Pages

21 Aug 2016

IDAN ZUCIYA TA GYARU Episode 3 to 4

IDAN ZUCIYA TA GYARU 
 
 By yasima Suleiman




IDAN ZUCIYA TA GYARU


 Episode 3 to 4

**************** 

Ta mike tana gyara yafa gyalanta domin tana sanye da doguwar riga mai hade da dankwali ne sannan ta ce, "Ka san Allah na gaji da jiranka, ko kana so ko baka so zanyi aure, ba zan biye maka ba Mustafa,tana kaiwa nan ta nufi kofa da sauri. Mamaki ya kamashi ganin lokaci guda tana neman yi masa tawaye, ganin ta nufi kofa ya bita da sauri da azamarsa, amman sai ta kara sauri kafin ya taddata tuni ta fice, haushi ya cika shi ya bita yana kiranta amman bata ko waigo ba balle ya sanya ran zata tsaya ma, yana kallon ta ta tare mota ta haye, haushi da takaici ya gama kashe shi ga wani masifaffen kishinta da yake ji musamman a yanzu don yana ganin idan ta yi aure ya rasata kenan, zuciyarsa tana gaya mishi hakan, don haka da zarar tayi zancan aure sai ya ji duk hankalinsa ya tashi, haka nan ya koma gida ransa a bace.Yana komawa ya tadda missed call har guda shida ya dauka da sauri yana dubawa, sai yanzu ma ya tuna da yau ne Zainab zata koma gidansa, da sauri ya kirawo layin Momin ya kama kare kansa da wai yana bandaki ne. Ta ce "Shi kenan daman maganar komawar su Zainab ne yau, don Alhaji ya dameni wai su koma tunda sun cika kwana arba'in kuma sun warke, ka san dai yau ne ko?" Ya ce, "Momi ina sane zan shigo da daddare mu wuce yanzu gyaran gidan ake yi." Da haka suka yi sallama ya fice da sauri ya nufi gidanshi ya sanya maigadi da direban suka gyara gidan tsaf ya amso kafet dinsu da zannuwan gado da aka wanko duk aka shimfida gidan ya yi kyau gwanin sha'awa kama amarya za'a kawo. Da daddare ya isa gidan gurin Babansa ya fara zuwa wanda yake daki yana kallon labarai daga BBC news, ya sami guri ya zauna ya fara gaida Baban nasa. Da sakin fuska ya amsa ya dauki remote yana rage magana sannan ya maida hankalinsa gaba daya kansa ya fara magana, "Yau ne Hajiyarku ta ce matarka zata koma ko?"

 Da sauri ya ce "Haka ne, yanzu ma su nazo dauka." "Yayi kyau hakan, sai dai zanja hankalinka da lallai ka kama kanka, domin yanzu ka fara ajiye iyali musamman da Allah ya fara baka mace kaga kenan duk abinda kake yiwa 'ya'yan wasu za'a yiwa taka, haihuwar mace babbar ishara ce a gareka idan ka kama kanka ka tuba kai da wanda ya halicceka, don na haife ba zai zama lallai na shiryar da kai ba, shiriya a gurin Allah take, sai dai ina yi maka addu'a kullum wacce bana tantamar ta amsu gurin Allah sai dai lokacin da zata fara aiki a kanka ne ban sana ba, Allah ya shiryaka, ka kula da iyalinka ka sauke nauyin da ke kanka na su, Allah ya shi maka albarka, ka tashi kada dare ya yi muku." Wani irin tashin hankali da nadama suka shige shi, wato duk abinda yake yi yana zaton Iyayensa basu sani ba ashe suna sane kuma abin yana damunsu, ya dinga jin kamar kasa ta tsage ya shige don kunya, haka nan yayi sallama da Baban nasa ya shige cikin gida. Can din ma nasiha Mominsa ta dinga yi masa mai tsoratarwa, tunda yake a duniya bai taba da na sani da nadamar abinda ya aikata kamar yau ba, sai yake ganin kamar kowa ma ya san shi din fasiki ne. . Haka nan suka wuce gida bai da wani kuzari, sanda suka isa Zainab ta kula da yanayinsa don haka ta hau gyara kanta domin ta faranta masa. Shi kam shigarta wanka wata dama ce da ya samu don haka ya dauki diyarsa ya zuba mata idanuwa, maganar Mahaifinsa ta dinga dawo masa, yanzu haka nan wani zai keta haddin diyar sa mai kyan nan? Zufa ta dinga karyo masa ji yake kamar ya boye ta cikin jikinsa kada wani ma ya ganta, bai san sanda ya sabule mata pampers ba ya dinga karanta mata addu'ar neman tsari daga zina yana tofawa a gabanta har yayi babu adadi sannan ya kwantar da ita. Ya tallafe goshinsa cike da tashin hankali, Zainab ta iso inda yake ta zauna bisa cinyarsa tana fadin, "Baban Zainabu yaya aka yi ne na ganka wani iri ko wani ne ya taba mini kai?" Ya lumshe ido gami da kwantar da kansa jikinta yana ajiyar zuciya ya ce, "Zainab ina tunanin irin rayuwar da Zainabu zata yi ne, na baki amanarta ki kula da tarbiyyarta matuka don Allah, ina neman afuwar Allah bisa laifukan da na aikata ina kuma rokonsa ya sanya hakkin ayyukana ya koma kaina kada ya shafi Zainabu albarkacin masoyin Allah.Ta dinga shafar kansa cike da soyayya tana fadin, "Ka kwantar da hankalinka, Shi Ubangiji ai yana son bawansa mai saurin tuba, kai dai ka cigaba da tuba Allah Gafururrahimu ne shi." Da haka ta samu ta kwantar masa da hankalinsa ya ji dan sanyi a ransa.

