SANYIN IDANIYA
SANYIN IDANIYA
parts 25
Na khadija sidi & Hauwa M jabo.
Abbu shiru yayi Dan baqin cikin da matarsa Huwaila take cunkusa masa, tabi duk ta bata masa tarbiyar yaya. Allah ka tsare mu da iyaye irinsu Gwaggo.
*************
Bayan ya fito restaurant din da yake bashida lecture sai kawai yaje gun gang dinsa suka kama hanya kamar yanda sukace saba yana gaba suna biye, suka wuce gida, sun so su masa tambayoyi, amma basuga fuskaba, sai kawai suka share, kamar yanda suka saba, sun rakashi har gida, sannan suka wuce gida suma.
Moh ya shigo palonsu, duk an hallara ya cire helmet dinsa da shadow dinsa, yaje har gurin dady ya hada kafadarsa da tashi, suka gaisa.
Hajiya bushra ta fito daga kitchen dauke da abinci, sabida duk kudinsu bai saka hajiya bushra qin yiwa mijinta girkiba, sannan saqartawa iya saqartawa tama yaranta, amma hakan bai hana su Fatima da zainb shiga kitchen ba, sun iya girki ko wane iri,
Ya gaida hajiya bushra, ta amsa cikin murmushi da sakin fuska,
Fatima da zainb ma suka gaidashi ya amsa, fuska a sake sabanin da da hannu Kawai xai daga musu ko ya musu murmushi, yanda suke hada abinci a table ya burgeshi, wani murmushi yayi na gefen baki, yadan cije gefen lebensa, ya kuma lashe leben nasa.
Haka Kawai yakejin nishadi, qannensa na burgeshi sabanin da da suke bashi haushi,
Fatima,! ya kirata, na'am ta amsa tana daga ido cikin mamaki, rabon da taji ya kira sunanta har ta manta, tama dauka ya manta sunan ta, zo ki gaya min wane irin kaya yan mata suke amfani dasu,!
Shi kanshi baisan dalilin da yasa yace hakan ba, hasali ma kamar bakinsa ne ya kubuce, ita kanta ta jinjina wannan tambayar
Mi xakayi da kayan mata? Wai ma kayan make up kake nufi ko miye !?
Ya dago ya kalleta, Yace mi akeyi dasu!? Ya tambayeta a ataqaice, tace kwalliya,ya dago ido ya kalleta kallo mai cike da ma'ana sai ta fahimci yana nufin to kwalliya xa'ayi da wayanda xata fada mai.
Ta kuwa xauna ta fara xaro masa su kala kala, harsu dady sukaxo chin abinci, nan dady yake tambaya suruka aka samo mana!? Yar gidan waye, ? Ya musu banxa, ya fara chin abinchinsa, yanachi yana murmushi, Kawai yanajin nishadine, amma baisan daliliba,
Moh kenan gentle wise, komai nashi a natse yake yinsa, kamar bayason aikatawa, wayansa ya dauko ya lalubo number Sumayyah kamar xai kira sai kawai ya fasa.!! ya kira shamo kuxo mu fita anjima, ka kirasu ka gaya musu. Bai jira amsaba ya kashe wayarsa, dama maganar Moh bata wuce biyu ko uku, ya kalli iyayensa yayi murmushi ya miqe ya wuce dakinsa.
Hajiya bushra tace da gani akwai magana bari na bashi na jiyo mana......!

HASKEN IDANIYA
parts 26
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo
Hajiya Bushra ta miqe xatabi Moh, su kuwa qannensa, sun dauka kawai ya tambayane Dan ra'ayin kansa, yanda kosu yan uwansa basa gaban shi ina xai kula wata mace. Wayan Hajiya yayi qara, sai ta dawo ta dauka, bayan ta qare waya ta nufi dakin, tana xuwa taji qofar a garqame ya kulle kenan, tabe baki tayi ta dawo, su fati suna mata dariya, tasan idan ya shiga ya shiga kenan.!
Da daddare Moh kwance kan gadon sa,sanye ya ke da wando three quarter fari da farar singlet,ya na ta wasa da wayar sa, kan numbar Sumayya ya tsaya,ya yi tunanin kiran ta,sai ya ga toh ya kirata ya ce me? sai ya fara kokarin ma ta text, tinaninsa mixai rubuta mata.!? Sai ya rubuta, sai kuma ya goge, yayi hakan yakai sau wajan biyar, har yayi sendn empty text ba tareda ya saniba.!
