ASHE KAINE MIJINA
ASHE KAINE MIJINA 67?
Na Hauwa M. Jabo.
******************
Yau nazia ta fito lecture tare da sabuwar qawarta da tayi mai hankali da natsuwa Aysha ameen sokoto wacce haifaffiyar sokoto ce yarinyar nimw kaina jabo nq yaba da natsuwarta amma najma ake kiranta dashi yarinyar akwai ilimi kamar ana mata wahayi ga natsuwa da hankali, abinda yasa tasu taxo daya da nazia kenan duk da naxia akwai tsiwa amma tadan natsu yanxu.!
Suna tafe suna tadi har suka kawo gurin cin abinci sunyi letti ba sakwara gashi ita sukeson ci sai sukace to su fita wajen makarantar su siyo a motar najma ameen aka tafi motar sukaje Dady smart anan suka yada zango sunyi sa'a akwai sakwara a gun suna ci suna tadi anan nazia take cewa taji qamshin wani turare mai tayar mata da hankali yanayinta yadan chanza amma ta fuske kada najma uwar wayo ta ganota.! sunci sun qoshi, suna dati sama sama daga sama taji muryar da ko cikin bacci ko mutuwa tayi ta dawo taji muryar zata ganeta rabonda ta ji muryar wata shida kenan.
Muryar deen dinta ne yake kiranta hulwaty!!zunbur Ta miqe cike da mamaki ta kalleshi ya chanxa gaba daya. ya tara suma a fuska sai kuma ya mata kyau! chan ta tuna da chin mutuncin da ya mata ta daure fuska Malam lafiya ?? Kawani xo ka tsayawa mutane akai.? Najma kinsan shine? Gurinki yaxone? Najma ta kurba malt ta kada kai alamar aah. Ta watsamai kallo da dara daran idonta masu rudar dashi tace to malam sai anjimako. Yaja ya tsaya yana kallon ikon Allah hulwa ce take nuna cewa bata sanshiba! Da taga ya kafe kamar an dasa ice sai ta zargu tacewa najma suje.
Suna kan hanya najma tana driving tace waye wannan mutumin na dazu?? Nima bansanshiba ta bata amsa a tsanake, Najma ta murmusa dama akwai wayo najma ko hanjin mutum tana gani! Amma acting dinki ya bayar dake naxoo, alamu sun nuna kunsan juna ! kuma kunyi kewar juna! kuma kunason juna! kuma kun tsani juna! kuma..... Is ok phycologist!@ ke haka kike kullum da fassara ni ko mai kama dashi ban taba ganiba sai yau najma ta qara murmusawa naxoo ki gaymin mana duk maganar da najma take bata kalli nazia ba tuqinta take hankali kwance, amma hajiya nazia hadda xufa dan kuwa ta rude tasan najma smart girl ce amma batayi xaton xata gane haka da sauriba. Sai ta basar da maganar. kai yaufa zamu shiga hannun Dr shu'aib kinsan bamuyi assignment dinsaba ko? Najma ta ganota sai ta shareta itama ta murmusa tace Eh yanxu muje muyi kamin mushiga lectr. ahaka har suka isa makaranta...
Naxia kam duk ta rude ganin deen tsohon abu ya dawo mata sabo, ta samu dagyar aka tashi ranar batayi bacci ba dan tunani!...
*********
Nura kuwa binsu yayi a hankali har yaga inda suka shiga.
Tun daga ranar dan fodiyyo ta zamo mishi gida har ya gano department dinsu hulwarsa.
Ranar nazia ta fito shago ta siyo musu malt najma na hall tana jiranta sai kawai tayi kichibic da nura. Tsoro ya cikata. Haba hulwa miye duniya karki manta deen dinkine masoyinki mijinki...
Ta katseshi da daga hannu, ?
That was then..! but now lost substances value & no regard before me.You are completely out of my mind, you are neither trusted nor reliable. Please find your way live me alone.!!
Bata jira amsarshiba ta qara gaba abinta malt dinda batasha ba kenan zuciyanta tana quna amma taji dadin maganganun da ta danna mai ko banxa tasan ya yaji haushi.. Najma ta kasa gane kan nazia qarshe naxia tasa kuka dagyar najma ta rarrasheta.!!
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA?? 68?
Na Hauwa M. Jabo.
Bayan tayi shiru ne take tambayarta abinda ya faru anan nazia ta baiwa najma labarin komai amma bata fadi mugun aikin da suka aikataba..
Najma ta murmusa I know that. ! Na fahimci akwai wani abu tsakaninki da wannan guy din tun ranar. na barkine kawai dan naga bakyason maganar.! Amma miye aibi tunda yayi regret ku daida kanku mana?? Kinasonsa yana sonki mistk ba wanda ya wuce yinsa inaga kawai ki haqura nazooo ku maida aurenku. Ashe kin taba aure bansaniba.!! shine idan ana zancen banana kike fuskewa kinuna mana irin u don't now everything. Kai nazoo kin burgeni u are so smart more than me wallahi nazoo tadan dara batace komaiba.!
