Pages

12 Jun 2016

AURE KO ZAMAN GIDA? 1 - 2

AURE KO ZAMAN GIDA? 




 AURE KO ZAMAN GIDA?

•••••••PART 1••••••••

 HAUWA M.JABO

akan hanyar asibiti nida qawata zeenah khalifa

zamuje duba wata maqociyarmu da batada
lafiya,Muna shiga asibiti mukayi karo da wata mata
da yara guda biyu a hannunta zenah khalifa tayi
sokoko tana kallonta.Ke zeenah khalifa kinji haushi
ki kalli maza ki kalli mata.! Banason wulaqanci
hauwa jabo.! Mikike nufi da inkalli mata in kalli
maza? kamar wata bunsura..!!! Na kwashe dadariya
nace yanzu dai yimin bayani mi kika hango.?? Ta
kwashe da dariya kibari kawai,Hauwa jabo matar
nan ta hadu billahillazi..Da ace ba baqa bace sai ince
wllhy ba indiyace keni muje muyi qawance da ita,Ke
zainab muna fama da talaucinmu zamuje gurin
masu kudi.? Bazanje a wulaqantaniba gaskiya,Ke
Hauwa jabo wllhy kin cika tsoro,Idan bazakiba bari
inje ingabatarda kaina,Ta kwace wayata taje tana
kuri. Bansan yanda sukayiba naga har sunyi
musanyar number suna yiwa juna murmushi wani
namiji yazo naga yana mata magana tay murmushi
ya rungumeta hannunsa dayan hannunsa riqe da
handbag dinta ya mata kiss a kumatu ina tsaye ina
kallo araina nace dama matan nigeria suna
soyayyah haka? In shot sun burgeni kuma inason
inji tarihinsu da inda suka iya soyayyah irinta Iranian
saboda Iranian ne kawai zakiga sundaukarwa
matansu jaka su rungume jariri kuma su rungume
matar kamar wani zai kwace musu.. !Zainb ta dawo
sai murna takeyi ina tsaye,Sai wangale baki takeyi
zainab,Amma fa matar ta haduko H jabo? uhun ba
laifi!, Ke Wllhy kincika matsala,! Nidai muje, Zamu
shiga kenan sai gasu sun fito suna dagawa zainab
hannu sai wangale baki take har yar wushiryarta da
dan dimple dinda take kuri dashi ya fito araina nace
zainb ansamu aikin yi, Munshiga mun duba mara
lafiya munfito muka wuce city plaza muka dan sayi
ice cream muka samu keke npn sai gida.....

Eshqi mano too... tuye qalbam mimune....zandagi
batu behtare..... Ringtone din zainb kenan kuma
gashi tashiga wanka naga anrubuta sister zainb
araina nace waye kuma sister zainb... hello, hello
namesake, nasissim adaya banqaren naji dafada
cike da dariya... Araina nace wannan yar turkiyace
ni jabo ba Turkish na iyaba hakadai na amsa mata
nasissim eyem ebit ta kwashe da dariya.. Araina
nace zatace ban iyaba na kwabsa, Sai tace ni ban
iya wannan da kika fadaba nima nay dariya, Tace
yaushe zaku zo gidana da sauri nace gobe zamuzo
ba matsala, Eh kuzo ta fada cike da shauqi, Ta bani
address dinta na rubuta zeenah khalifa na fitowa
nace namesake dinki takira tace gobe muzo...
ihuuuuuuhw.!! Wani ihu tayi tanajin dadi nima naji
dadi ko banxa inason muje inyo gulma...

Tun safe kinsan yau zamuje unguwa ko? Unguwa
kuma.? Lallai wllhy jabo kinji dadinki kin manta
zamuje gidan namesake dina.!!?? Au natuna qarfe
nawa ma zamuje.?? 12 mukace mata. Kk.. mun isa
gidanta wani qaton gidane da shuke shuke ya rufe
ko ina nace anya nanne zainb karmuje a cire mana
kai, Eh nanne mana muka danna bell maigadi yabude
mana yace su zainb ko mukace eh kushigo, Araina
nace har angayawa maigadi zamuzo Lallai anaji
damu..
Munsameta tsakiyar gida tana ganinmu tazo ta
rungume mu......

 muje zuwa muji yanda hauwa jabo
zatayo mana gulma agurin zainab......

