HASKEN IDANIYA
HASKEN IDANIYA.
part 1
Na khadija sidi & Hauwa M jabo.
Tafiya yake saman bike dinsa qirar Yamaha,irin wannan katan bike din mummulalle,wanda idan ka na kai sai a ganka kamar ka dan kurkushe yanda shape din bike din ya yi.
Ya saka wasu kaya na musamman irin wayanda bike rider suke sakawa. helmet din sa ka dai abar kalloce ba abinda ake gani a jikinsa komai ya rufe, ya saka wasu hand glove, duka dressing dinsa in black ya yi komai baqi haka bike din nasa ma baki ne......
Haka yahau express yana gudu kamar xai tashi sama, bashida damuwar komai a xuciyansa.
Yana kawowa daidai hotoro kawai sai ga wani saurayi ya bullo shima saman nashi bike din amma na farkon yafi girma da alamar tsada.!
Suna tafiya su biyu haka sukayi ta bullowa har sukakai su biyar. Amma na farin shi ne kan gaba,da alama shi ne jagoran su.
Yana gaba su kuma su hudun biye da shi a baya.. gudu suke kamar xasu tada birnin kano.!duk traffic jam din da ake yi a kano da sun shiga xa kuga kamar ana bude musu hanya,in dai ba mutum na san yin asara ba ne.
Sannan basa jiran traffic lyt, idan sun danno xakaga suna gudune basa tunanin mixai faru gabansu bare bayan su...
Ganin yanda mutane suke ba su hanya ya tabbatar da cewa su sannannu ne a gari. Basu xame ko inaba sai North-West, tun kafin su qarasa mu ka hango mai gadi ya wangale kofar da sauri ya ja gefe,shigewa ciki suka yi su ka bar mai gadi da qura.
Direct Eat & Go suka wuce suna xuwa sukayi parking guri daya kamar yanda suke na farkon shine gaba hudun suna bayan sa haka suka yi parking a gu daya.
Ganin su samari su ka dau ihu,ana Moh....Moh.... Moh.... Saurayin ne ya daga hannu cikin lalaci irin kamar daga hannun yana mishi wahala, hakan ya tabbatar mana da cewa sunan shine Moh... Wasu kuma naji suna fadin bike riders sun iso....
Lokaci daya suka cire helmet dinsu, ko wanne ya manna katan shade bisa idan sa, mamaki ya cika mu ganin fuskar wannan saurayin da suke kira da Moh.. Ya na da wani abu wait kyau,very handsome,down to earth,ya hadu. & yanada kwarjine da haiba.
Gefe guda su ka zauna domin kuwa nan ne wajan zaman su,drinks da su ka bukata aka ka mu su guda hudu kowannan su daya,amma ban da Moh.... Baisha ba,kawai dai ya zauna abun shi yana tauna chewing gum a hankali yana wani hargitsa fuska kamar yaga kashi. Amma hakan da yakeyi da fuska dada fito da kyawunsa yayi.! Kallo daya mu ka ma sa mu ka gane cewa Dan gatane, fuskarsa ma kawai xata nuna maka cewa Dan hutune.!ba tsoro su ka fidda wani dan takarda dauke da wani irin farin gari,suka zuba cikin drinks suka jijjiga,hankali kwance su ke kora shi cikin makoshin su.
Suna kare sha, su ka manna helmet dinsu suka hau bike gami da qara wuta...
Direct gun bord suka wuce suna zuwa naga duk mutanen gurin sun watse sai wata yarinya wacce iya haduwa ta hadu, da ganin tama irin tanajin kanta saboda kyau da koma komai na ta ya nuna kudi, ita ta ki kaucewa. Suna kawowa naga daya daga chikin su yasa qafa ya shuremata guiwa sai gata a qasa, ya bone kamar ba shine yayi hakanba. kuma ko ajikinsu, Suka qare dube dubensu suka wuce ko kallon ta basuyi ba,tana zaune a gurin ta danne qafa tana kuka...
Kai tsaye bike dinsu suka nufa suna shirin fita.
Koda suka hangi gate a kulle tun daga nesa suka fara horn amma har suka iso mai gadi bai bude gate ba...