Haka najma tayita rarrashinta tana bata haquri har tadan saki rai suka rabu akan zatayi tunanin akan shawar da najma ta bata, koda ta aminta saita walfa nura..
Nura kam yasha wulaqanci kala kala a gun nazia wanda sam baya damuwa burinsa ta amintace masa su maida aurensu. Tunda yaqara sakata a ido ya kasa sukuni da walwala kullum yana dan fodiyyo (( nidai jabo nace kawai ya nemi admtn makarantar ya fiye masa yawon hanya??)).
Wannan karon ma nura ya tare nazia tare take da najma ya mata magana kamar yanda ya saba itama ta bashi amsa kamar kullum, ta nunashi da yatsa waike wane irin mutum ne?? And I won you not get to any of my bussinees any more.It also look like you don't have human conscious & moral values. Leaves for your own interest. Ta murguda baki ta wuce abinta.
Ran najma ya bace ba kadan ba, kuma tasan duk randa nazooo taga nura tamai cin mutunci sai tayi kuka tana dana sani abinda ta aikata Najma ta kalli nura ya bala'en bata tausayi sai ta wuce su dukansu tabar nazai ita kadai tayi kukanta har ta qare ba mai rarrashi....
Ran nazia ya bace wato najma laifinta ma take gani abinda takema nurako duk zata raba jaha dasu. Gobe sai taqi xuwa makaranta wasa wasa nazia saida tayi sati daya batazo skull ba ba nuraba hatta najma hankalin su ya tashi nura yaga najma ya daure ya tambayeta tamai bayanin rashin xuwanta ya bata haquri akan kada tayi fushi da aminiyarta akanshi. yakamata ta kira taji lafiyarta tunda bata saba fashin xuwa makatantaba. ya karbi number najma akan xata sanar dashi lafiyar nazoo idan sunyi waya.
Naxai kuwa ta sharawa inna qarya da yake inna ba yar boko bace tace sun sami dan hutune. Inna tahau ta zauna.
Bayan tafiyar nura najma ta kira nazia amma taqi dauka takira yafi sau biyar amma shiru ba labari, bayan lecture ta wuce gidan su nazoo. A palo ta sameta nazia ta daure fuska najma ta kwashe da dariya taja hannunta tana kwacewa har dai suka shiga daki. Ta ijiye jaka taje ta gaida inna ta dawo ta bude fridge ta samu malt daya ta bude zatasha nazoo ta kwace daga bakinta ta harareta tace: dan uwanki nura bai siyo mikiba!!? Maganar ta baiwa najma dariya tace ya siyomin gata a jaka ba sanyine ta bude jaka ta fito da malt ta bude xatashi naxia taqara kwace wai baza'asha abin nura a gidansuba. Najma kam dariya Abin yake bata dagyar ta samu naxoo ta dan saki jiki sukayi nagana ta fahimtar juna. Ta bata shawara har cikin ranta taji dadin maganar suka shirya suka dawo kamar basune suke rigima ba nazia har tana tambayar najma da gaske shi ya siya mata malt tace wasa takeyi wallahi ita miye hadinta dashi a hanya ta siya suka tafa ta tafi.... najma ta kira nura tamai baya ni nazia lafitanta lau da sauran bayanai kuma tace zata taimaka masa. amma bata nuna mai cewa naxia ta haquraba tadaice yaci gaba da addu'a kuma yaci gaba da mata magana...
**********
Kamar kullum sun fito lecture tace a bari ta samo musu dan cake da malt susha da yake nazia mayyar malt ce ta hadu da wani course mate dinta da yake mutuwar sonta mai suna ahmad. ahmad Allah ya jarabceshi da son nazoo amma daidai da rana daya bata taba bashi fuskaba sama sama duke gaisawa yauma sun dai gaisa sai suka jera tare har shagon suka dawo. A kan hanya ya bata labarin ban dariya ta kyalkyale da daria dago kanta da zatayi sai taga deen gabansu ya daure fuska kamar ance maigari ya mutu. Keeeeee waye wannan?? Ashe bakida hankali bansaniba?? Kina da aurena akanki kike tsayawa tare da samari??
Kin manta........ shot your mouth up.! Don't ever called me matarka.! Am not & I will never be the one! So yafi kyau kasan inda dare ya maka!! Ta watsamai harara. ahmad yace malam an rasa hanyar da za'a bullone sai aka fake da cewa matanace so sai a nemi wata hanya bawannan ba. Naxoo ba tasan lokacinda ta kamo hannun ahmad ba tace muje ko baby na.!! Tuni idon nura sun rufe ya wanke nazia da wani wawan mari. Ahmad ya daga hannu zai rama mata nura ya riqe mai hannu..... Boy! Don't make the mistake of bullying me...! And for your information, you made a great mistake the other time because she's married to me, any time I sight you talking with her, you'll rest behind the bars...