 *** *** *** *** ***

 Kwanakin Zainabu biyu tana jiran Mustafa amman ko wayarsa babu, don haka ta shiga tsahin hankali matuka ta kuma yaddarwa ranta Mustafa ya gama son ta, zaton da take yi na yafi son matarsa yanzu ya tabbata, ta yi kuka mara iyaka, duk ta wani rame ta jeme da ita, Sala kam ta gaji da mita ta zuba mata idanuwa. Ranar da ya cika kwanaki hudu Asma ta taddata da wani dare tana kwance bisa sallaya hannunta da carbi tana lazimi, ta rike baki cike da mamaki sannan ta ce, "Zainabu me nake gani? kinga yanda kika koma kuwa?" Zainabu ta tashi zaune idanuwanta masu ruwan zaiba sun rine sun koma jajir ta ce, "Asma ina cikin tashin hankali, Mustafa ya barni gashi ina son nayi aure na rasa wanda zai aure ni, duk cikin masu so na babu mai aure sai dai watsewa, rayuwa ta tana cikin garari yaya zan yi." Hawaye ya dinga silalowa daga idanuwanta. Asma ta tafa hannu tana salati ta ce, "Lallai kin gamu da babban aiki, domin dai Mustafa ya kama dahir, idan baki sani ba bari na sanar da ke, a Germany da nace miki zamu je da saurayina na hadu da shi da shegiyar yarinyar nan da kike tausayawa, kada ki ga irin soyayyar da suke zubawa, ga diyarsu da suka haifa ko ina yana rike da ita, wallahi da fari na yi zaton ba Mustafan da na sani bane, sai da na bishi na tabbatar shi ne domin dai hotel daya muka sauka,Zainabu ta waro idanu waje ta ce, "Kada ki gaya mini maganar banza, yaushe ne Mustafa ya saki jiki da yarinyar nan da har zata haihu, yanzu ma nice na yi masa bore shi ya sanya ya yi fushi, amman na san Mustafa ba zai ki sanar da ni ba, idan matarshi ta haihu zai sanar da ni komai bama 'yar haka da shi." Asma ta tabe baki tana fadin, "Lallai Zainabu, duk goguwarki da bariki har yanzu baki gama sanin halin maza ba, don na san ba zaki yadda ba ma shi ya sanya na taho miki da hotunan da na daukesu suna yawon honey moon da diyarsu mai kyau." Ta fito da hotunan sun kai guda talatin kowanne suna dariya ga diyarsu nan a kirjin Mustafa, daga gani babu tambaya kamar shi daya da diyarsa. Hankalinta idan ya kai dubu duk ya tashi, jikinta ya dinga rawa, ta ma gaza kukan, wato ita ce Mustafa ya maida 'yar iska, shi ne Yayi sanadiyyar lalacewar rayuwarta gaba daya amman ya manta da ita, wato aikin da yace ofis dinsu ya tura shi karya yake yi ya tafi yawon shakatawa da matarsa ne, kuma wai har yayi diya ya kasa gaya mata, to me yake nufi, ita ya maidata karuwa abar 

