Pages

21 Aug 2016

.IDAN ZUCIYA TA GYARU, DUKKAN JIKI YA GYARU Episode 5 to 6

IDAN ZUCIYA TA GYARU 
 
 By yasima Suleiman




IDAN ZUCIYA TA GYARU


 Episode 5 to 6

**************** 

Yanayin ciwon Zainabu yana firgita 'yan uwanta, Sala kam tayi burari da ihu ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido, domin dai bata magana Zainabu sai dai ta zauna kurum ta yi shiru tana kalle- kalle, can kuma idan abin ya motsa sai ta kama tirje-tirje da fisge-fisge, sai da ta yi kusan kwanaki shida a haka sannan aka samu ta daina wannan tirje-tirjen, sai dai ta zauna shiru tana kalle- kallenta kawai babu um babu um-um. Ganin haka ya sanya aka basu sallama, sannan aka ce za'a dinga zuwa ana karbar mata magani idan anyi dace zata warke, haka nan aka maidata gida bata san komai da kowa ba. Zainabu 'yar gayu ma'abociyar son kamshi da tsafta sai gata babu wanka balle wanki, sai Sala ta kama hannunta ta kaita bandaki wani lokacinma sai ta yi mata da kanta, ana mata tana kuka, abinci ma sai an kai mata gabanta idan zata kwana ta yini ba zata iya cewa a bata abinci ba sai dai idan tana jin yunwa ta kwanta tayi ta birgima tana kuka. Zaid ya shiga tashin hankali matuka duk ya kode ya rame har Malam ya fara dagoshi, amman Iyayansa mata suna zaton ko mutuwar matarsa ke dukansa, kullum yana gidansu Zainabu, zai sanya ta a gaba yana tambayarta mai kike so, mai za'a kawo miki, a baki wani abin? Ita kam sai dai tayi ta kallonsa bata Uhm balle Um-um, idan ya bata abu wani lokaci ta ci wani lokaci kuma ta watsa masa a jikinsa. Tun Sala tana gaya masa kada ta bata shi har ta kyaleshi, domin ta lura kamar Zaid sonta yake yi taji dadi kuwa, yaron da take hantara a da shi da Sadiku yanzu kam son shi take tunda dai bai gudun diyarta duk da lalurar da take fama, Jamila kanwarta ma da suke daki guda cewa ta yi gaskiya ba zata iya zama da mahaukaciya ba haka kawai cikin dare ta makureta babu mai kwatarta.

 Da yake Sala tana ji da ita yanzu saboda ita ce ke samo mata kudi ya sanya ta hau rarrashinta amman ta ce gaskiya ba zata iya zama da ita ba, don haka ta koma dakin Sala da zama, ita dai Zainabu idan dare ya yi sai dai a kulle ta a dakinta don kada ta fice idan suna daki, kafin gari ya waye duk ta bata daki gwanin tausayi, da yake mai tsafta ce idan ta yi bayan gida ko fitsari sai ta wurgar da zanin ta koma gefe ta rakube bata son najasar wai ta taba ta. Watanni suka shude Zainabu na cikin tabin hankali, Malam kam yana taimako da ruwan addu'a ko da yaushe shine ma ke hanata wannan fizge-fizgen, Zaid kuma yana iyakacin kokarinsa gurin karbo mata magani domin dai duk shi ya dauki dawainiyar maganin nata, domin Sadiku ya so ya amsa amman yace shima ai kanwarsa ce don haka ya kyale masa, sai dai shi Sadikun ke kawo musu kayan masarufi da duk wani abu da za'a bukata, mutanen unguwa kuwa sai Allah ya kara suke yi don ma dai ana tsoron Sala sai dai ayi gulmar a bayan idonta. INA LABARIN MUSTAFA Yana cikin kunci matuka a rayuwarsa domin ya dukufa da addu'a da neman gafarar Allah shi ya sanya ba'a gane halin da yake ciki, sannan Zainab na iyakacin yinta taga ta kwantar masa da hankali, dake idan ya dauki diyarsa sai ya dinga ganinta kamar Zainabun gaskiya, matuka yana son Zainabu sai dai yayi alkawarin ba zai nemeta ba. Da wata daya, biyu, uku suka shude Zainabu bata nemeshi ba abin ya daure masa kai matuka, shin duniya kuwa da gaskiya Zainabu zata kishi, lallai ya san yayi mata laifi amman ai hukuncin shi bai kai haka ba a gurinta, zuwa yanzu ya dace ace ta hakura ta yafe masa don yayi Imani da Allah Zainabu ba zata auri mutumin nan da ya gansu tare ba ko da kuwa maza sun kare, ya san ranar nan ta gaya masa maganganun nan ne domin ta rama abinda yayi mata, ya dace ace ta hakura haka nan, ya gaza jure rashin Zainabu domin dai yana jin kamar ya rasa wani abu ne a cikin jikinsa don haka kullum sai yaje bakin layinsu ya tsaida motarsa ko Allah zai sanya ya ganta ta gilma amman kuma bai ganinta ko mai kama da ita bai gani, iyakacin zuwansa a wata biyu bai ga Zainabu ba. Yau dai Allah ya sanyashi ya ci karo da kaninta abokinsa Ila ya zuge glass dinsa baki yana kwalawa yaron kira, da gudu ya isa inda yake don ya ganeshi, da yake yanzu yayi dan hankali ya sanya ya gaishe shi. Mustafa ya ce, "Isma'il yayar ka ne kwana biyu bana ganinta sam?" Yaron ya dubeshi da mamaki ya ce, 