Ya sakeshi da qarfi.
Auntie M. Jabo:
A SHE KAINE MIJINA 69 ?
Na hauwa m. Jabo
Ya sake mai hannu da qarfi & ka bace min da gani! ahmad yaji tsoro, ya matsa baya sai na hadaka da security wallahi ya wuce yan surutai ya juyo gun nazia. kada kiga ina nibiyarki ki nemi wulaqantani gaban mutane.! Ke har kin isa ki rqee hannun namiji a gabana wannan ya....!!
Ta kalleshi ido cike da hawaye murya na rawa ta rasa abin fada mai yaji haushi, duk fasaha ta bace mata. I definitely loved you before I know your dirty hidden color. Learn your lessons as appropriate.... I really hate you deen...!!
Ta bi ta gefensa ta wuce ya rasa abin fada waima shi da yake neman sulhu mixai kaishi marinta?? Ya dungule hannu ya daki iska ya wuce abinshi. Abin mamaki nazia sai bata fadawa najma abinda ya faruba tunda tasan batada gaskiya kuma ta mata alqawarin xata daina wulaqanta nura.!
Tana xuwa tace miya tsayar dake haka tace fada na tsaya kallo security sukazo garin gudu aka bigemin fuska. ayyah sannu.!!
************
Tun daga ranar nura bai qara xuwa makarantarsuba harkwana hudu.! Nazia tadamu tana kallon cewa abinda ta masa ne yasa yaqi dawowa gashi ba halin magana,
Naxoo xamuje gidan uncle dina na karbo saqon umma please tunda bamuda lecture sai 4.. naxoo ta aminta sukaje, a hanya najma sai danne dannen waya take a mata sms itama tayi har suka isa gidan ba kowa maigadi ya gaidasu ya basu key suka shiga najma tace ta zauna ta kawo mata lemu. Ta kawo mata lemu ta shiga wani daki ta dauko wasu ledoji ta fita tace mata idan kun shirya ki mini waya inxo mu koma skull..!! Nazia ta miqe tsaye banganeba malama mi..... ta budebaki da mamaki miya kawo nura nan gidan?? Yasa key ya kulle qofar ya maida key aljihu ya matso kusa da ita tsoro da mamaki suka kamata wato set up ne suka mata ko??
Ta rasa bakin Magana sai ta nemi guri ta zauna. Nura ya matso kusa da ita ya tsuguna yana fuskantarta qamshin turarensa ya daga mata hankali amma ta fuske.... nura ya fara bata haquri akan marin da ya mata a skull gaban saurayinta, nifaba saurayina bane! Ok. Koma miye kiyi haquri ta kawar dakai. Nura ya shiga aikin rarrashin nazai yana magana yana kuka alamu sun nuna yayi dan dana sanin abinda ya aikata. Ita dama tuni ta yafemai kodan ganin halin da ya shiga, (( kaji mace idan dai tanason namiji tsakani da Allah wallahi komai ya mata zata haqure)) batace dashi komaiba ganin ya tsananta kukanshi ne sai taga rashin dacewar haka yana namiji yaxo yana mata kuka tace shikenan ya wuce!! Ya dago jajayen idinsa ya kalleta nazai kice kin yafemin mana!! karo nafarko da ya taba kiranta da nazai saidai hulwaty....!!
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA 70?
Na Hauwa M. Jabo.
Ta kasa magana tausayinsa da tausayin kanta ya kamata ta tuna soyayar daya nuna mata amma lokaci daya ya wulaqantata har yana cemata yar iska!!!
Batasan lokacinda ta fashe da kukaba ta dora kanta akan cinyoyinta tana rera kuka.! Hankalin nura yayi matuqar tashi ganin kukan hulwarsa baisan sanda ya rungumota jikinsa ba yana rarrashi tana shaqar qamshin turarensa hankalinta yana neman gushewa a jikinta batayi qoqarin kwace kantaba taci gaba da kukanta da sauti. tana kwance a jikinta shiko yana ta rarrashinta yana bata magana yana jadda damata ya karbi kuskurenshi bazai iya rayuwa idan bataba, tana kuka tayi qasa da murya daidai kunnensa tamai magana kamar rada, deen u betrayed my life! U really hurt and harm my life because my heart insisted & become mad in your love.!! It's not an exergration that i can't do with out you. I remain yours no shacking I sincerely love you.!
Deen please kada ka qara barina please!!