Bangaran Sumayya kuma kwance ta ke a dakin su,tunanin duniya ne ya ishe ta,ita dai kam ta na fatan Allah ya ba ta miji na gari ita ma ta yi aure ta huta.
Gwaggo ce ta shigo,ta mi ka ma ta kudi ta ce ga duba daya,sauran na aje zan fara rage kayan daki kema ina mi ki taro. Allah dai yasa sanadin arxikin naki kenan, dama ko cokali bakida.! Sumayya ta karba tare da fadin toh Gwaggo, nagode, Gwaggo ta fice Sumayya ta koma ta kishingida. Wayar ta ta ji yayi karar shigowar sako,ko da ta duba sai ta ga sunan Muhammad,ta yi jim ta na tunanin wane Muhammad ta ke da shi a waya? Batasan tayi savin number Muhammad ba, duka wayar ma number Maxa bai wuce 7 ba, ta bude sakon ta ga wayam,empty txt ne. Ta yi jim ta na tunanin ko waye? Koma waye yasanta tunda ga number sa a ciki wata qila itace ta manta dashi, da ta na da kudi da ta kirash ta ji.....oh ashe fa dazu wannan da su ke kira Moh din ya sa min kudi a waya,ni yar arziki ko na ce nagode, ta duba ta ga 5k account balance din ta,ita da ba ta sa kati sama da dari biyu,sai ta zaro ido,lalle ta yi arziki.....har za ta kira numbar da ta ma ta empty txt din sai kuma ta fasa,ko ma waye ya matsu ya bibiya, kila ma shi ma be san ya yi ba,after ol ba ta ma san wanene ba,gwara ta lallaba dubun ta biyar a waya ya ma ta wata da watanni ...ita kadai ta ke magana,Lele ta shigo ta na Adda lfy?kar dai kyautar da aka mi ki yau ce ta sa ki za ki zauce,tun dazu fa na ke jiwo surutan ki! baki bude Sumayya ta ce dadi na da ke Lele rashin kunya wlh.! tun da ba a taba min kyauta ba dole na zauce.! Lele ta dara kana ta ce ba dai a taba mi ki wacce ta kai wannan ba....Sumayya ta dauke kan ta ta na fadin ban da lokacin ki mara kunya kawai. Lele dariya har da shekewa,wai dubu biyar ya sa Adda sumbatu.!
Aje wayar yayi, kansa yayi zafi sosai, ya fara jin haushi, ba gaira ba dalili, ya tashi,Kai tsaye wata drower ya nufa, ya saka pin numbers ya bude, sai ga wani dan karamin akwaiti sai kyalli ya ke,ya dauko ya mayar da dorowar ya rufe,kan gadon shi ya koma ya zauna,sannan ya bude akwaitin,ya dauko wata powder fara kal cikin Leda,ya bude ya dan shaka sosai, sannan ya jefa kai baya kamar irin ta buge shi sosai, sanin ya dawo ya diba da yatsun sa, ya na sakawa a hanci ya na shaka,kasan hancin sa duk garin ya bata tuni ya rikide kamar ba Moh dinda kuka saniba, idonsa sunyi wani jaaa .... na kalli Jabo jiki na rawa na ce kai yar uwa zo mu cika rigar mu da iska ya fara sana'ar ta sa..,Jabo ta tsaya idanun ta kan sa tana fadin Sidiya ba haka ake ba,ya kamata mu san abun da ya ke shaka dan kar mu bar ma su karatu cikin duhu....ganin ya na wani irin cijewa ya na dukan goshin sa da hannu iya qarfinsa.....tuni na rude, na juyo da sauri nace Sidiya na yarda da zancen ki,mu gudu kawai, na ga wayam ba sidiya ba labarinta, dan ina, tuni sidiya tayi takanta,ta bar Jabo yan ganin kwakwaf,da sauri nima na cika rigar ta da iska nace ai ba haka ake rayuwa ba ka tafi ka bar dan uwan ka cikin hadari!!......

