Pages

22 Aug 2016

IDAN ZUCIYA TA GYARU THE END

IDAN ZUCIYA TA GYARU 
 By yasima Suleiman




IDAN ZUCIYA TA GYARU


THE END

****************


Iyayansa da kansu sun lura da halin da ya shiga don haka sun dukufa gurin yi masa addu'a da sanyawa ana masa sauka. Yau kam ya dira a cikin gidan nasu, Suna soro da Zaid bisa tabarma suna karatun Sahihul Bukhari yana mata kari ya shigo da sallamarsa, suka yi kallon kallo da Zaid sannan suka gaisa Zaid ya hade littafansa yana fadin, "Zainabu bari naje na dawo, daman na gaya miki ina da Interview da azahar, zan shigo da dare." Ta bishi da kallo tana fadin, "To sai ka dawo." Sannan ta maida kallonta ga Mustafa dake tsaye hannuwa zube cikin aljihu ya sha kunu matuka, ta yi murmushi sannan ta ce, "Bawan Allah ka zauna mana, irin wannan kumburi haka kamar zaka rufeni da duka." Ya yi kwafa sannan ya zauna yana fadin, "Rainin hankalin naki ne naga yana neman wuce gona da iri, yanzu haka ina ofis a zaune na gaza tsinana komai saboda rashin sanin matsayina a gurinki kullum raina yana cikin fargaba da dar-dar, an ya Zainabu duniya da gaskiya za ki so wani da raina da lafiyata?" Ta dan yi murmushi gami da gyara hijab dinta ta ce, "Malam Mustafa kenan, nice da baki na na gaya maka ina son wani ko gaya maka aka yi?to sai an gaya mini? ai duk wanda ya ga yanda kuke da Zaid ya san kina son sa, don wata gulma wai karatu yake koya miki kullum yana manne da ke, duk makarantun garin nan basu yi miki ba sai nashi karatun eye, ni kam na gaji da ganin wannan abu ki sanar da ni matsayina a gurinki kawai Zainabu." Ta yi jim sannan ta ce, "Mustafa ai kafi kowa sanin matsayinka a gurina ko na fada ko ban fada ba duniya ta shaida irin son da nake maka, kuma wallahi har abada ina sonka, sai dai duk son da nake maka kayi mini nisa ka haramta a gareni dole na hakura da kai, dole na yi amfani da karin maganar hausawa da suka ce 'idan so cuta ne hakuri magani ne', domin wallahi ba zan kuma yadda na sabawa Allah da gangan ba, zuciyata ta gyaru don haka ina son duk kan mu'amalata da aiyuka na suma su zama gyararru." Jikinsa yayi sanyi idanuwansa suka sauya launi ya ce,

 "To Zainabu baki ganin muna da sauran dama, ina ce kwanaki mun yi maganar auran kisan wuta da zaki yi sai mu mai da auranmu? Amman muddin kika auri Zaidu nasan na rasaki har abada domin wallahi ina ganin irin son da yake miki cikin kwayar idonsa, ki taimake ni Zainabu kece ruhina don Allah." Idanuwanta suka ciko da kwalla sai taji wani son Mustafa ya kuma taso mata, sai dai tsoron Allah yayi tasiri a zuciyarta matuka don haka ta ce, "Mustafa muji tsoron Allah mu daina tsarawa kanmu rayuwa bama tuno da mutuwa, yanzu ka duba ina Sala take, wane irin buri ne bata ci ba a rayuwarta, shin buri nawa ta sami damar cikawa? babu ko daya, don haka ka sanya a ranka ko yau ko gobe ko yanzu zaka iya amsa kiran Allah, don haka ni kam bazan boye maka komai ba na yanke shawarar zan auri Zaid aure na tsakani da Allah, ba zanyi aure da niyyar na fito ba, sai dai idan Allah ne ya kaddara mini, idan Allah yayi da rabon zama a tsakaninmu zamu sake yi a gaba idan kuma babu mu godewa Allah da duk yanda ya tsara mana, amman ni kam babu batun auran kisan wuta a gabana, kai ma ina so kaji tsoron Allah Mustafa.....kuka ya ci karfinta saboda yanda zuciyarta ke tafasa da son Mustafa, ji take kamar ta kwanta a jikinsa taji sanyi, amman ina yayi mata nisa har abada domin dai tana rokon Allah ya sanya mutuwa ce zata raba ta da Zaid. Kamar zai kuma cewa wani abu amman sai ya kasa kawai ya mike a zuciye ransa yana tukuki ya fice. Ta mike ta bishi da sauri don kada ya yiwa kansa illa ta taddashi har ya shiga motar ta leka kanta ta windo ta ce, "Mustafa ka tuna kai musulmi ne cikakke, kuma imaninka ba zai cika ba sai ka yadda da kaddara, lallai rabuwarmu muna son juna tana cikin kaddarar da Allah ya shirya mana, kayi imani ka amsheta hannu biyu, ka kula da kanka kada kayi tukin ganganci, kayi ta zikiri ga Allah zaka samu sauki da rangwame a zuciyarka." Ya kura mata ido ganin yanda hawaye ke malala a kuncinta ya sanyaya masa jikinsa, ya tabbatar Zainabu na son sa sai dai kaddarar zata raba su kamar yanda ta ce, yayi kokarin kakalo murmushi yana fadin "Na gode Zainabu zan dawo wani lokacin amman ina ji a jikina yau ce rabuwarmu ta karshe ko na mutu ko kuma na rasaki har abada, zan rungumi Zainab da Zainabu ne sune zasu maye mini gurbinki, Insha Allah zan zama mai kokarin juriya da rashinki, ina fatan zaki yafe mini duk wani laifi dana taba yi miki a rayuwarki.