"Daman baka san Anti Abu bata da lafiya ba? Ai ta jima bata da lafiya bata zuwa ko ina ma." Ya waro ido waje cike da tsahin hankali ya ce, "Da gaske kake yi, me ke damunta ne?" Ila ya ce, "Ai hatsari tayi tun kwanaki ta sami tabin hankali yanzu haka ko magana bata yi tana gida a zaune." Mustafa ya tsorata matuka da abinda ya ji sai yake ganin kamar yaron ba daidai ya gaya masa ba, amman dai bai musa ba ya ce "Shigo mu karasa gidan naku na ga jikin nata." Suna tafe yana tunanin abinda ya sami Zainabunsa, lallai yasan banda rashin lafiya babu abinda zai hana Zainabu ta neme shi, domin dai yasan tana son shi matuka laifinsa bai ci ta guje shi haka ba. Sanda suka karasa Ila ya shiga gidan yayi masa iso, Sala kam cewa tayi ya shigo ai duk daya ne, ya shiga da sallama ya tadda Sala a zaune a tsakar gida ya gaisheta sannan ya shiga dakin Zainabu din. Yana shiga ta dago kai tana kallonsa, ta zuba masa idanuwanta masu kama da zaiba wanda suka kara kodewa saboda rashin gyarawa, jikinsa yayi sanyi ya tsugunna a gabanta. A hankali ya fara kiran sunanta, "Zainabu zumana kece a haka nan meke damunki?" Ta zuba masa idanuwa kawai tana kallonsa ba tare da ta tanka masa ba, ya kamo hannunta yana fadin, "Kice mini wani abu ko naji dadi mana." Ta fizge hannunta da karfi tana harararsa kamar ta gane shi. Ya kwantar da kai yana fadin, "Zainabu kiyi mini magana mana ko zanji dadi a cikin zuciyata don Allah." Sadiku ya dago labulen ya shiga dakin da sallama ya sami guri ya zauna, Mustafa ya mika masa hannu da sauri suka yi musabiha sannan ya fara da cewar, "Wallahi ko da wasa ban yi zaton Zainabu bata da lafiya ba, mun sami sabani da ita da ya sanya nayi fushi da ita nace sai ta nemeni da kanta ashe ita tana nan babu lafiya, garin yaya aka yi haka ta fara da ita?" Sadiku yayi ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ranar da kuka rabu a daran ai ta sami wannan lalurar, domin dai Zaid yana biye da ku komai ya faru a gabansa."Ya dafe kai yana salati sannan ya ce, "To yaya aka barta a gida ba'a kaita asibiti ba?" Sadiku ya gaya masa duk irin maganin da ake yi mata, suna cikin magana Zaid din ya shigo dakin da sallama, shima din suka gaisa sannan suka kama tattaunawa akan maganar ciwon Zainabun, ita kam kallonsu kawai take yi tana zare idanuwanta. Sun dai rabu akan gobe zasu tattauna abinda ya dace idan fita da ita kasar waje ma za'a yi to sai a fita da ita din. Da wurwurin Mustafa ya shigo gidan ya yo musu siyayya kaya kala-kala domin dai sai almajirai ne suka dinga shigowa da su, Sala kam murna ta cika ta matuka tasan lallai Zainabu ko bata da hankali tana da masoya na gaskiya. Ya shiga da fanice a hannunsa domin dai ya san tana matukar son shi shine kuma ya koya mata son shi tunda mutuminsa ne, ya zauna a gabanta yana fadin "Zainabu ki sha ice cream din da kike so ne." Ya matsa gabanta ya zauna sosai ya bude fanice din yayi kankara kuwa gwanin dadi, ya sanya cokali ya datso ya mika mata a bakinta, babu musu ta bude baki ya zuba mata, ya ji dadin hakan kuwa don haka ya cigaba da bata, cokali hudu ta sha ta shammace shi ta warce ta watsa masa a jikinsa, ya firgita matuka domin bai yi zaton hakan ba ga sanyi da ya ratsa shi ya mike yana salati. Sala ta shigo da gudu tana fadin, "Ta bata maka kaya ko? Ai ban san abu zaka bata ba da na gaya maka watsawa mutum take yi a jikinsa, bari a kawo maka abu ka goge." Ta mika masa toilet paper da Zaid ya siyo don Zainabu din, ya goge jikin nasa yana fadin, "Kada ki damu babu komai ai ba da hankalinta tayi hakan ba, Zainabu mai tsafta da son gayu ba zata batawa mutum jiki ba ban da lalura ba." Suna cikin haka Zaid ya shigo ya mika masa hannu suka yi musabiha sannan suka fara tattaunawa akan maganar jiya. Zaid ya ce, "Akwai wani asibiti da na sani a Madina mai kyau ne wanda ya shafi masu lalurar tabin hankali ina ganin can ya dace a kaita." Mustafa ya yi dan jim sannan ya ce, "Ba wai naki shawararka bane amman anan ma muna da kwararrun likitocin da zasu iya nake gani, mai zai hana mu gwada su mu gani, akwai wani abokina Abdul- Wahab Masanawa (Duba littafin labarin Fauziyya) kwararran (Phyciatric doctor) ne, don na sha ganin mutanen da suka