parts 27
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
************
Rayuwar Sumayya haka ta ci gaba da tafiya,Allah na ta hada ta da Moh,ita kuwa sam ba ta kaunar hakan, ita ji take gara kowa ya tsaneta, akan Moh ya kulata. dan gaba daya ya addabi rayuwar ta na makaranta,sai ta na zaman zaman ta ba zato ba tsammani ta ga mutum a kan ta, kuma yazo ya tsareta da mayun idonsa, hakan na bala'en takuramata kuma ya hanata sakewa.
A kwana a tashi semester ta yi nisa,an kusa fara exam,ga wani sanyin da ke shigowa ana fama da hazo. Da la'asar sakaliya,lecture din yamma Summayya ta yi,ta taso a gajiye ta ci sa'ar samin mota da wuri. Ta na zaune bayan bus,wasu samari su ka zauna gaban ta,sai zuba su ke kamar kanya, duk sun cika mata kunne da surutu, ba halin magana tunda motar kasuwace, haka dai aka dauki hanya. Kamar daga sama ta ji sunan Moh a bakin su,tuni ta kasa kunne tana ji mi xasuce.
Daya daga cikin su ta ji ya ce toh kai wannan girman kan na sa da fadin rai aka ce ma ka na banza ne?mutumin da ba wanda ya ke tsoran takawa,mai takalmin karfe kuwa, ya taka mutum kuma ya taku.... ai hakan sai dai mai shakar powder din!!!dayan ya ce gaskiya dai kam,wata rana fa shi kadai za ka ga kamar jin kan sa ya ke ya na fizgar sa,na farin ya ce ba ta sake shi ba kenan. Dayan ya ce wai kuna nufin shaye shaye ya ke?ai ni na zaci tsabar takama da arzikin uban sa ne kesashi yin hakan, nifa na tsani guy dinnan,! dayan yace ni kawu bala'en burgeni sukeyi, shaye shayen ne kawai ke hadani dashi, Dayan ya ce a haba, ai duk bike riders din nan ba wanda baya taba shaye shaye....Sumayya ta sa hannu ta kama baki,sai da ta kusa da ita ta dan kalle ta,ta yi saurin wayencewa da goge baki...ta na ji saurayin ya kara da ba fa shaye shaye irin na tsami ba kamar su wiwi ko giya ba,yaran nan Moh cocaine ya ke shaka.....sumewa ne kawai Sumayya ba ta yi ba dajin abinda Moh yakeyi, aranta ta jinjina cocaine!!! ,ashe dan cocaine ke bibiyan ta.....!!!

parts 28
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
Dayan ya kara da ummm mazaaaaa manya kenan!!!in ba dan gwaska ba ina ya isa ya sami cocaine,yasin ina yin sa, yana wani daga hannu, burge ni ya ke dukda hakan,!!! Dayan ma ya ce ko ni ma burge ni ya ke, dayan ya taboshi yace waima na ji ance wata gurguwa ya ke ma wayo........gaban Sumayya ya fadi daram!!! Dayan ya ce ka dallah,in ma wayon ne ga classy gurls ya rasa wacce zai ma wayo sai ita..ya ce wlh a gaban ido na rannan ya ce kayan sa ce!!!! Kai Moh fa ba ya harkar mata,no homo amma. Toh akan yarinyar nan dai wannan muryar ta shi da ba a ji sai ka ji shi har gate wlh,haka za ka ganta simi simi ta na cilla kafa,amma yawanci sai ka gan sa biye da ita, wani lokaci ma fa tana tafiya yana biye da ita daga baya bata ma san yanayiba, waya sani ma ko irin su daya,jirgi daya ya kwaso su kila yar hannu ce,ka san wasu ba a gane su,ka bar mace kawai wata salihar ta fi wata shegiyar shegentaka....su ka yi shewa su ka tafa.
