanta dan samin rabauta a kwanciyar kabari ba ki yi Lale,baki san karanta Khafi da juma'a ba,ba azkar,ba zikiri,wayar ki ce ta zama rayuwar ki,shi ne abu na karshe da ki ke ajewa da dare,shi ne abu na fari da ki ke dauka idan an wayi gari,idan ki ka koma ga Allah haka me za ki ce ma sa ranar gobe kiyama?ya za ki wanye?

Lele ta ce kin ji fa yanda ki ke jero min wa'azi  sai ka ce wasu lefi na ke,har da fadar wani ya zan wanye ranar kiyama? masu manyan lefi ace mu su me?ai fa ranar Adda ina gefe cikin inuwa ina cin apple,kan a gama da ma su manyan lefe a zo kan mu.....assha!Sumayya ta jinjina kai, ji sani duk lokacin da kike wannan tunanin na cewa wai wani laifinsa yafi nawa to har abada baxaki taba daina abubuwan da kikeba, gaskiya lele duniya na rudar ki,Allah ya shirya ya sa ki fahimta,har yanzu da sauran ki!Lele ta murguda baki,ta juyawa Sumayya baya,ita kuwa Sumayya Qur'anin ta dauko dan karan ta suratul Mulk,ta na gamawa ta yi adduar bacci ta yi kwanciyar ta,ta bar Lele da danna waya...


HASKEN IDANIYA

part 16

Na Hauwa M. Jabo & Khadija Sidi.

Washagari ko da Prof Abdulrahman koda yashiga aji, aji ya cika fam Dan kowa yasan halinsa, ,sai ya zabi group C,ya ce su za su fara presentation, dan haka su fito gaban aji,haka su ka fito su 19 su ka jeru gaban aji,ko da prof Abdulrahman ya duba takardar ta su,su ishirin ne,ba mutum daya kenan,ya dube su cikin harshen turanci ya ce wanene shugaban ku?leader ya daga hannu,ya ce me ya sa ba ku cika ba?waye be zo ba?da saurin ta ta shigo,ta hawo stage din ta na fadin am here sir!!!!yanda aka ji yar muryar na ta ba zata,da kuma yanda ta ke cilla kafa cikin sauri,ga Hijib din ta kamar ya fi karfin ta ya sa yan ajin bushewa da dariya. Prof Abdulrahman ya bata rai tare da daka mu su tsawa,ya na tambayar what is funny!!ji ka ke tsit!!ya dubi Sumayya da ta jeru cikin yan uwanta,cikin harshen turanci ya ce ta matso ta fara,ita za ta yi presentation din......nan ma aka kara wani shewar,gani suke Sumayya ba za ta iya ba,yanda su ke ganin ta kullum sumi sumi cikin hijabi,magana ma ba ta iya ba bare ace za ta yi representing group. Prof Abdulrahman ya dada daka mu su tsawa,tare da gargadin idan su ka kara zai dau mataki me girma,ajin ya yi tsit Sumayya ta matsa gaba,ba kwarin gwiwa,group leader ya dan matsa kusa da lecturer tare da fadin dan Allah ko za ka zabi wani cikin mu,ba za ta iya ba...!hannu Prof Abdulrahman ya daga ma sa,sannan ya ce da Sumayya ita ake jira.

Ta fara da gaishe su,ta shiga gabatarwa(introduction)Muryar Sumayya,sautin muryar ta ya fara tashi,wato ba dalibai ba,hatta Prof Abdulrahman sai da ya matso ya dada kallan fuskar Sumayya,ba dan ita din ce  gaban sa ba,da ba zai taba yarda bakar fata ce ke magana ba,bare kuma ace Sumayya....kai harshen baturiya sak ke tashi!yanda turancin ke fita,da yanda ta ke ba wa kowace kalma hakkin ta....kun san turanci bakin fulbe ba magana,kuma abun tsoran shi ne Sumayya ba karantowa ta ke ba,Sumayya da ka ta ke zubu mu su baiwa daga Allah. Har ta takakkare da ba da tafarkin da za a iya bi dan rage yawan barazanar da ke tartare  da tashin farashi kan tattalin arzikin Nigeria.!