Can muka hango mai gadi da gudu yaxo ya bude gate maimakon su fita sai sukayi parking suka sauka gaba dayan su suka nufo shi..Moh ne a gaba suna biye dashi su hudu a baya, Mai gadi yana ganin sun nufo shi ya saki wuta, ya gudu abinshi kada a lallasashi a banza. basuba koni jabo saida nayi dariya but naga khadija sidi batayi dariya ba.
Bike riders suka saka dariya gaba dayansu amma Moh.... Wani murmushi kawai yayi da gefen baki, Wanda ya masa kyau. suka hau bike dinsu suka wuce.
Maimakon suyi hanyar gida, sai kawai su ka yanki daji, Da Moh ne farko sai lokaci daya su ka tsaya ana daidaitawa, sai kuma qarar bike din ta sauya suka saka wata qara lokaci daya kawai sai naga an fara tsereeee........
HASKEN IDANIYA.
part 2
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
Sunyi gudu kamar na 100klm, duk bai wuce 30mnt ba,sannan sukayo kwana suka dawo chikin gari.
An kawo hanyar da suka hadu dazu dukansu,ammaba Wanda yayi kokarin wucewa gidan su,sai wucewa unguwa mai suna Sulemanu crescent su ka yi, saida sukaxo wani Babban gida su ka tsaya bakin gate shi kuma Moh... ya wuce ciki, yadan shiga sai ya daga helmet dinsa ya juyo da kanshi, amma hannayen sa suna riqe da bike din ya kalle su ya yi murmushi ya daga musu babban yatsa duk su ka yi horn lokaci guda suka wuce..
Yaqarasa cikin gidan sosai, yayi parking, agun da yayi parking akwai bike a gurin sunkai 9. Ko wanne kalanshi Daban.
Yana sauka ya cire helmet dinsa, yabi wani corridor, sai gashi a wani qaton parlour, da takalmin sa ya wuce yana xuwa a shagwabe ya xauna. Wata yarinya xata wuce suka hada ido tayi murmushin dole, tace Weldon broos.! daga mata kai kawai yayi ta wuce ta murguda baki da basuyi ido biyuba da baxata gaida shi ba.
Hajiya bushra taxo da fara'arta yadan saki fuska, ita ta fara gaidashi murmushi kawai ya mata, alamar ya amsa, bata damu ba sam,ta sa aka kawo masa abin tabawa amma ba wanda ya kalla bare yaci, TV kawai yake kallo yana kallon motoGP yayi wani doro yana kallon yanda ake tsere da bike..
Wanene Moh....???
********
Muhammad sunan shi,saurayi din kimanin shekara ishirin da takwas, sunan mahaifinsa habeeb, shi ne da na fari a gidan,sai qannen sa biyu mata Zainab da Fatima, Muhammad dan gata ne gaba da baya sabida idan kaga yanda yakeyi a gidan ba za ka yi tunanin ma ya na da qanne ba, xa ka dauka shi kadai ne a gidan shi ya sa yake yin yanda yake so.
Moh.... Kyakyawane ajin qarshe hez so silent baya magana sosai. Yafi yin sign akan magana, Yana yawan aiki da hannu, ko kai gurin sign yafi amfani da sing akan magana ko yayi murmushi ko ya daga hannu ko kada kai ya kan yi hakan sau dari kafin kaji ya yi magana daya. sannan akwai wani kallon da ya ke yiwa mutane ko ba kasan Moh ba xaka gane mi yake nufi da wannan kallon da yamaka..!
Silent killer kenan..A rashin magana yake duk abinda yaga dama, yana taba shaye shaye amma maturely yakeyi irin na 'ya'yan manya so ko iyayensa ba su san yana taba shaye shayen ba, kuma baya ganin darajar kowa. Ba abinda ya dameshi da kai kokai waye idan ka mishi xaisa a lallasa mishi kai.!
Mahaifinsa fataccen mai kudine Wanda xa'a iya lissafashi a jerin masu kudin kano. Amma asalin sa dan sokoto ne business da aiki ya mayar dashi kano. Alhaji habeeb Matarshi daya hajiya bushra. Auren saurayi da budurwa sukayi suna tare har yanxu, Alhaji habeeb yanada kudi har na fitar hankali.