 *********************


inna fatan kasancewa cikin afuwarku sakamakon rasa shafuka kusan 3ko4,saidai fatan ga masu littafin a hannu zasu taimakamin dashi, page 163-166...Pls me shi ya tsimakamin..zamu dora domin nasan zaku fahimta. Ta san me ake ciki ba, ta yi dan murmushi tana goge idanuwanta da suka ciko da hawaye don tana son taga ya koma cikin nutsuwarsa ya manta da Zainabu ya so ta ko da rabin na Zainabun ne. Ya karanto abinda ke ranta don haka ya kai hannunsa yana goge mata idonta yana fadin, "Ki daina kuka Zainab ki taya ni da addu'a kinji itace magani, amman ke din kin yi mini duk wani abu na kyautatawa don haka ki kwantar da hankalinki bani da kamarki yanzu Zainab." Wani irin dadi ya kamata har bata san sanda ta ce masa "Yanzu kana nufin kana so na kamar Zainabu kuma ka cire ta daga ranka kenan?" Ya yi murmushi mai ciwo sannan ya ce "Ki bar wannan magana Zainab duk son da nakewa Zainabu ai ya tashi banza tunda dai a yanzu kece matata kece mai faranta mini rai, don haka zanyi kokarin ganin na manta da komai na Zainabu amman sai da taimakonki da soyayyarki, son Zainabu zai zama tarihi na sani." Kukan dadi ya kwace mata ta kifa kanta bisa kirjinsa tana kuka tana goga kanta, ya dinga lallashinta yana gaya mata kalamai masu dadi a cikin kunnenta har bacci ya daukesu. Kwanansu tara da tarewa Zainabu ta matsa masa da lallai sai ya dauko mata 'ya'yanta, don daman tana son yaran gasu da kyau ga biyayya musamman Shahid da yafi son mutane ko don ya fi su wayo ne, shi kam sai dagewa yake yi don Zainabu ta karantar dashi soyayya mai wuyar mantawa, sai yanzu ya gano abinda ya sanya Mustafa da duk wanda ya taba mu'amala da ita ya nace mata, ba ta da lokacin komai sai na gyaran kanta da faranta masa, har tsokanarshi abokansa ke yi wai ya fara timbi da naman wuya, amman dai bai son abinda zai taba masa ranta don haka ya dauko su. Sai dai Shahid da Sudais bangaransu daban ne don su maza ne gashi sun fara girma, don Shahid yana shekara ta sha biyu kenan, Sudais yana ta tara, sai Ummul-Khair da take shekara ta biyar. Yaran suna da tarbiyya mai kyau don haka Zainabu ta rike su da amana da tattali sai sannan suka fara mantawa da maraicin Mahaifiyarsu don suna ganin kamar ta dawo ne, domin babu wanda zai ce Zainabu ba itace ta haife su ba. Shekara guda da yin auran amman Zainabu ko batan wata, hakan ya fara damun Ustaz Zaid don haka ya ce ko zasu je a dubasu, ita kam daman ta fidda rai da haihuwa amman don kada ya ga kamar bata damu ba ya sanya tace su je din. Daga Nigeria har kasashen larabawa da suka je sunyi iyakacin bincikensu sun kuma tabbatar da Mahaifar Zainabu ta sami matsala saboda shan kwayoyin hana daukar ciki da ta jima tana yi gashi kuma ta taba samun ciwo daman sanda aka yi mata abortion don haka sai dai hakuri kawai babu batun haihuwa a gareta har abada. Ta shiga tashin hankali matuka har ta gaza sukuni da walwala, sai dai Zaid ya fara karanto mata Hadisai da ayoyin Kur'ani na masu hakuri da dangana da irin romon rahamar da suke samu sannan ta nutsu, sannan ya ce, "Ki dubi Sayyada A'isha da irin soyayyar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yayi mata, amman har ta koma ga Allah bata taba haihuwa ba, don haka ki yiwa Allah godiya a duk yanda ya barki." Ta kuma yiwa Allah godiya ta yadda bata da 'ya'yan da suka wuce su Shahid domin Zaid bai nuna mata ba ita ce ta haife su ba komai zai musu sai ya shawarce ta, su kuma sun zama 'yan gatanta ta babu kamar Umma ma da kullum tana manne da ita, Zainabu kam ta sami rayuwa mai kyau da albarka karatunta na addini na habaka matuka har tana koyar da Ummul Khairi ma, su Sadiku ma sun samu nutsuwa da kwanciyar hankali, bashi da abokiyar shawara da ta wuce Zainabu ta zama babbar mace mai fada a gurin mijinta da danginsa. Shi kam Baba Abbakar da kyar suka samu yayi aure wata bazawara ce da mijinta ya mutu ya aura, sai suka bude masa dan shagon saida kayan masarufi a kofar gidansu, sannan kannensu ma da taimakon Malam aka kaisu makarantar addini ta kwana, duk da sun fara girma amman da yake ayar Allah suke sha sai gashi sun nutsu Lubabatu ma tayi auranta sun sha shagali matuka.