Ya qara matseta a jikinsa, ya rada mata a kunne
Hulwaty..!! I can't leave you! You're my life, sight. I wholeheartedly love you. Your love is in my blood. me all my short comings, I will never repeat it again.!
Ta qara lafewa a jikinsa batace komaiba taci gaba da kukanta yana shafata yana rarrashi nidai jabo na saki baki ina kallonsu abin yana bani mamaki wai har sun shirya! dama ance tsakanin mata da miji sai Allah, da nice da ba haka kam??...
Sun fahimci junansu sun yafi junansu a hankili ta janye jikinta daga cikin nashi yace kin gaji dani ne tamai murmushin nan da yayi watanni bai ganiba ya shafa fuskarta daidai dimple dinta shima yayi murmushi. Suka share hawayen Junansu suka dan taba hira chan nazia tace: najma fa tana jiranmu, deen yace nifa har na manta da ita! Lallai deen duk taimakon da ta maka shine zaka manta da ita? Waima ya akayi kukayi wannan tunanin?? Ba ruwanki sirrine tsakaninmu.! Su rirri manya koda muka fito sai mukaga bashir da najma suna soyewa..( aruwar jabo najma da basheer suna burgeni da sunyi aure da saina rubutomuku labarinsu.)
Sannunku fa, laaaa kinga ni har na manta da ku. U see.. da deen ma yace ya manta dake! Laa hulwa banda sharri fa yaushe nace na manta da najma, ai ni banida kamar najma a fadin duniyar nan. Duk muka kwashe da dariya....
Mun koma makaranta cike da farin ciki na baiwa najma labarin abinda ya faru tanajin dadi har tana cewa yaushe zamusha biki!
************
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA 71?
NA HAUWA M JABO.
********
Wata sabuwar ssoyayyah akeyi tsakanin nura da nazia kamar ba abinda ya taba shiga tsakaninsu nima dai hauwa jabo suna burgeni kuma ina daukar darussa a love dinsu kamar su hadiye juna. Haka zaka gansu kamar wasu budurwa da saurayi, amma duk da haka naxia akwai abinda bata yi dan kawai tsare gida.!
Nura yama mai gari magana akan sun daidaita da nazia zasu maida aurensu kowa yayi farin ciki da haka bada bata lokaciba aka maida aurensu nan ma anyi sabuwar bidi'a auren ssoyayyah...!!
Daren ranar nura ya tuhumi nazia akan xubar mai da ciki da tayi kamin ta gane shine mijinta aranta tace ASHE KAIE MIJINA bansaniba.!! sabida haka yau sai ya tabbatar da cewa ya sami wani yaron. bata bashi amsaba dan tasan bata zubar da cikin ba tayi niyya sai Allah yayi nasa ikonn. sai bayan sati daya tace ya rakata asibiti yana mamakin mi ya sameta tace sudaije a sibiti takaishi gun Dr da ya dubata anan Dr yama nura bayanin cewa ba zubar da cikin akayiba zubewa yayi da kanshi sanadiyar damuwa da tashiga da kuma rashin lafiyar yaron kuma ya gaya musu dagyar ma idan xata qara samun ciki hankalin nura ya tashi dajin haka Dr ya kwantar mai da hankali da cewa akwai magungunan da takesha tana qarewa zata warke zata samu ciki. Haka kuwa akayi nazia tun daren farko data koma samu wani cikin. Soyayyah suke kamar su hade juna suna girmama juna.!!
Sun shiryaa da sister khadee amaryar ammar, kamar basu ba haka qawancen su da najma sai abinda ya qaru dan nazia nason najma. dan itace sanadin maido mata da farin cikin ta, so tana mata fatan samun yaya bashir dinta. zainb khalifa kuwa uwar kuri da iyayi kullum tana min waya ya baby irin dai ana neman gindin zama gun nazia wai ita dangin miji....
***********
Naxaia da nuraddden kullum cikin farin ciki suke Cikin ikon Nazia ta haifi yayanta uku duk maza AHMAD HAMEED MAHMOUD. yayan abin son kowa kyawaonsu ma ya wuce misali nima jabo nayi kamen daya da yata dazan haifa idan nayi aure.. ummulkhairi qarin jini ma tayi kamun daya da yarta mai shan nono.....
Tammat bi hamdillah.
-----------------------
Ina godiya ga dinbin masoyana masu bibiyar books dina da masu kirana a waya da masu mini magana a whtassapp duk ina godiya da qauna da kuka nuna min nagode....
Duk da tsaikon da aka samu na rashin kammala littafin da wuri ina dada baku haquri.. kuma kuyi haquri da hausar tawa sai a slow. sai mun hadu a wani book nan gaba mai suna...........WACE CE ITA.
ASHE KAINE MIJINA
ASHE KAINE MIJINA
ASHE KAINE MIJINA
No comments:
Post a Comment