hutawarshi tunda ya san bata da mamora shi ya sanya ya hanata aure. Hawaye ya dinga jika hotunan da ke hannunta, bata da sauran kalmar da zata yi musu ga Asma ta yadda Mustafa bai sonta bai yi da ita abinda ya rage mata ta sami mai sonta ko da bata son sa ta aure shi ta huta da wannan gallafirin a duniya. Asma ta gyara zama gami da fito da kwalbar shandy tana tsotsa ta ce, "Kinga abinda ya dace kawai ki shareshi ki fita ki yi rayuwarki tunda dai kina da masu sonki, Allah ya sanya baki da mummunar kirar da zaki yi kaico."Maganganun Asma ba suyi tasiri a zuciyarta ba hasalima abinda zai gusar mata da hankali take nema ko ta daina ganin Mustafa da Zainab da diyarsu, ta warci shandy din dake hannun Asma ta kafa kai ta kama sha kamar zata cinye kwalbar, sai da ta shanye ta duka sannan ta dire kwalbar, ta hau laluben tabarta ta shaidan yau kam babu ruwanta da wani turaren wuta kowa ma ya san tana sha, ta kunna ta ta dinga zuka tana fesarwa, sai da taji kanta yana wani juyawa sannan ta fada gadonta ta lumshe idanuwanta, Asma ta gaji da surutunta tayi mata sallama ta wuce gidanta. Kwanaki uku tana cikin daki babu wanka balle wanki, sallah kawai ke fitar da ita, duk ta zama wata iri, idan dare yayi kuma tayi ta shan tabar ta da shandy, Babanta kam ya gane halin da take ciki amman yana tsoron fadi kada Sala ta tsireshi shi don idan suna jin warin tabar sai ta fara Allah ya isa tana fadin, "Shegu su rasa inda zasu sha tabar su sai kofar gidanmu." Shi dai shiru kawai yake yi don baya son abinda zata yi masa tijara ana zaune lafiya. Sadiku da Zaid suna zaune a inda suka saba suna hira Zaid ya ce, "Sadiku baka ga ya dace na yiwa su Shahid uwa ba? Ina so nayi aure ko domin na cigaba da tarbiyyantar da 'ya'yana a gabana, bawai ina rena tarbiyyar su Malam bane sai dai suna shagwaba yaran da yawa domin basu da Mahaifya, ni kuwa ina ganin kamar hakan zai sanya su lalace ne kawai." Sadiku ya ce, "Haka ne, ai watanni biyu sunyi da mutuwar Mahaifiyarsu don haka babu laifi don kayi aure, sai dai ina ganin ai baka tsaida wacce zaka aura din ba, ko daman kana da wata ne ban sani ba." Ya karasa maganar da Zolaya. Zaid ya yi murmushi yana shafa gemunsa ya ce, "E to kusan dai bani da budurwa, sai dai a kwanakin nan Allah ya jarabceni da son wata yarinya, duk da nasan ba lallai kayi na'am da zancen ba, itama na san ba zata so auran Ustaz irina ba don tafi son 'yan gayun zamani." Sadiku ya yi dariya ya ce, "Ka ji ka, wallahi halayyarka da kirkinka babu macen da zaka dosa ta kika, ga ilmi sannan ga kyau, kaima kuma din ai kana taba gayun tunda dai yanzu gashi cot ce a jikinka, amman ka sanya wata hula, suka yi dariya har da tafawa. Sannan Zaid ya ce, "Ba wata bace illa kanwarka Zainab, ita ce nake so a raina, kwana biyu da bana ganin gilmawarta sai naji duk na damu matuka.....". "Kai Zaid amma baka iya zabe ba, ina ce cewa kayi kana son ka cigaba da baiwa yaranka tarbiyya, to Zainabu ina taga tarbiyyar da har zata baiwa wani? wani abu da baka sani ba na sanar da kai yau Zainabu.....