 BAYAN SHEKARA BAKWAI

***

 Zainab tana zaune a falo tana baiwa sabon yaronta madara, yaron dake musu ban ruwa wani almajiri ne da suka shaku wanda bai wuce shekaru sha bakwai ba ya shigo falon da sallama. Ta ce, "Yauwa Balarabe daman zanje babban gida ne dubo jikin Momi gashi direba baya nan shine nace kaje ka dauko Zainabu daga makaranta, Inna Ade (Mai aikinsu) zata shirya ta sai ka kaita Islamiyyar idan na dawo zan biya can na daukota." Da ladabi ya ce, "Shi kenan Hajiya." Ta mika masa kudin mota ya karba sannan yayi mata sallama ya fice, ta mike da sauri itama don yau har murna take zata fita domin Mustafa kam akwai shegen kullen tsiya. Karfe uku suka shigo gidan da Balarabe da ya goyota akan dan acaba, ta shige cikin gida shi kuma ya kama aikinsa, can ta fito da sauri tana fadin, "Kai Balarabe Inna din fa bata nan, babu kowa a gidan har Momin ma, ka zo kayi mini wanka kada na makara Makarantar Islamiyya." Ya yi dan jim can sai ya tuno sanda zai tafi daukota Inna Ade ta fito a gigice don anyi mata waya danta mota ta kade shi autanta, kuma idan bai shirya Zainabu ta tafi makaranta ba lallai Hajiya zata yi masa fada, don haka ya ce muje na shiryaki. Ta dakko kayanta na makaranta ta ajiye a falo ya debo ruwa a kicin zai mata a 'yar harabar falon nasu, ya sanyata ta debo duk kayan kwalliyar da komai. Ya dara yi mata wankan yayin da take tube jikinta mai taushi ne da sulbi, domin irin yaran nan ne masu 'yar kiba gwanin sha'awa, don idan kaga yanayin jikinta zaka yi zaton ta kai shekara goma, ga shegen wayo da kyau, a hankali Shaidan ya fara kitsa masa wani abu a kan 'yar ficiciyar yarinyar da bata san wacece ita ba, ya dauki yarinyar cak ya shiga da ita cikin falon, ta fara fadin "Kai Balarabe yaya baka gama mini wankan ba zaka shafa min mai, kuma har da kumfa fa a jikina." Shi dai bai ce koma ba sai da ya sadata da kujera ya kwantar da ita ya fara sabule wandonsa, sam yarinyar bata san me zai aikata mata ba don haka ta kama masifa har da mikewarta amman sai ya maidata ya haye kanta. Wata irin azaba da masifa yarinyar Zainabu ta fara ji, wani irin abu mara fasali, ta kama zunduma ihu kamar ranta zai fita amman babu mai ji saboda girman gidan nasu. Mustafa ya shigo gidan don zai dauki wasu kaya sai dai tun da ya doso yake jiyo ihun Zainabu, nan da nan ransa ya baci don ya zaci Mamanta ke dukan ta sam ya manta ta fita domin dai yafi kowa son Zainabunsa.