AURE KO ZAMAN GIDA ?


•••••••PART 2••••••••

…Munci munsha mun hole anan na fahinci zainab
tanada balaeen saurin sabo kuma akwai tsiwa da
wasan rainin hankali, Nandanan muka saba da ita
amma naga tafi maida hankali gurina ko dan taga
nafi hankaline ohoo..?
Watannmu uku da sanin zainab duk ansanmu a
gidanta tana zuwa gidanmu sosai,Ranar munje
gidanta, Nan nanemi ta bamu labarinta daga farko
tayi gardama daga baya mitayi tunani ta amince
naso inyi shishigi intambayeta amma sunyi rayuwa
a iran ko amma sai nafasa nace bari in barta kawai
maji daga baya...

Tun safee nazo inji gulma nikadai nazo saboda
nasan idan nazo da zeenah khalifa to labarin
bazaimun dadiba, Nayi sa'a tagama aikinta gaskiya
zainab tanada kazar kazar batada son jiki ko kadan,
Takawomin fresh milk nashanye, Ta gyara zama ta
fara bani labari kamar haka.........

Sunana zainab Abdullahi mahaifiyata gurin hai
huwata Allah yamata cikawa, Mahaifina mutum ne
mara kulawa sosai, Sam bai damu da tarbiyarmu ba
baidamu da chin muba bai damu da shanmuba,
Gamu mu mu shida ne a gidan ni kadai nake agun
mamata data rasu sauran biyar din duk yayan
kishiyar mamanmune maza uku mata biyu,Agurin
kishiyar mamata na girma, kishiyar mamata
mutumce wacce batayi dan Allah idan kikayi mata
zata miki idan baki mataba to bazatayi mikiba,Amma
bata cutar da kai sai ka cutar da ita, Tana dauramin
tallan kayan miya ranar da nasiyar to zamuji dadi
idan kuwa yayi kwantai to bamu ba abinci sam
saboda da dan ribar da take samune take bamu
abincin safe dana rana, Nadare kuwa baba yake
bayarwa, Bata ta6a dukanaba kuma bata cika yimin
fadaba amma tanacin uban yayanta sosai nice
babba agidan, Banta6a sanin hanyar makarantar
bokoba balle ta addini har nakai shekara goma sha
daya bana karatu sai yawon talla, Ina sha'awar boko
sosai inada wata qawa wacce muke yawon talla
tare da ita amina s bawa, Ita tana dan boko ta bani
littafinta daya tafara koyamin A B C D.... Ina ganewa
sosai saboda inada hazaqa duk ranarda muka saida
kayan miya da wuri to ranar zamu zauna muyi boko
wasa wasa har nafi amina iya karatu sai tafara jin
haushi saboda musun da nake mata akan wannan
haka yake tace a'a ba haka yakeba, Haka yake
tadaina koyamin komai ataqaice duk wata takardar
qosai ta unguwarmu idan nagani sai nakaranta na
iya hada kalmomin english inkaranta amma bansan
ma'anarsuba ke intaqaita miki jabo duk wani karatun
indai karantawane ina iyayi da rubutawa.....

Akwai wata rana na fito tallan wara saboda yanzu
nadaina tallan kayan miya wara nake talla yafi
kasuwa ina tafiya naga wata qatuwar mota baqa
baka ganin waye aciki,Anyi parking dinta a gefen
hanya, Kusan wata daya Kullum sainaga motarnan
wani yaro yace wai mai motan yace ki kawo wara
na kalli motan lokacin iya tunanina nasan mai
Wannan qatuwar mota bazai ci waraba, Nace
bazanje, Shegiya matsiyaciya arziki yana kiranki
kina gudu kar kije miya dameni wannan mutumin
duka yake siya yace kikai masallaci....

No comments:

Post a Comment