 Kada ka fada mini komai na san komai na Zainabu, nasan tayi bariki nasan tana shaye-shaye, sannan na san yanda take da Mustafa, duk wadannan ba zasu hanani auran ta ba, domin ina sonta a duk yanda take kuma ina fatan Allah ya shiryeta a hannuna, ka kuma lura tun daga ganin Aisha da tayi jikinta yayi sanyi da komai, balle da ta rasu Zainabu tayi nadama matuka, zaka yi mamaki idan na auri Zainab yanda zata koma domin irinsu suna yin komai da karfin su ne, idan suna son suyi lalata babu mai hanasu haka nan idan suna so suyi aikin kwarai babu mai hanasu, shin ko kasan ina saka idon tun daga ranar da Aisha ta mutu bata kuma fita da wani saurayi ba? Sai rannan da Mustafa ya dinga binta da kyar ta shiga motar tashi ma, ina zaune bata cika awa guda ba ta dawo gida ranta bace, tun daga wannan ranar kuma bata kuma fita ba, duk wani hali nata na sani, kai dai ka tayani da addu'a kawai. Jikin Sadiku yayi sanyi, ya yadda lallai Zaid yana son Zainabu, ai shi zaifi kowa murna idan akace Zainabu ta shiryu amman yana da sauran abin cewa, ya gyara zama ya ce "Kana ganin kamar yanzu Zainabu ba auran kisan wuta zata yi ba domin tana son Mustafa da yawa fa." Zaid yayi murmushi ya ce, "Na sani kuma nima ina zaton hakan, sai dai ai ba kowanne namiji ne yake kashe wutar ba, wani rurata yake yi, to nima zan rurata ne har ta kone kudirin dake zuciyarta da ikon Allah, ban fara sanar da kowa maganar Zainabu ba sai da nayi istihara na ji sonta na kuma karuwa a raina, ka dai taya mu da addu'a." Sadiku ya ce, "Nagode Zaid Allah ya shige mana gaba ya sanya kai ne silar shiryuwar Zainabu, domin na damu da halin da take ciki." Sun yi hira sosai akan Zainabu ya ce zai kai mata kokon bararsa da kansa tunda dai ya isa namijin da kowacce mace zata so.


Yau kwanaki goma sha daya kenan rabonta da Mustafa, iyakacin tunaninta ya gama gaya mata Mustafa ya daina sonta, ya hadu da wacce yake so mai haihuwa don haka zata cigaba da rayuwarta zata koma da aikinta har Allah ya kawo mata mai sonta da aure tsakani da Allah, don haka yau kam tayi wankanta tayi kwalliya sai dai idanuwan nan nata tamkar rana suke babu kwalli sun jeme sun kode. Tana zaune a tsakar gidan su tana duba wani littafi yaro ya shigo ya ce ana sallama da ita, kamar ta shareshi mai sallamar amman sai tace yaje ya tambayo waye. Yaro ya dawo ya ce mata "Wai DPM ne." Babu musu ta hau shiri domin dai shine wanda take tunanin taje ta samu akan maganar komawarta aiki daman, don haka ta shirya ta fice, Sala kam dadi ya cikata matuka har da lekenta don ta tabbatar ta fita din. Yana cikin mota a zaune ta jingina da motar tana wani yauki da yangarta, shi kam dadi ya cika shi don baiyi zaton zata fito haka da sauri ba. Ya dinga washe baki yana fadin, "Zainabu tauraruwar mata ashe zaki fito, wallahi gwadawa kawai nayi don sonki ya dame ni matuka gaya, naji labarin daman auranki ya mutu." Ta yamutsa fuska domin dai don dole take tsaye da shi, ji take yi kamar ta shakeshi ta huta. Shi kam dadi ne ya cika shi ya kuma gyara zama yace, "Tauraruwar mata ki shigo mana kin yi tsaye a waje kamar wata gidahuma, ko kuma mulkin ne ya motsa?" "Kaga malam nan ma ya isa daka samu na fito ma, ni tsiyata da kai kenan shegen surutu kamar aku kuturu." Ya kyalkyale da dariya domin dai yau kam a cikin farin ciki yake na Zainabu ta saurareshi, sai kace wani soko ko wawa ya ce "Tuba nake, wai don kada ki gaji ne dama.....