samu lafiya a hannunsa don haka zan tuntibe shi muji abinda zai ce din." Da wannan shawarar suka yi matsaya, har Zaid ya tafi ya bar Mustafa domin dai zama yake a gabanta yana surutai kamar yana yi da wata mai hankali. Dr. Abdul-Wahab Masanawa na Fauziyya ba da kanka a sare kaje gida ka ce ya fadi, shine ya amshi case din Zainabu, ya ce amman dole sai an kaita asibitinsa da ya bude na masu tabin hankali din, babu musu aka kwasheta aka yi can da ita. Tana samun kulawa matuka domin dai baya kyankyamin ko kyarar masu tabin hankalin yana bi dasu da lallami da rarrashi, don haka ba tare da bata lokaci ba ya hau bincike akan Zainabu ya gano abinda yake damunta kamar yanda aka fada tun farko don haka ya dora ta akan magungunan da yake ganin zata samu lafiya. " Cikin sati guda sai gashi ta fara surutai har da nuna abu idan tana so a bata, don haka 'yan uwanta suka ji dadin hakan, kada dai Mustafa da Zaid su ji labari, har an rasa waye ya fi kulawa da ita. Zaid ya so ya biya kudin da komai na magunguna amman sai aka ce masa ai tun kafin a kawota an biya komai, ya san ba wani bane illa Mustafa, shi kam har ya fara sarewa da lamarin Mustafa din. Kanwarta Karimatu ke jinyarta duk da ba a kwana a gurinta sai dai a wuni, suna cikin asibitin ne Asma ta zo duba Zainabu domin bata gari sai da ta dawo ta sami labarin abinda ya sami kawar tata, tana can tana yawon sare-sare domin dai ta koma business domin dai karuwancin ya fara ja baya sai dai tana tabawa idan ta hadu da abokan watsewarta. Sanda taga yanda Zainabu ta koma sai da ta yi kuka da nadama, sai taji harkar bariki da shaye-shaye duk sun fice mata a ranta, wai kuma yanzu ma ta fara samun sauki, lallai ta yadda mutum ba a bakin komai yake ba musamman da taji irin mutuwar da DPM ya yi, don haka tun da ta dawo bata koma ko ina ba kullum tana tafe asibitin kusan tare suke wuni da Karimatu din ma. Cikin wata biyu Zainabu ta sami lafiya da taimakon Allah da na dakta Masanawa, duk mai son ta ya taya ta murna matuka, aka sallameta har da satifiket din wanda ke tabbatar da lallai ta warke din. Karimatu duk ta sanar da ita abunda ya faru da ita da irin dawainiyar da masoyanta suka yi mata, ta kuma tsorata da duniya matuka don haka bata magana ko hira kullum tana cikin lazimi tun da ta fara samun sauki. Zaid kam tana ganin girmansa da darajarsa matuka, yayin da taji son Mustafa ya lunku a ranta, ta tabbatarwa da kanta shi din mai kaunarta da son ta ne tsakani da Allah, lallai yana da hujjar da ta sanya shi yayi mata abinda yayi mata a baya, sai dai idan ta tuno babu aure a tsakaninsu sai taji bacin rai da tashin hankali matuka, ga shi yanzu bata iya sakin jiki tayi magana da shi kamar da duk ta zama wata iri kamar ba ainihin Zainabun da jama'a suka sani ba ma'abociyar tsiwa da rigima da fitsara ba. Sanda suka koma gida kam ta kuma shiga taitayinta ta tsananta neman gafara gurin mahaliccinta da neman kusanci da shi, idan kaga ta fito tsakar gida to lallai wanka ko alwala zata yi, har Sala tana mata tsiya ita kam yanzu rayuwar ta fice mata a kanta musamman da aka gaya mata mutuwar DPM, ta kuma tuno da abinda ya faru gare su, bai taba tunanin sauran mintina kalilan ya mutu ba, ba don ta tsaya sun yi sa'insa da Mustafa ba sannan ta ce sai ya koma da ita gida da ta amince masa da yana cikin aikata alfasha Allah zai karbi ransa, yanzu shi kenan tasa ta kare, idan wannan tunanin ya zo mata takan wuni tana kuka. Sai ta fara yiwa Sala da kanwarta Jamila nasiha akan abinda take aikatawa, amman sai Jamila din ta hayayyako mata tana fadin ta kyaleta ita sanda tayi nata iskancin waye ya hanata don haka ta kyaleta kawai itama ta more lokacinta. Don haka ta zuba musu idanuwa kawai, sai dai idan Mustafa ya zo su gaisa bata iya sakewa da shi domin gani take yanzu bata da darajar sauran mutane tunda dai har hauka ta yi, da ya lura da halin da take nuna masa ne ya shiga zuwar mata da takwararta sannan ya gaya mata dalilin da ya sanya ya boye mata haihuwar Zainab din, ta amince da abinda ya ce din amman tana ganin yanzu ita kam rayuwarta bata da sauran amfani da ya wuce tayi bautar Allah da tuba bisa laifukanta.Ranar wata laraba suka shiga wani mummunan