Jikin Sumayya har rawa ya ke,ashe haka ake ganin ta? ashe bakin fenti na bibiyan ta ba ta sani ba. Allah kadai yasan masu kallon ta irin hakan, tsaki tayi saida ta kusa da ita ta kalleta, itakam Adduar ta be karbu ba,dan kuwa har aka zo inda za ta sauka samarin nan ba su sauka ba. Haka ta ce a tsaya,ta dan ja hijab din ta gudun kar saurayin nan da ya ce an yi a gaban sa ya gan ta,ta sauka,su ko lura da ita ba su yi ba. Tsayawa ta yi dan kar ta fara tafiya su gan ta su gane ita ce,sai da ta bari motar ta kure sannan ta kama hanyar gida,ta na tafe ta na goge hawaye,Allah ya so har ta je gida ba ta hadu da Usman ba,haka ma Gwaggo ta na sallah ranar da baqin ciki ta kwana, bata bari ko lele ta gane halinsa take cikiba.
************
Zaune su ke a inda aka ware dan hutawa cikin gym din da su ke zuwa,dukkanin su sanye su ke da sport wears,rigunan armless. Sun gama exercise ne su ke hutawa kan su tafi gida. Shamo ya dubi Moh wanda yake zaune kansa a qasa ya tsurawa gorar ruwan da ke hannun sa ido, ya ce Moh,pls for d last tym,me ka ke bukata da ga wajan yarinyar nan?Moh ya daga kafada ya sauke ba tare da ya tanka ma sa ba bare ya dena kallan abun da ya ke kallo idonsa suna kafe a gurin, Mu abokan ka ne,ya kamata ka fada ma na,in ji Son...Mike ya ce ko ni ma abun na daure min kai. James ya kalle su ya na kokarin sauya takalmi ya ce no comment from me...shirun da ya mu su ya sa su fidda rai da jin amsar su.....
HASKEN IDANIYA
parts 29
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Kusan 2 mint Ba tare da ya dauke idan sa kan abun da ya ke kallo ba ya ce nothing, am just working on her no more no less......in lokacin da za ku fahimta ya yi za ku gane,for now ask no more...
ya aje goran ya tashi ya nufi hanyar fita. Shamo ya jinjina kai,ko mene abun working kan wannan local gurl din kuma gurguwa,?duk ajin Moh ya rasa wacce zai na bibiya sai wannan gurguwar?Mike ya murmusa ina wani aji tin da ya kira wannan kayan sa,ai ya fado. Son ya kara da nd hez becoming more nd more arrogant!! Moh ya dawo hannun sa dauke da wani ruwan,ya ji kalaman Son na karshe,ya zauna tare da fadin may b i was born arrogant by nature.....So d more nake girma d more zan na kara zama arrogant don't you think? yana gama fada ya bude ruwan ya kai baki kan sa a sama ya na sha,James da tuni ya gama sauya takalmin na sa ya daki kafadar sa cikin wasa ya ce son of a gun!!!!!!
duka su ka yi dariya amma ban da Moh da kawai sauke ruwan yayi daga bakin sa ya na danyen murmushin nan na sa.
***********
Daren ranar da kyar Sumayya ta sami bacci,tunanin hirar samarin nan ne ya tsaya ma ta a rai. Washagari ta shirya tsaf za ta makaranta,sai ta ga takalmin nan na ta da ta ke bala'en ji da shi ya kusa tsinkewa,ta na son aran na Lele ta na gudun raini,dan haka sai ta tari aradu da ka,ta sa shi haka ta lallaba ta dawo tinda lecture daya gare ta. Dan haka ta dau hudajjiyar jakar ta,ta karbi kudin mota gun Abbu,ya hada da nasihar da ya saba ma ta kullum,ya ce" Sumayya ki dage ki yi karatu,shi ya kai ki makaranta,ban da abun da zan iya baki a matsayi na na mahaifinki da ya wuce ilimi,ban da arziki ban da komai,ki yi karatu ki sami ilimi shi ne arzikin da ni mahaifinki na baki...kar ki yarda wani abu ya taba karatun ki bare rudu irin na jami'a......."Sumayya ta ma sa godiya,ta ma Gwaggo sallama sai makaranta.