Kuma yana sakarma yaranshi kudi son ransu, hakan ya baiwa Moh....damar wasa da kudin, yayi abinda yakeso, ya taka Wanda yaga damar takawa, yana ganin kowa a wulaqance bamai daraja saisu.!
ya fara raina mutane tun yana yaro, har yaxo kan dan shaye shaye abu dayane bayayi shine neman mata, mata da Maxa duk kallo daya yake musu.!
So ba ruwanshi da mace., Moh... yayi karatunsane a Nigeria inda ya ke karanta economic a jamiar North-west, yana ajin karshe, sabida sam bayason rayuwar waje, burin sa ya ganshi tare da dadin sa kuma a qasar sa.!
*******
Yana xaune a parlour sai ga dady ya shigo, da sauri ya miqe yaje gunsa yana murmushi, yace gud day dady. Sai Lokacin mu ka ji maganar shi, voice din sa irin lion voice dinnan ne, idan ya na magana xakiji voice dinsa da girma amma a hankali take shiga chikin kwakwalwar mai sauraro. Kuma a hankali ya ke magana a sanyaye. In short voice dinsa so sweet, zaka sami mutane masu sanyin murya masu girman murya amma kuma samun irin voice din Moh., gaskiya sai anyi bincike..!!
*****
Bayan dady ya amsa gaisuwar sai Moh ya wuce sashin sa kai tsaye.
Nan ma abin mamaki sabida ko mutum mai aure aka warewa wannan part din sai ya wala bare mutum daya, duk abinda yakeyi ba wanda zai san ya na yi duk a chikin gidan su.
Sai lokacin ya cire takalmin qafarsa ya cire kayan jikinsa, ya shiga wanka, irin maxan nanne masu wadataccen jiki, duk mace lafiyayya xatayi fatar ta samu miji mai kyan jiki irin na Moh...
HASKEN IDANIYA.
part 3
Na khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Kamar kullum Moh ya fito daga gida ya nufi hanyar skull, akan hanya ya hadu da gang din sa, suka wuce, yauma gate a bude yake tun kamin su qaraso mai gadi yasan time dinda suke shiga da fita. So wannan lokacin ya nayi xai wangale gate gudun bacin ran Moh..., shi kanshi mai gadi yana yana yin Moh ko ba komai ya kan yi ma sa yayyafin kudi in ya so... Kuma bike riders din suna burgeshi duk da dai Moh yafi burgeshi akan kowa.!
Suna xuwa direct hall suka wuce, koda sukaje an fara lecture & prof bello ne, Wanda idan ya shiga sai dai kowa ya tsaya bakin window, wani lokaci window dinma kora yakeyi, su Moh na xuwa duk su ka cire helmet din su amma ban da Moh, haka ya fada hall din, ga students sunkai 15 a waje jikin window an hanasu shigowa, amma su sun wuce direct, gang din nashi sun dan daga kai sukace sorry sir,shi kuwa Moh ko kallon lectr bai yi ba ya nemi waje ya xauna.
Sai lokacin ya cire helmet dinsa amma idanun sa toshe da bakin glass. Ya kalli prof bello yanda ya wani daure fuska, sai lokacin ya kula zuwansa ya janyo hayaniya a hall din, sauran students din da ke waje suma duk sun shigo ciki, haushi ya cika prof bello ya tattara kayansa yabar hall din, ko ajikin Moh... Dan shi kawai yana xuwa skull ne dan kare yawa bashida wani qoqari dama,ko an result ba ya dubawa sai lokacin registration ya yi ya ke sawa a duba ma sa ko an yi gangancin manna ma sa CO.
Yana fita students suka fara gunagunai.