tashin hankalin a gidansu, Jamila ta tashi da rashin lafiya ga amai da zazzabi mai zafi, hankalinta ya tashi matuka domin tana ganin abinda ya taba faruwa da ita ne ke shirin faruwa ga kanwar tata, sam Sala bata farga ba sai da ta sanar da ita abinda take tunanin sannan ta farga. Hankalin Sala yayi mummunan tashi ta kama salati da sallallami, nan kuma suka hau zare idanu suna sallallami lallai biri yayi kama da mutum. Sala ta dubi Jamila da jan ido sanda ta tsareta a daki tana fadin "Ki gaya mini wanda yayi miki wannan cikin, shin wai ina kwayoyin hana daukar cikin da kike sha ne ma naga kina amfani da su." Ta yi narai- narai da idanuwan ta tana fadin "Wallahi Sala kullum sai na sha, shi ya sanya ma banyi tunanin ciki ne dani ba sai da kika fada na tsargu, ni ai ba zan san wanda yayi mini ba takamaimai tunda ina hulda da mutane da dama." Sala ta ce, "Haka ne, shike nan gobe idan Allah ya kaimu zamu yi sammako muje gurin wani likita da yake zubar da ciki a cire miki ki huta nima na huta, sai ya baki shawarar yanda za'a yi." Zainabu dake alwala duk tana jinsu don haka ta shiga dakin Sala din ta sami guri ta zauna tana dubansu sannan ta fara magana, "Sala kada ku zubar da cikin nan domin kuwa babban hatsari ne da shi, na farko kinga dan iskan likitan nan yayi lalata da ita da karfi da yaji, sannan zai kakaba mata karafuna wanda azabar su ba zata kwatantu ba, sannan kuma zai iya lalata mata mahaifarta ta rasa haihuwa a gaba, ki dube ni shekara nawa da aure amman ban ko taba batan wata ba, wadanda muka yi aure da su sau nawa suka haihu, ga kuma azabar Allah." "Da zaku ji ta tawa da kun hakura da zubar da cikin nan, sai a kaita can wani guri ta reni cikinta ta haihu, wallahi ni nayi alkawarin zan rike duk abinda ta haifa na zama nice uwarsa, don a yanzu nayi nadama matuka akan zubar da cikin da nayi a baya ashe shine kadai rabona a duniya na haihuwa, yanzu ko mutuwa nayi bani da masu yi mini addu'a." Gaba daya suka hayayyako mata da masifa, Sala tana fadin, "Lallai Zainabu zuciyarki ta mutu murus, haka kawai don mu jawowa kanmu abin kunya sai mu bari ta haihu? So kike ayi ta zundenmu kenan." Ita kuwa Jamila cewa ta yi, "Rabu da ita Sala don dai tasan abin kunyar ba a jikinta yake ba, sanda tayi nata cikin mai ya sanya bata barshi ta haihu ba sai yanzu da yazo kai na, to wallahi baki isa ba sai an zubar mini." Lallai ruwa ya doki babban zakara domin dai Zainabu bata kuma cewa komai ba ta mike ta nufi dakinta amman dai tana jin kyamar abinda zasu aikata din matuka, ta yi sallah tana rokon Allah ya shirya Sala kamar yanda ya shiryeta. Washegari kuwa suka yi asubanci suka nufi asibitin da aka taba zubarwa da Zainabu ciki shekarun baya da suka wuce, sai dai babu asibitin sai shaguna da aka maida gurin, gaban Sala ya yanke ya fadi ta dubi Jamila amman ba tace komai ba, sai ta matsa kusa da wani mutum dake sai da nama a gurin dan bata manta sanda suka kawo Zainabu ma ta ganshi. Ta dubeshi da fara'a tana fadin, "Barka da rana bawan Allah." Ya dago yana dubanta ya ce, "Barka ka dai Hajiya, ina fata dai lafiya ko?" Ta gyara tsayuwarta ta ce, "Eh to lafiyar kenan, daman wani asibiti nake nema wanda na san shi anan gurin naga kuma yanzu ban ganshi ba sam."Ya kalleta sosai gami da kallon Jamila domin dai ya san dun mai zuwa wannan asibiti zubar da ciki ya zo, ya kuma kallon Jamila wacce ya tabbatar da lallai ita za'a zubarwa da cikin, a zuciyarsa ya ce "Allah ya shiryeku" A fili kuma cewa yayi "Hajiya ai wannan asibiti yayi kusan shekara takwas ko tara da rushewa, domin dai hukuma ta gano irin barnar da ake aikatawa ashe har safarar jariran da aka ciro ake yi don haka aka kama likitan aka yi masa kisan gilla ta hanyar rataya, sannan kuma sauran ma'aikatan duk aka kullesu sannan gwamnati ta kwace filin daga gurin mai shi tunda yasan abinda ake aikatawa a gurin shi ne aka gina shaguna na haya." Sala ta dafe kai tana salati ta ce, "Yanzu shi kenan an tashi asibitin nan, amman ba'a kyauta ba, kai naga ta kaina yanzu yaya zan yi." Ta dubi Jamila wacce ke kallonta. Mai naman ya kuma cewa, "Hajiya ya dace kome ya same ku ku yadda da kaddara kada ki je garin neman gira ku rasa idanuwa.....