Can makaran ta kuwa,bayan Moh sun fito daga aji sai ga kiran Dad,ya ce da shi tafiyar nan tashi nan da 3hours ne,ya na so su gana kafin nan,ya ce toh Dad,bara na taho yanzu ma. Ya kalli su Shamo ya ce old man ya kira ni,za ku wuce ne ko kuwa?duka su ka tashi,kowa ya sa hamlet din sa,da niyar tafiya,ga mamakin su shi wanda ya ce a tafi din shi ne ya tsaya be fara shirin tafiyar ba,ganin ya cire hamlet din na sa ya bi wani waje da kallo ya sa su ma su ka kalli wajan,nan su ka hange ta tafe,sai dai tafiyar na ta na yau ya sha bambam da na kullum,dan yau kafar da ta ke daidai shi ta ke jan takalmin kafar ta da ya tsinke ma ta.!

parts 30
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Sumayya kuwa sam ba ta lura da su ba,cike ta ke fam da takaicin ragon azancin da ta yi,ai gashi ta na sauka daga motar ta yi tuntube takalmin ya tsinke. Ta zo dab da su Shamo ya ce Moh wannan kayan na ka......Moh na duban Sumayya ya ce kar ka haura gida na....ya aje hamlet kan bike din sa ya karasa gun Sumayya ya bar abokan sa cike da takaici.
Sai a sannan Summayya ta yi ido hudu da Moh,gaban ta yayi mummunar faduwa ganin shi tsaye gaban ta,maganar samarin jiya ne ya fado cikin ran ta....ta tsaya cak ta kasa magana. A hankali ya ce ki tsaya na sama mi ki ride,kai kawai ta gyada mai dan kuwa ta gama gigicewa. Su James su ka tsaya ganin ikon Allah,wai Moh ne da kan sa ya sa hannu ya tsaida mota dan a ma sa alfarma. Ita kuwa wacce aka tsayar da ta ga Moh ne tuni ta ja ta tsaya,yau Moh ne da kan sa ya tsaida ita. Yiwa Sumayya alamar ta taho ya yi sannan ya dan sunkuya ya kalli ta motar tare da fadin sunnun ki,ko za ki iya taimakawa kaya na? yarinyar ta murmusa wai yau ita ce Moh ke yiwa magana,da sauri ta na dan waige ta na fatan Allah ya sa daya daga cikin kawayen ta su ganta tare da Moh, koba komai yau ya daga class dinta, ta ce haba it is my pleasure Moh. Ta na jira ta ga ya dauko kayan na sa,sai gashi ya bude gaban mota ya ce zo ki Shiga..me za ta gani sai ga Sumayya ta shigo....ta yi kokarin boye disappointment din ganin mace ce ma,ta ce ina zan sauke kayan na ka....?ya kalli Sumayya ya na neman amsa,ta ce lecture hall A11 accounting department.....ya kalli yarinyar ya sakar ma ta murmushin mai kayatarwa, duk da ta san social bribe ne ba ta san sanda ita ma ta mayar ma sa martani da saurin ta ba,ta kara da zan kai ta a rude take da ganin yanda ta bada amsa,. Ya tsunsa biyu ya sa a goshi sannan ya sauke,alamar ya gaishe ta,murna kamar ta yi ihu,lalle kawayen ta za su ji wannan,ta tada motar ta,ya gyadawa Sumayya kai da ta yi zugum ta na ganin duniya. Yarinya ta yi gaba far in ciki fal ran ta.
Son ya ce ai sai ka zo mu tafi ko? Moh ya dawo ya dau hamlet din sa ya sa,ya haye bike din sa tare da fadin na sami change of plan,in kuna da abun yi, kar ku jira ni.....ya tada bike kamar walkiya ya bashi wuta,ya bar su suna kallan juna,jikin su ya fara sanyin da Moh,dey ar losing him to Sumayya duk da dai ba su san takamammen in da ya nufa ba,ba wai son Sumayya kadai ne ba sa yi ba,balain kishi su ke da ita. Ya za su yi Moh ya zame mu su jiki lokaci daya akan wannan gurguwar, Dole su ka zauna jiran gawon shanu cike da takaici.
HASKEN IDANIYA
parts 31
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Har aji yarinyar ta sauke Sumayya,ta ce dan Allah ya ki ke da Moh?dan uwan ki ne?Sumayya ta bude baki za ta ce ah ah,sai ta tuna zancen samarin nan ta yi saurin cewa eh,ta bude motar da sauri ta fito,ta rufe ma ta kofa ta na godiya, yarinyar ta ce madallah, ita kam yarinyar yau jinta take a sama, wai Moh ne ya mata magana....