Ya wani miqe tsaye ya juyo ya fuskance su kaji anyi tseeeet, kallon da ya musu kawai ya Isar da saqon da yakeson ya Isar, ya kama hanyar fita wata yarinya ta yi kuskuran jan tsaki,nan fa Moh ya tsaya,a tare su ka juyo su ka kalle ta,baki na rawa ta ce Allah ya ba ku hakuri!kai ya gyada,kafada tsaye ya juya cikin takama su ka fita. Bike riders kenan,duka sunan girma da aminci gare su,amma sun sauya irin na yaran zamani wanda da ka ji ka san akwai rudin rayuwa a tattare da su,Muhammad ya koma "Moh",Jamilu a kira sa "James",Shamsu ya na amsa "Shamo",Sunusi "Son" ya ke,Mika'il ya koma "Mike"
Haka suke in group suna tsula tsiyar su a skull dama cikin garin kano baki daya. ba wanda ya isa ya tabasu sabida iyayensu masu kudine sosai, musamman Moh...
*********
Kai tsaye babban joint na students suka xauna saman bike dinsu. Kowa na harkar gabanshi duk da cewa akwai ma su satar kallon su da ga mata har maza,
Suna dan hira sama sama amma Moh Yana sauraran su ne kawai bai cika magana ba hankalin sa na kan wayar sa.
Da yake joint din dalibaine ,maza da mata, daga chan gefe wata yarinyace kyakyawan gaske, tana xaune sanye da hijab din ta har kasa, tayi tagumi mafi yawancin guys din gurin kowa na kallon ta,dan gaskiya an aje kyau a wajen, idon James ne ya sauka kan ta, lokaci daya ya wani rude kai Ku kalli wasu kaya acan! Ya nuna musu ita da yatsa, kai,gaba daya su ka mai da hankalin su gare ta,amma ban da Moh,sam ya nuna be ma san a na yi ba,dan ko daga kai be yi ba!!! Shamo ya kara da kamar Ita tayi kanta dan kyau kai bara na taimaka na karo ma ta aji, ya miqe yadan gyara da niyar ya je ya ma ta magana dan zaune ta ke ita kadai,
kan ya karasa wani rubabben gajan guy,sam be hadu ba ya riga shi qarasawa gunta. abun mamaki yaga da fara'ar ta na kulashi, ba Shamo ba ba kuma su James ba,duk mazan wajan ba wanda be yi mamaki ba,ashe duk sun lura da ita,tsoran tinkarar ta su ka ji tsabar gwarjinin da ta mu su, ya beb kamar wannan za ta kula gaja kamar wannan,!!
haka sauran yan group dinsu suke mamaki, Shamo cikin isa ya ci gaba da nufo ta dan idan ya koma saboda wannan toh ya fado,toh fa kowa ya tsaya ya ga tashin bomb,dan Shamo be da sauki,kuma sun lura gun yarinya ya nufa.
Karasawa ya yi da isa irin nafi qarfin wannan gajan da kike magana dashi, amma ko daga kai batayi ta kalleshi ba,bare ta kulashi, duk da ta kalleshi ta gefen ido kuma ta gane shi. Kuma ta san su waye bike riders a makarantar,toh waye ma be san su ba?Sam ba sa gaban ta ne.
Cike da takaici ya ke duban ta,ya na shirin daukar mataki Ya ga ta tashi za ta bishi,ta daga kafa za ta taka...me zai faru sai ga beb tana cilla qafa.. gayu su ka sa ihuuuu da shewa,dan kuwa tafiyar ta ya bayyana mu su dalilin da ya sa Sumayya kula wannan gajar,toh in ba dai irin shi ba wa zai kula mai nakasa?haka ta su kwakwalar ta ba su.
Ihun yayi yawa, anan ne Moh ya daga kai yaga mi yake faruwa. Nan idanun sa suka dira bisa yarinyar,duk da yaji suna xancen wata yar buty ne , san kyan ta ya kai haka ba....Moh ya saki Ido da baki yana kallon halittar Allah, cilla qafar da ta ke yi ya bashi mamaki matuka,,wannan yarinya how comes ta ke haka?me ya sa mi kafar ta haka?
Mace ta farko da ya fara bi da kallo a rayuwar sa kenan har ta qure masa chan yaji wani yace sumy cillire..
Ya maimaita sunan a xuciyansa.
Sumyyyy.
Sumayyah....
Ku biyo yar gidan Muhammad jabo da khadija sidi Dan kuji waye sumee cilliree.!
Insha Allah posting ba kullum bane, xai xama sai jibi, idan anyi yau gobe baza'ayiba...!
No comments:
Post a Comment