kaga malam ba wa'azi nace ka yi mini ba na gode, muje ke." Ta katseshi da sauri sannan suka wuce suka tafi, a hanya ta yanke shawarar zuwa gidan sister, duk da dai sun dade rabonsu da ita. Sanda suka isa gidan ma sai suka ga kamar alamar da mutane da yawa a ciki sabanin da can da suka san ita kadai ce a ciki abinda ya baiwa Sala mamaki, sai dai tayi sa'a akwai shagon aski da ta gani a jikin gidan don haka ta matsa tana tambayarsa. "Barka da da rana malam yaya aiki da gari? Don Allah ina tambayar sister domin dai naga kamar bata gidan yanzu." Ya kalleta da kyau sannan ya ce, "Hala Hajiya kin jima rabonki da ita? ai sister ta jima da rasuwa, tun sanda aka kai mamaya wani asibitin kudi da take aiki aka kama su, ita laifi biyu aka sameta da shi na yin aiki biyu a lokaci guda sannan ga laifin da aka samu asibitin da shi, don haka hukuma ta soke takardar aikinta da aka bata sannan aka daureta shekara shida, bayan ta dawo gida ne ta gama zamanta a kurkuku jinya ta tsananta a gareta don daman tun can bata da cikakkiyar lafiya, daga karshe dai aka gano cutar kanjamau take dauke da ita, daga karshe 'yan uwanta suka saida gidan nata aka yi mata magani karshe dai ta mutu a asibitin zana shekaru biyu kenan da suka wuce." Sala ta kama tafa hannu tana salati tana fadin, "Yanzu sister ta rasu kenan, Oni Salamatu Allah mai iko, to Allah ya jikanta. Muje Jamila." Ta baiwa diyar tata umurni. Suna tafe cike da tashin hankali can Sala ta ce, "Yanzu haka zamu koma gida muna ji muna gani ki haihu? Kai amman da munga abin kunya da tashin hankali, kai 'yar nan kin jawo mana masifa." Jamila ta tabe baki tana fadin, "Ki ji Sala, ina ce kece kika daure mini gindin na tara miki kudi, sai kuma yanzu za ki ga laifina, amman dai akwai wani asibiti da naji wasu kawayena suna fada wanda ake zubar da ciki a can Wazahad ko muje can din mu gani ko zasu zubar mini?" Sala ta washe baki tana fadin, "Yauwa diyar albarka, kice kema kin san wani guri, bari mu tare babura mu hau domin dai bani son ki kwana da cikin nan kada munafukai su farga." Suka tsaida babura suka haye suka nausa Wazahad. Sunyi da ce kuma likitan shima kabila ne ya amshe su ya cajesu kudin da yake bukata suka biya sannan aka shigar da Jamila dakin da ake cire ciki, Sala kam gani take yi ai ta rabu da cikin ta gama cikin 'yan mintuna domin dai na Zainabu ma bada jimawa aka rabata da shi ba.Minti talatin, awa daya, biyu har zuwa awa biyar ba'a fito da ita ba, har ta gaji da jira can dai tayi kokarin lekawa cikin dakin sai taga ba kowa, ta kuma tura kofar a hankali sai ta buda ta tura da saurinta amman bata ga kowa ba sai alamar fita da aka yi ta dayar kofar, can ta hango Jamila kwance a gado jini yana zuba ta gabanta da alamar ko motsi bata iya yi, ta nufeta da sauri hankalinta a tashe sai taga ai ta jima da mutuwa ma, ga abinda aka dauko cikinta nan cikin wata 'yar tasa ta likitoci har an fara yi masa halitta, ta sanya hannu a kai ta kunzuma ihu cike da tashin hankali tana neman dauki amman babu kowa, domin dai daman asibitin kamar gida yake sannan shi daya tal suka tadda, wato dai guduwa yayi da yaga ta mutu kenan. Sala ta bazamo waje tana neman taimako amman da yake unguwar duk babu hausawa ya sanya babu wanda yake jin abinda take fadi ma, ta yi kukan ta more idanuwanta suka yi luhu-luhu, daga nan ta mike tayi can titi domin ta samo wanda zai kaisu gida, da kyar ta samu wani mai tasi domin duk wanda ta yiwa bayanin abinda ya faru sai yayi gaba abinsa, shima dai da suka tsadance kudi mai yawa sannan ya yadda, suka ciccibeta da kyar suka sanya a bayan motar har lokacin Sala kuka take yi. Sanda suka isa gidan aka kiraye-kirayen Sallar Isha'i, don haka ta shiga da sauri ta kirawo Zainabu ta ce tazo ta taimaka musu su shigo da ita cikin gidan tun mutane basu farga ba. Sanda Zainabu ta ci karo da gawar Jamila jikinta tsima ya kama yi ta kama kabbara da kiran sunan Allah, da kyar ta iya daurewa ta kamata suka shigar da ita cikin gida, sai a sannan ta ji kuka mai ciwo ya kamata ta fashe da kuka tana fadin, "Sala yanzu wacce riba kika ci da wannan mummunan aiki da kike aikatawa? Yanzu me zaki cewa Ubangijinki da ya baki amanar mu? Ki dubi Jamila ta mutu sakamakon zubar da ciki, da wanne hali zaki tunkari Allah? Shin kina zaton zaki dauwama a duniya, yanzu ina abin duniyar da kika tara tun daga kaina har zuwa Jamila? Babu saboda haram bata albarka, ki dubi gidan nan gaba duk wani abu da kika gani Karimatu ko Sadiku suka kawo shi, duk abinda na tara ya kare saboda haramtacce ne balle na Jamila, sai ki tuba ki san rayuwa ba a bakin komai take ba." Saboda kuka muryar Sala har ta dashe dan tunda take a duniya bata taba nadamar abinda take aikatawa kamar yau ba, yanzu ace diyarta guda ta mutu gurin zubar da ciki, abin kunyar dai da take gudu ya riga ya fita, amman dai zata roki Zainabu ta rufa mata asiri don haka cikin kuka ta ce, "Abula nayi nadama mara amfani sai yanzu na gane gaskiyar da kike gaya mini, da ace Jamila mutuwa zata yi wallahi da na barta ta haifo ko 'ya'ya goma ne, na shiga uku na lalace yanzu shike nan na rasa diyata, amman ina neman ki rufa mini asiri mu samu mu gyarata sannan mu sanar da mutuwar tata, kuma zamuce rashin lafiya tayi na wuni daya ki rufa mini asiri don Allah." 