Kai tsaye aji ta nufa ta na jan takalmin ta. Ta yi sa'ar samin gaba, ba da dadewa ba lecturer ya shigo. Saurayi ne dankwalisa irin ma su ji da kan su dinnan,da ya shiga ya ke jan kofar sa ba bu mai shiga.
Ya na shiga ba tare da bata lokaci ba ya fara abun da ya kai shi.
Moh ya dawo bayan kusan awa daya,kai tsaye lecture hall din da Sumayya ta fada ya nufa,ya tadda suna lecture ga wasu dalibai a waje da alama hana su shiga aka yi. Hunnun sa ruke da yar leda ya ja gefe ya jingina,Moh da ba ya jira, ko uban cikinsa baya jira bare wani lecture, yau sai gashi shi ne da jiran Sumayya har awa daya,amma shiru ba su fito ba,gashi Dad na jiran sa,haka su Son da ya bari can. Ya fara gajiya,sai kai kawo ya ke ya na duba agogo,lecture din 2hours amma har an dora minti ishirin a kai,sai a sannan idea din ya leka ajin ya zo ma sa,ko da ya leka su ka hada ido da malamin kai tsaye ya zagaya ya sa kai cikin lecture hall din,ajin yayi tsit kowa ya zubowa Moh na mujiya,ita ko Sumayya gaban ta ne ya fadi,ta fara karanto adduoi.
Ya na wannan tafiyar ta sa ta isa,hannu daya cikin aljihun wandan sa,dayan ruke da yar leda,ya haura kan stage wajan da lecturer ya ke,tin kan ya karasa gare shi Malamin ya ce ta yaya zan iya taimakon ka? Moh ya ce Mallam kaya na ne ajin ka....Malamin ya gyada kai tare da fadin dau kayan ka ka tafi kar ka daukewa dalibai na hankali. Moh ya ce sako zan ba ta Malam,ba daukan ta zan yi ba.....cike da mamaki, malamin yace za ka ba tafa ka ce?ya gyada kai wacece kayan ta ka?idanun sa ne su ka sauka kan dalibai da alama ita ya ke nema. Sumayya ta durkusar da kai,yau ta yi dana sanin zaman gaba a rayuwar ta,ji ta ke kamar ta kutsa cikin dalibai ta buya. Ai kuwa idanun sa ya sauka kan ta lokaci guda sunan ta ya fita daga bakin sa,Sumayya......Malam ya ce wace Sumayya?who is Sumayya?wanda su ka san ta su ka juyo su na kallan ta,da kyar ta iya tashi tsaya,ganin yanayin fuskar malamin mai wuyar fahimta ya sa ta sunkuyar da kai,Mallam ya ce ga ta nan,ja kayan ta ka ku bar min aji,na sallame ta....kirjin Sumayya ke dukan uku uku,shikenan yau ya ja ma ta,mallam ya sallame ta me hakan ya ke nufi,abun da ya kara kular da ita shi ne ganin Moh ya murmusa tare da gyada kai hankali kwance ya juya ya na fita,maimakon ya tsaya ya rokar ma ta Mallam,ta tsaya sororo idanun ta kan sa,Mallam ya ce Hajiya ki na bata mana lokaci fita ki same shi kya fi kallan sa da kyau.....yan aji aka sa dariya,idanu cike da kwalla ta hade littafin ta ta kama hanyar fita ta na jan takalmin ta,sam ba ta gane komai,maganar Abbu ke yawo a kwakwalwar ta "Sumayya ki dage ki yi karatu,shi ya kai ki makaranta,ban da abun da zan iya baki a matsayi na na mahaifinki da ya wuce ilimi,ban da arziki ban da komai,ki yi karatu ki sami ilimi shi ne arzikin da ni mahaifinki na baki...kar ki yarda wani abu ya taba karatun ki bare rudu irin na jami'a......."