" Dannowar motar Mustafa ta sanya gabanta faduwa ta kurawa motar ido babu makawa shine din, ya dallare su da hasken fitilarsa, DPM ya hasala sosai ya hau masifa yana fadin "Kai kaga wani dan iska yazo yana kashewa mutane idanuwa ko ubanwa zai gwadawa mota." Ita kam da ta tabbatar shine sai taji ta gwammace ta shiga motar DPM din da dai ta tsaya ta kulashi, domin tana jin har abada ba zata kuma kulashi da sunan soyayya ba, da sauri ta zagaya ta bude motar ta shiga, abinda ya sanya DPM din jinshi kamar ya shide don murna, lallai yau da sa'a ya fito yana ganin zai sami abinda yake so. Shi kuwa Mustafa daga can cikin motarshi ya gama ganin abinda ke faruwa, don daman ya tabbatar Zainabu ce ya sanyashi hasketa da fitila, ya kuma gane wanda suke tare, yana jin duk cikin manemanta babu wanda yafi tsana kamarsa domin tsohon dan iska ne mutumin gashi shegen kauye bakinsa ya dafe da taba yaji zuciyarsa tana tiriri.Yau kwanaki goma sha hudu kenan yana fama da masifar sonta a zuciyarsa yayi kokarin ya danne ya shareta amman ya gaza, duk wanda yake tare da shi ya san yana cikin damuwa don haka ya yanke shawarar ta auri yaronsa Kamu mai musu wankin mota, duk da yana da mata da 'ya'ya zai biya komai na auran har inda zasu zauna idan yaso bayan sati guda sai ya saketa, shine kadai yake ganin mafita domin ya san Kamu da shegen son kudi idan yaga makudan kudi zai aikata duk abinda ya ce din. Amman abin bakin ciki sai gashi ya taddata da shegen kauyan nan, ya riga kuma ya san halinsa sarai tunda ya ganshi da ita yasan ya bata masa bajat dinsa, shin tun yaushe nema ta koma mu'amala da wadannan 'yan iskan? Sanda ta bude motar ta shiga kuma ji yayi kamar ya hadiyi zuciya ya mutu don shegen kishi da bakin ciki. Shi kam DPM ya dage sai hira yake mata amman sam bata fahimtar abinda yake cewa gaba daya hankalinta yana gurin Mustafa, tana son yau tayi masa wulakanci da dai wanda yayi mata, can ta ce da DPM din ya ja motar su tafi. Jikinsa har rawa yake yi sanda yake tada motar sai wata sha-sha-shar dariya yake yana fadin, "Zainabu tauraruwar mata." Sanda suka hau bisa kwalta Mustafa ya rufa musu baya don yaga inda zasu je, shima Zaid dake tsaye kofar gidansu kan motarsa yana kallon duk abinda ke faruwa ya rufa musu baya da gudun shi. Sunyi nisa sosai bisa titi ta hango har lokacin yana biye da su har sun fita wajen gari kuma, da kansa DPM din ya lura yana binsu. Da fargaba ya ce, "Zainabu naga waccan motar kama mu take bi, kuma daman naga yana haskemu tun a can kofar gidanku ko kin sanshi? don kinsan zamanin babu gaskiya kada dai barayi ne ke biye da mu sai sunga munyi nisa da gari su far mana." Ta kalleshi a kule a ranta tana fadin, "Banza matsoraci sai iskanci, amman tsoro kamar farar kura." A fili kuwa cewa tayi, "Sami guri kayi parking mu gani idan mu yake bi din." Da saurinsa yayi parking gefen hanya, ta bude bangaran da take ta zagayo ta jingina da motar tana jiran isowarsa, ya take wani irin birki sannan ya kashe motar ya fito a hasale, domin dai ya ganota tsaye jikin motar ya kuma san tabbas ta gane shine ke binsu. Ya iso gabanta yana haki kamar wani tsohon bijimin sa, ya kalleta da jan idonsa kamar zai cinyeta danya sannan ya fara magana a hasale "Kina zaton zaki boyewa ganina ne, wai shin yaushe kika koma wannan mummunar huldar ka kika nuna mini kin daina, wato daman munafunta ta kike yi ko?"Yanda yake feso maganar a hasale da bacin rai ya kuma kona mata rai don haka da zafin rai itama ta fara magana, "Sannu shugaban mayaudaran duniya macuci azzalumi, shin kaine ka halicceni ko kuma auran ka ne a kaina da zaka hanani watayawa, to ka sani Mustafa dubunka ta cika a gurina, na gane ba don Allah kake sona ba sai don mu watse, domin na gano tafiyar da kace kayi ashe karya ne ka tafi yawon shakatawa da matarka da diyarka ne, don haka ka shareni sai da ka dawo kuma kake neman ka hanani aure domin ka mai da dadi ranka, to ka sani nasan komai, yaudarar ka a gurina tazo karshe Mustafa." Ya ji wani iri, yaya aka yi ta gano abinda yake boye mata? Allah ya sani ba wai yana boye mata don wani abu bane sai don gudun bacin ranta gashi kuma taji, sai yanzu yayi da na sanin kin sanar da ita gaskiya da yayi, sai kuma ya koma kokarin kare kansa. Ya kwantar da murya yana fadin, "Haba Zainabu yanzu har kina zaton.....kaga Malam bana bukatar jin wata kalma daga bakinka ka bace mini da gani, don babu sauran wani abu a tsakani na da kai, ka ga wannan" Ta nuna DPM din "To shine wanda zan aura yanzu, kada kuma kayi tunanin zanyi auran kisan wuta ne, a'a har abada na rabu da kai bana sonka bana kaunarka, na tsaneka kai da halinka, ina addu'ar Allah ya saka mini bisa cutata da kayi a rayuwata.....