Nan fa aka shiga tafawa Sumayya,dan ba shakka ta yi bajinta,Prof Abdulrahman sai gyada kai kawai ya ke.
Aka bawa ma su tambaya dama,nan aka shiga watso mu su tambayoyi su na amsawa,har ana shirin sallamar su,sai wani da yayi suna wajan basira da gwazo ya ce ya na da tambaya zuwa ga wacce ta gabatar da assignment din,wato Sumayya,tuni gaban yan grp din ya fadi,duk da gwanintar da ta yi komai na da iya,bare kowa ya san halin wanda su ke kira kwaro indai wajan tambaya ne,akwai shi da kure.!


HASKEN IDANIYA

part 17

Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.

Prof Abdulrahman ya ce da Sumayya are you ready?ta ce yes Sir.....kwaro ya karanto tambayar sa kamar haka..."how is unemployment related to inflation in an economy....?"(Ta yaya rashin aikin yi ya ke da dangantaka da tashin farashi?)ya na bukatar karin haske daga gare ta a matsayin ta na wacce ta gabatar da jingar ta su. Aji yayi shiru dan tambayar ta yi sarkakkiya a level din su,saboda haka prof Abdulrahman ya gyara murya,tare da fadin amsoshin da suka amsa a baya yayi,bara ya amsa ma sa wannan.

Ga mamakin sa sai ji yayi Sumayya ta ce za ta amsa tunda ita din ya tambaya,cikin harshen turanci ta fara ba shi amsa da..."akwai amsoshi kwarara guda biyu da ke nuna dangantakar rashin aikin yi(Unemployment) da tashin farashi(Inflation)wanda su ka dogwara da yanayi biyu:dogon zango(long run) da gajeran zango(short run)"

Amsar fari shine zance da masan kan tattalin arziki(economists) suka samar cewa a gajeren zango(short run), tashin farashi(inflation) yana magantuwa idan rashin aikinyi(unemployment) ya karu. Ma'ana dai  idan aka sami tashin farashi ya yi yawa,toh a rage maaikata saboda aikin yi ke sa a sami yalwan kudi sosai a kasa har farashi ya tashi,idan aka rage samar da aikin yi,sai samin kudi ya ragu hakan kuma ya sa komai ya daidai ta. Sai dai wannan zance yana da dan rauni kasancewar ba akowanne lokaci hakan yake tabbata ba a zahirance.

Amsa ta biyu shine sakamakon sabon binceke na masanan tattalin arziki(Economist)su ka ce; a gajeren zangon(short run) ma biyun basu da wata kwakkwarar dangantaka. Hasalima sunyi imani da cewa shi rashin aikinyi a dogon zango(long run) dauwamamme ne ba chanji, bayan tattalin arziki ya gama samun saiti daga matsaloli bare har ya shafi tashin farashi.  Ma'ana dai shi rashin aiki yi fanni ne daban mai zaman kan sa,a dogon zango ana samin tashin farashi har kuma a yi maganin sa amma kuma rashin aiki yi nan daram ba tare da samar da shi ko rashin samar da shi ya girgiza ba.........aji ya yi tsit,Prof Abdulrahman gyada kai kawai ya ke dan kuwa dai Sumayya ta burge shi....Sumayya ta kara da 

A takaice, akan ce akwai dangantaka tsakaninsu sai dai bai cika tasiri ba sakamakon sauran abubuwa masu karfi da ka rage tashin farashi banda rashin aikin yi....shiru kamar wanda ruwa ya shanye haka ajin ya yi,Sumayya ta dubi sauran dalibai da tatabbatar da rainin da su ka ma ta,ta ce I.....ta dan dakata sannan ta dada cewa I COVER MY BODY WITH HIJAB BUT NEVER MY BRAIN.......

No comments:

Post a Comment