Zainabu ta dubi Sala ta ce, "Idan ni na rufa miki asiri Allah ai ba zai rufa miki ba, domin sai kin amsa abinda kika aitaka ranar tsayuwa don haka abu mafi a'ala ki tuba kawai, ki sani yau abinda Sadiku yake jiye miki shine ya same ki, ya sha sanar damu irin wannan rana, wacce Allah zai maido mana da mugun aikinmu kanmu." Sala tana kuka take fadin "Ya isa haka nan Abula na tuba na bi Allah, ba zan kuma aikata abu makamancin wannan ba, ki taimaka mini mu gyara Jamila." Zainabu ta taimaka mata suka gyara ta suka sanya mata kunzugu don kada a gane, domin dai jini bai daina zubowa ba, sai da suka tabbatar ta gyaru sosai sannan ta fasa ihu tana kuwwa, Zainabu na hanata amman ina yi take yi kamar ranta zai fitaKan kace kwabo gidan ya cika da mutane sannan ta fara ambaton mutuwar Jamila, nan da nan gari ya dauka, jama'a kowa da abinda yake cewa. Sadiku ya shigo cike da tashin hankali sanda ya sami wayar Zainabu sai dai ta sanar da shi abinda aya faru komai da komai, ya zube a tsakar gida yana kuka mai sosa rai da Allah wadaran halin Mahaifiyarsu, mutane da dama sunyi zaton ko zafin mutuwar ke damunsa, amman shi hanyar da ta mutu din tafi yi masa ciwo akan mutuwar ta ta, can sai ga Karimatu ma ta shigo da nata kukan, suka hadu suka kokawa kansu har jama'a suka tafi gidajen su domin dai dole sai tayi kwanan kesou. Anan suka kulle kansu a daki suna nanata zancan, shi kansa Baba Abbakar ya shiga tashin hankali matuka da jin sanadiyyar mutuwar diyar tasa. Sadiku ya dube shi yana fadin, "Baba ka sani yau kaci amanar da Allah ya baka ta tarbiyyarmu da renonmu, domin ka sakarwa mace ragamar rayuwarmu wacce ba itace ya wajaba ta tarbiyyantar da mu kadai ba sai da sanya hannunka, yanzu ka dubi gawar Jamila ka kuma ji dalilin mutuwarta gurin zubar da cikin shege, to ka tabbatar Allah zai saka mana bisa abinda ka yi mana kai da Sala, domin kamar yanda kake da hakki a kanmu muma muna da shi a kanka, babu ruwana da abin da kake aikatawa a waje wannan kai da wadanda kake yiwa ne, sai dai zan so yanzu ka rungumemu kamar yanda kowanne uba ke rungumar 'ya'yansa da tarbiyya da kulawa." Jikin Baba Abbakar ya hau rawa, sai kawai ya fashe da kuka yana neman gafara 'ya'yansa, kusan dai zaune suka kwana. Da safe da aka tashi Malam ya ce Zainabu da Karimatu da Sala ne zasu yiwa Jamila wanka, domin haka aka fi so tunda dai bata da miji, yana fatan sun iya.