 Ke Zainabu ki rufe mini baki, ni kike zagi akan wannan tsohon dan iskan? To ko a gwaji aka gwada mu kinsan na fishi quality ta ko ina, don haka ina miki addu'ar kada ki auri irinsa har abada." Ta yi dariya mai ciwo tana fadin, "Mustafa kenan, kai yanzu har kana ganin akwai wanda kafi kyan zuciya, to naji na gani ko wanene shi nake so shi zan aura kai din baka isa ka kuma taba Zainabu ba har abada,Ya dauketa da wani wawan mari da ya gigita ta, ta rike kuncinta cike da tsananin bakin ciki, shi kam ko dar bai ji ba sai ma haushinta da yake ji bisa abinda take gaya masa, domin dai ya san DPM mutum ne azzalumi ga iyalansa, sam baya kyautata musu, ya yi karatu da ya kai shi matsayin da yake amman har yanzu iyalansa suna kauye kuma basu daina komai na wahalar rayuwa ba kamar surfe da sissika da sauransu, domin kudi yake badawa ayi noma a jibge musu,Shi kuwa ya gina katon gida a cikin binni wanda yake holewarsa da mata, baya komawa gidansa sai ranar asabar da safe ya dawo lahadi da yamma da sunan ya tafi aiki ne, don haka yake ganin ta hadashi da mutumin da bai isa komai a gurinsa ba. DPM din ne ya fito a hasale daga motar tashi ya daga hannu zai wankawa Mustafa mari wai don ya marar masa Zainabunsa, sai dai hannunsa bai isa ga fuskarsa ba ya rike hannun nasa domin karfin ba daya bane, Mustafa matashi ne da yake ji da kuruciya da karfi shi kuwa girman ya fara kamashi, Mustafan yayi wurgi da hannunsa gefe gami da nunashi da yatsa yana masa kashedi. "Kai ka kiyaye ni idan ba haka ba wallahi sai na babballaka a gurin na, kada kuma kaga Zainabu na fada mini wannan maganganun har abada ni take so, wallahi takalmi na ya fika daraja a gurinta ta kuma gwada ka gani." Yana gama fadin haka ya kalli Zainabu da bacin rai ya ce, "Na kyaleki ba zan kuma nemanki ba duk ranar da kika gano gaskiya zaki nemeni da kanki, sai dai ki sani har abada kece kawai abar sona kuma zabina." Yana fadin haka ya juya ya shige motarsa ya tada kura ya bar gurin. Zainabu dake dafe da kunci ta bishi ta tsaki sannan ta koma cikin motar ta zauna ranta yana suya da kuma juya kalaman Mustafa. DPM ya zagaya ya zauna yana huci yana fadin, "Shege dan iska mara kunyar karya haka ake so dole? Yarinya tace bata sonka amman ka nace mata, zan sanya ayi maganinsa kinji tauraruwar mata kada ki damu kinji ko?" Ita kam bata fahimtar abinda yake cewa sam har ya fada motar ya fara tafiya, tunanin da take yi mai zurfi shin da gaske Mustafa yana da gaskiya ko kuma wata salan yaudara ce zai kuma yi mata, can kamar wacce aka tsikara ta farga da gudun da DPM yake yi, domin dai shi gani yake yi yau ta fadi gasassa zai yi yanda yake so. Ta dubeshi da takaici ta ce, "Malam ka maidani gida ina zaka kai ni ne?"ya dubeta sanda ya marairaice don ya ga samu yana neman kuma ya ga rashi haka kawai ya ce, "Haba sarauniyar mata kada muyi haka da ke mana, wallahi zan samar miki duk irin aikin da kike so, sannan ki fadi duk abinda kike so na baki wallahi zan baki,bana so Malam ka maidani gida na ce." Ta fadi da tsawa, jikinta sai tsima yake yi. Ganin yanda ta birkice masa don kada ya jawa kansa taki yadda da shi har abada ya sanya yayi niyyar mai da ta gida, a ransa yana tsinewa Mustafa don dai shine dai ya bata masa bajat dinsa. Yana kokarin juya motar bisa wani (U-turn) sam bai kula da katuwar motar da take shirin shigowa hannun da yake kai ba, Zainabu ce ta farga amman ina babu sauran wata dabara domin dai motar shi ta doki katuwar motar dake kokarin cin birki amman ta gaza, ji take gararaf-gararaf, motar tashi ta yi sama sosai murfin da Zainabu ke zaune ya bude akayi cilli da ita can gefe motar ta dawo ta daki tsakiyar titi sai ta kama wuta, kafin mutane su kawo dauki tuni ta kusa konewa amman dai anyi nasarar kashe wutar. Zaid dake biye da su ya taka birki gami da dafe kai don duk akan idonsa komai ya faru, ya bude motar ya fito yana kiran sunan Allah, har da shi aka baiwa motar taimakon gaggawa domin dai yana zaton Zainabu tana ciki. Sai da wutar ta mutu sannan aka fara kokarin fito da wadanda ke motar, DPM ne kadai a ciki duk ya kone jikinsa ya sabule amman dai babu rai a tattare da shi, (Lallai mutum ba a bakin komai yake ba, gwarama ka bi Allah ko ka cika da imani, shi dai ku dubi irin yanda ya cika, sai dai shi Allah Gafururrahimu ne inji Fauza) . Nan fa Zaid ya dage da akwai wata a motar don tare ya gansu, amman iyakacin bincike ba'a gano Zainabu ba, sai can aka ganota yashe a gefen titi jini yana zubowa ta hanci da kunnenta da alamun ita dinma babu rai a tattare da ita, ya dafe kai yana hawaye, yanzu shi kenan ya rasa Zainabu sanya yake matukar sonta da kaunarta? gashi har ta koma ga Allah bata san yana sonta ba, mai ya sanya yayi kwaron baki bai sanar da ita yana sonta ba? Ya tallafota a jikinsa domin dai bai yadda ta mutu din ba gwara ya je asibiti a duba masa ita. Mutane suka taimaka masa aka sanyata a mota shi kuma DPM aka fara neman layin 'yan sanda don su zo su tafi dashi, shi kenan rayuwar kowa zai koma ga Allah komai dadewa ya amsa irin abinda ya aikata a duniya (duba ranar mutuwa a mujallar fim) Allah dai ya sanya mu cika da kyau da imani Amin. A (A&E) na asibitin Malam Aminu Kano aka amshi Zainabu, Nurses da suka fara ganinta kafin likita ya karaso suka sanya abun gwada numfashi da taba jijiyar hannunta da yatsu biyu babu alamun numfashi don haka suka kalli Zaid suka ce sai dai kayi hakuri malam amman bata da rai. Ya kuma dafe kai yana fadin, "Hasbunallahi wa ni'imal wakil, Ni'imal maula wa ni'iman nasir, la haula wala kuwwata illa billah, ya hayyu ya qayyumu.