HASKEN IDANIYA
parts 32
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Ta na jin hayaniyar yan aji,da muryar Mallam ya na su yi shiru..amma ina hankalin ta ya yi gaba,zuciyar ta ta yi nauyi,Moh ya wuce gona da iri......a waje ta same shi,ya juyo zai mata magana kawai ta daga ma sa hannu tare da fadin dakata Mallam!me za ka ce min!!!!idanun ta cike da kwalla ranta idan ya yi dubu ya baci....cike da mamaki ya ke kallan ta,abun da ya ke nema daga Sumayya yau ya gani...and God....shez too beautiful....ashe haka take indan ran ta ya baci.... ashe ta na iya nuna bacin ranta,ashe za ta iya nuna bacin ta gare shi,amma abun da ya kasa ganewa shi ne me ne ya kawo bacin ran.....!?
Nan kuwa ya sami amsa dan cikin bacin rai Sumayya ke magana,idanun ta sun rufe wanda hakan da ta ke yi ja hankalin yan ajin su da ke wajan,can gefe kuma su Shamo ne da zuwan su wajan kenan sun ji Moh shiru...Sumayya ta ci gaba da fadin KA TAKURA MIN!KA MATSAMIN KA ISHE NI!!!rayuwar ka da tawa ba iri daya ba ne,ni talaka ce,am jst tryn to make my lyf worth living!!!!idan kai you ar born with a silver spoon,ka saba taka kowa hankalin ka kwance ni so na ke na tsira da rayuwa ta,ina zuwa makaranta ne ba dan na yi having fun ba,da dan haka ne da ba ka ganni a nan ba,dan na sami ilimi na tsira na ke zuwa makaranta...na san darajar malamai na,ka iya yin komai,(ta hade hannayen ta biyu)....amma dan Allah kar ka bata min suna wajan malamai na,dan Allah ka fita daga rayuwa ta.......
Mike,James,Shamo da Son mamaki ne ya cika su,suna jira su ga Moh ya dauki mataki mai girma dan kuwa yau Sumayya ta yi abun da ba su taba gani ba a tarihin rayuwar su,,wai mace talaka ke mishi masifa.....haka sauran jama'ar gun. Moh kuwa duk da maganganun Sumayya sun soke shi kamar kibiya,amma ta burge shi kwarai,alas!Sumayyar ba sokuwa bace all in all. Ga mamakin kowa,Moh ya murmusa,murmushin da su Shamo ba su taba ganin ya yi irin sa ba,ya aje ma Sumayya ledar da ke hannun sa gaban ta tare da fadin ina fatan za su mi ki tin da daka na yi.....wayarshice take qara ya dauko ,wayar shi yakara ya daga ya na am so sorry dad,ka yi hakuri wani uziri ya tsaida ni.....ya ma su Shamo alama da hannu,na su tafi,ya wuce gaba ya na wannan tafiyar ta sa waya a kunnan sa,Su Shamo su ka rufa ma sa baya cike da mamaki, da haushinsa,haka ma idanun Sumayya,da ta fara saukowa,jiki ya fara sanyi.
Jama'ar gun sai kuskus su ke,yau Sumayya ta yi abun fada,gaba daya ta rasa me ke ma ta dadi,ganin Mallam ya fito ta yunkura za ta bi bayan sa,wata ta ce kin manta ledar ki baiwar Allah!daukar ledar da Moh ya aje ma ta tayi,ba tare da ta ma sani ba,ta bi bayan Mallam da sauri duk da tsinkewar takalmin na ta.
Cikin office ta tadda Mallam,ya zauna kenan ta yi sallama,ya daga ido ya kalle ta tare da amsa sallamar,ganin ta ya ce ai ke ce ashe,kayan Muhammad, gaban ta ya dada faduwa,ya ma san sunan sa kenan,ta sunkuyar da kai ta ce dan Allah Mallam ka yi hakuri,ka janye sallama ta da ka yi,wlh ba ruwana da,dan Allah Mallam. Cike da mamaki ya ke kallan ta,ya ce ke ai ba wai na sallame ki baki daya ba ne,shi Muhammad din ai tsokana ce ta sa har ya iya shigowa ya same ni,abokin wasa na ne fa....taubashi(cousin)na ne...dan mamaki ba ta san sanda ledar hannun ta ya subuce ya fadi kasa ba,abun da ke ciki ya fado.....ta bishi da kallo yayin da idanun ta ya sauka kan wasu takalma silver colour ma su bala'in kyau da tsada......wayyo Allah na abun da ta fada kenan jin yanda danasani ya lullube ta......
No comments:
Post a Comment