 Da sauri Karimatu ta ce sun iya, domin dai basu son wani ya ga abinda suke boyewa, kuma aka yi sa'a ta iya din don haka su uku suka wanketa suka shiryata cikin likkafani, sun yi sa'a kuma jinin ya daina zubowa da alaman ma jinin nata ya kare domin dai babu alamar akwai shi a jikinta, domin dai jiya dakin da aka yi mata abortion har kafar mutum nutsewa take yi a cikin jini, domin shi kansa likitan da yayi mata aikin yayi kokarin bayan ya zaro abinda ke cikinta ya tsaida jinin sai dai iyakacin iliminsa ya kare amman jinin bai tsaya ba, domin dai daman bai kammala karatun nasa ba, yana a shekarar karshe ta koyon karatun likita (medicine) aka kama shi da satar jarabawa (malpractice) don haka aka kore shi, shine fa ya gudo daga garinsu can Ibadan ya taho nan ya bude asibitin sirri na masu laifi, domin ba kowa yasan da shi ba sai wadanda ake zubarwa da cikin. To da yaga jinin yaki tsayawa kada asirinsa ya tonu ko Sala ta ce bata yadda ba har ta kai ga an kamashi yasan hukuncin kisa za a yanke masa ya sanya ya hada 'yan kayansa ya silale ta dayar kofar, ita kuwa Jamila da taga zai gudu ta fara yi masa magiyar ya kirawo mata Babarta amman bai kula ta tata ba ya gudu. Ganin ya gudu ya sanya ta far kiran Sala-Sala-Sala, amman ina sam bata ji ba domin dai kofar a kulle take, gashi bata da karfin da zata iya ko da motsawa balle ta tashi, tana ji tana gani jininta yana zuba, nan fa ta fara da na sani da neman gafarar Allah har Ma'aikin daukar rai ya dirar mata, sai dai da alama lokacin karbar tuban nata ya wuce don sai da taga mutuwa gadan-gadan sanda ake rufe kofofin na tuba sannan ta fara tuban, Allah dai shiya barwa kansa sanin yanda zai yi da ita (ALLAH YAYI MANA KYAKKYAWAN KARSHE).