 Zainabu mai ya sanya kika min haka? Sanda na rasa Aisha nake ganin zaki maye mini gurbinta kema sai ki bita." Ya kifa kansa bisa cikinta yana kuka, yasan ya so Aisha har sun zauna zama mai kyau da kyautatawa juna amman son da yakewa Zainabu a wannan dan tsukun sai yake ganin kamar yafi na Aishan ma, ko don ita ya zauna da ita, ita kuwa ko kalmar so bai furta mata ba ta mutu, kai wannan wace irin rayuwa ce mai wahalarwa, lallai yana ganin shima din binsu zai yi, kamar ba namiji kuma malami ba hawaye yake zubarwa sosai.can yaji anyi wata irin doguwar ajiyar zuciya, ya daga kansa da sauri sai yaga Zainabu ce tayi, sai kuma numfashinta ya dawo sai dai ba daidai yake bugawa ba, ya daga hannu yana fadin "Masha Allah Alhamdulillah." Nurses din suka farga da abinda ke faruwa suka kirawo babban likita da sauri, yana ganin halin da take ciki aka shiga da ita daki na musamman ya manna mata iskar (oxygen cylinder) numfashin nata ya fara daidaituwa sannan ya shiga aikinsa a kanta. Sai wajen karfe hudu na asuba aka samu numfashinta ya dawo daidai kamar da, sai a sannan Zaid ya dan samu nutsuwa kuma dai a sannan yayi waya ya sanar da Malam da Sadiku. Karfe bakwai na safe duk 'yan uwa da iyaye sun hallara gaba daya, kowa tambayar abinda ya faru yake yi, bai gaya musu gaskiyar magana ba don kada ya rage mata kima a gurinsu ko kuma suyi zargin wani abu, don haka yace ta tsallako titi da siyayya a hannunta mota ta bigeta shi kuma ya zo wucewa yaga an zagayeta da ya leka sai yaga ashe itace shine aka sanar da shi abinda ya faru, Sadiku kam bai yadda da maganar ba amman ya bar abin a cikin ransa. Sala kam da ta iso ihu ta fara da turmami a kasa domin Allah ya sani duk cikin 'ya'yanta babu wanda take so kamar Zainabu, itace diyar so a gurinta don haka taji abin matuka, sai da jami'an tsaro na asibitin suka ce tayi shiru amman har lokacin tana sheshshekar kuka sai Baba Abbakar ke lallashinta da kwantar mata da hankali. Kwanaki shida Zainabu tayi bata san inda kanta yake ba sannan ta farfado, sai dai bata farka cikin hankalinta ba, abin ya tsorata likitocin don haka suka hau bincike a kanta da kwanfutoci sosai. Bayan sun gano abinda ke damunta suka kirawo Zaid ofis dinsu domin dai shine tsaye akan komai, Dr. Bukar ne ya gyara glass din sa sannan ya ce "Malam Zaid kasan kuwa matarka tana shaye-shaye?" (domin dai sunyi zaton matarsa ce). 