*** *** *** ***

 Kwanaki bakwai da aka yi ana zaman makoki sai dai tun daga wannan rana ta farko Sala bata kuma runtsawa ba ko da safe ko da rana, domin da ta rufe idonta zata ga diyarta tana kuka da farin kaya a jikinta wanda ya rine da jini ga jarirai nan a hannunta suma suna ta kuka, don haka bata iya kwanciya da ta kwanta zata tashi a gigice tana surutai, tun 'ya'yan suna ganin tamkar zafin mutuwarce har suka gane ta fara samun tabin hankali don har kukan jarirai take yi idan dare ya tsala, daga karshe aka fara nemar mata maganin miyagu da na mutanen boye ana bata da rubuta da ruwan tofi a gurin Malam amman abun kamar tiri kamar ana kuma izata, daga karshe suka kwasheta suka yi asibitin mahaukata. Iyakacin bincikensu sun gano lafiya kalau kwakwalwarta take sai suka bata maganin bacci wanda da zarar tasha ta fara baccin zata hau bige-bige da surutai, daga karshe dai aka daina bata cutar rashin bacci ta shige ta. Kwana kusan arba'in suna abu daya, duk 'ya'yan sun shiga tashin hankali da damuwa, amman sun san abinda ta aikata ke bibiyarta, ranar da Jamila ta cika kwanaki arba'in cif da mutuwa itama ta amsa kiran Allah inda kowa sai yaje. Zainabu kam tafi kowa shiga tashin hankali, domin dai duk cikin 'ya'yan Sala tafi kowa shakuwa da ita balle idan ta tuno ayyukan da Sala din ta aikata, ta kuma raina wayon duniya ta san lallai ita din Mayaudariya ce da bata da tabbas balle alkawari, don haka gwara ma ka fara gudunta kai tun kafin ita din ta guje ka. Sai ya zama komai na duniyar ya kuma fice mata daga ranta musamman ranar da aka share makoki kowa ya kama gabansa taji gidan shiru sai ita daya da kaninta, ta dinga tuna Sala da sabgoginta da takeyi a cikin gidan, ta tuno duk irin son kudin ta har ta koma ga Allah bata tara su din ba, daran ranar kam gaza yin bacci tayi don haka ne ma ta dauro alwala ta dinga Salla tana nemarwa Sala sauki da yafiyar Allah, har sai da ta hada da Sallar Asuba sannan ta kwanta bacci. Da safe itace ta hada musu abin karyawa, yanzu kam Baba Abbakar tausayi yake bata domin tun daga mutuwar Sala ya zama wani iri magana ma sai da kyar yake iya yi, baya zuwa ko ina kullum yana kofar gida a zaune, abokansa na majalisarsa sun fara zuwa taya shi zama amman da suka ga koda sun zo sai dai suyi ta zancensu bai sanya musu bakinsa ya sanya suka janye jikinsu. Shi kam bai gajiya da zamansa shi kadai yayi ta tunanin Sala da rayuwarsu. Tana zaune a tsakar gida bisa kujera tana gyaran alayyahu amman har lokacin Sala tana mata gizo, idanuwanta na ta zubda hawaye Zaid ya shigo da sallamarsa. Ta daga kanta sau daya ta dube shi ta mai da kanta kasa, ya iso da sauri gabanta ya durkusa ya kwantar da murya yana fadin "Zainabu anya kuwa rayuwa zata yiwo a haka? Ya dace ki fawwalawa Allah komai, ki kuma tuna inda Sala taje muma zamu je, abinda tafi bukata a gareki kawai addu'a yanzu, bacin ranki yana taba mini zuciya ban son ganinki cikin damuwa Zainabu duk raina sai ya kasa sakewa." Ta dago ido ta dubeshi domin yanda yake maganar tashi sai ya sanya ta ji wani iri a ranta, domin ta fara lura da take- taken Zaid. Ya zame ya zauna a kasa ya kamo alayyahun yana taya ta tsigewa ya cigaba da magana, "Zainabu ina jinki a raina nasan kin lura da halin da na shiga amman ki ke basarwa, shin ko ban kai matsayin da zaki so ni ba? Ni kam na sani Allah ya jarabceni da son ki a raina mai tsanani wannan lokaci."Ta yi shiru kamar ba zata yi magana ba, can dai ta daure ta ce, "Zaid ka yiwa Allah ka bar wannan maganar a ranka domin dai kasan ko ni wacece, ka san iyayanka ma ba zasu yadda ka aureni ba, hali na da tarbiyya ta ba irin naka bane, sai dai naji dadi da ka nuna mini soyayya da kulawa, ba kai ba na san ko wani yanzu ba zai iya aure na ba domin babu wanda zai so auran Zainabu a yanzu, zan zauna nayi ta bautar Allah har nima lokacin karbar rayuwata ya zo." Ya yi dan yake sannan ya ce, "Lallai Zainabu kin jahilci su Malam, to ki sani tuni ya san da zancen ina sonki, ya ce dai nazo na nemi yardarki ne kawai, shi din ai uba ne a gareki ya san ko ke wacece, kuma ko da ace har yanzu kina halinki na da zan iya auranki a haka balle kin shiryu, Allah ya gyara zuciyarki da dukkan ayyukanki, domin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa sallam ya fadi “ 

…..IDAN ZUCIYA TA GYARU, DUKKAN JIKI YA GYARU…..

” Na gani a gareki, ki kwantar da hankalinki Zainabu ki daina ware kanki kina da damar yin rayuwarki kamar kowa domin shi Allah Gafururrahim ne, ki kuma sani ni Zaid bayan ke bana jin zan kuma iya kallon wata mace da daraja Zainabu dai nake so koma wacece ita ko yaya take." Maganganunsa suka sanyata jin kwanciyar hankali, sai dai tana jin nauyinsa matuka yanzu, amman dai ta sani shi din ba abin yadawa ba ne, domin dai yana cikin mazan da zasu birge mace, gashi da ilimi na addini matuka da kyau da mutunci da usuli, ta kuma sani babu wani abu da Mustafa zai gwada masa sai dai abu mawuyaci ne a rayuwarta ta so wani da namiji kamar Mustafa, shi ne kadai abin son ta. Zaid kam ya kafa harsashin gininsa a zuciyar Zainabu ko da yaushe yana tare da ita, maganganunsa na ilimi da karuwa har karatu ya fara koya mata na littafan addini haka ya sanya suka shaku matuka. Mustafa kam ji yake kamar ya shake Zaid domin ya lura yanzu Zainabu ta fi sakewa da shi a kansa, duk ta sauya masa, idan ya zo shi kadai zai yi ta zancensa bata kulashi, hankalinsa sam baya jikinsa gani yake ya rasa Zainabu har abada.

No comments:

Post a Comment