Ya yi dan jim sannan ya nuna bai sani ba don bai son suyi masa wata fassarar har ma yaso ya karyata abinda suka ce din, don ma daga shi sai Sadiku sai likitan ne a dakin. Likitan ya ce, "Ka yi hakuri Malam Zaid lallai matarka tana shaye-shaye don haka yanzu ta warke sai dai ta sami tabin kwakwalwa sakamakon shaye-shaye da suka yiwa kwakwalwar illa matuka, don haka yanzu zamu mai da case dinta bangaran masu tabin hankali (Psychiatric hospital) sai kuje ku kai wannan takardar."Ya mika musu takaddar. Jikinsu yayi sanyi matuka nan suka fice babu kuzari a jikinsu suka nufi bangaran da aka turasu, suna tafe kowa da abinda ya ke sakawa a ransa. Zaid ya dubi Sadiku ya ce, "Ina son ka rufewa Zainabu asiri har mu ga ta sami lafiya bana son ka sanar da wani gaskiyar maganar, zamu bar abin a cewar buguwa kawai tayi a kanta ina fatan ka fahimta?" Sadiku yayi murmushi mai ciwo sannan ya ce, "Zaid sau nawa kana rufawa Zainabu asiri, na sani duk wanda ya rufewa wani asiri shima Allah zai rufa masa, don haka koda baka sanar dani ba zan rufa mata asiri domin dai 'yar uwata ce, sai dai ina bakin ciki a raina domin banyi zaton lamarin nata ya kai nan ba, Ubangiji ya shirya ta." Ya sanya hannu yana goge kwallar da ke silalo masa. Zaid ya ce "Allah ya shiryi Zainabu don koda ace mutuwa ta yi Allah yaga zuciyarta." Ya kwashe duk abinda ya faru ya sanarwa da Sadiku wanda ya sani sannan ya dora da cewar, "Bana shakkar cewa ta yi ya maidata gida, ka santa da tsiwa, don yanda ya juya kan motar ya bani mamaki, don haka ina kyautata zaton Allah ya shiryata tun kafin ta sami wannan lalurar sai dai mu yi mata addu'ar samun sauki ya sanya kuma sanadiyyar kankarewar zunubanta ne Amin. 


No comments:

Post a Comment