 Sai dai me katon Allah ya gani bisa 'yar ficiciyar diyarsa kamar ya sani katuwar budurwa, ya fasa kara gami da nufarsa a gigce kamar zaki, shi kuwa Balarabe bai san ma abinda ke faruwa ba don hankalinsa yayi gaba, sai dai ya ji saukar naushi a fuskarsa sannan ya ankara,nan fa jikinsa ya fara kyarma, Mustafa kuwa ya hau dukansa babu ji babu gani, Ihunsa ne ya jawo hankalin direba da ya dawo daga cefane da maigadi suka yo gurin. Abin ya basu tsoro da mamaki ganin Mustfa yana kuka yana dukan Balarabe, can suka ji yana fadin, "Dan ubanka me zaka ji a jikin wannan 'yar karamar yarinyar, kaje ka nemi manyan mata mana, wallahi sai na kashe ka yau, wato duk gadin da nake yi na diyata sai da ka lalata mini ita ko." Sai a sannnan suka fahimci abinda ke faruwa suka fara salati da tafa hannuwa, sai da suka ga yana neman kashe Balarabe ne sannan suka kwace shi don kada ya yi kisa, da kyar suka lallaba shi suka bashi hakuri. Balarabe kuwa sai jan ciki yake yi domin duk ya karya masa kafafuwa, yana komawa daki ya fara nemo layin 'yan sanda sannan ya isa ga diyarsa wacce ke kuka ta kasa tashi, ya dauko tawul ya lullubeta yana kuka da idonsa, yau me zai gani wai 'yar Zainabunsa 'yar ficika aka yiwa wannan yankan kaunar. Shigowar 'yan sanda ne ya sanya ya daina kukan ya yi musu bayanin abinda ke faruwa, suka kwashi Balarabe aka yi asibiti da shi shi ma ya dauki diyarsa ya nufi asibiti da ita. Nan da nan kuwa aka karbeta domin dai kowa ya tausayawa yarinyar, sai dai Allah ya taimaketa bai samu damar shigarta gaba daya ba, 

yana kokarin shiga ne Babanta ya isa, sai dai duk da haka sai anyi mata dinki sannan aka bata kwanciya don sai ta cigaba da shan magani. Sai da ta sami bacci sannan ya kirawo Momi da Dadinsa yana sanar da su abinda ya faru, Hajiya Kubra kam sai taji har ta warke ma nan da nan sai gasu sun cika asibitn makil kowa kuka yake yi, karma Hajiya Kubra da Zainab da Sumayya suji labari, Alhaji Abdullahi ne ke rarrashinsu da kwantar musu da hankali aka samu suna yi dan shiru. Zainabu ta yi parking din motarta ta fito tana tafe a hankali da atamfa super yellow shar da ita sai dai ta sanya hijab dogo har iyakacin gwiwarta, tana tafe da samarinta da 'yar budurwarta dauke da kayan abinci, sai taga kamar Sumayya ke tahowa ta nufosu, suna haduwa kowa ya tsaya cike da mamaki da al'ajabi. Sumayya ce ta fara cewa, "La! Anti Zainabu ke ce, ashe kina nan daman?" Zainabu ta yi murmushi sannan ta ce, "Ina nan Sumayya ai kune ba ku da kirki ko ziyartar mutane baku yi, waye bashi da lafiya?" Idon Sumayya ya ciko da hawaye da kyar ta iya sanar da Zainabu abinda ya faru. Zainabu ta shiga tashin hankali matuka ta ma manta da abinda ya kawo ta asibitin, ta bi Sumayya suka nufi inda aka kwantar da Zainabun, ta gaisa da kowa a mutane sannan ta isa ga yarinyar wacce yau ne ganinta da ita na farko tun bayan rabuwarta da Mahaifinta, wani irin tausayi da tashin hankali ya shige ta, idanuwanta suka fara zubarda hawaye ta dafa kan yarinyar tana shafawa a hankali sai take jin kamar jininta ce, kamannin Mustafa ne a jikin yarinyar, ta jima a gurin a gurin su. Mustafa kam duk ya wani susuce ji yake kamar Zainabu ta dawo masa dole dai sai barin dakin yayi, Hajiya Kubra ta yaba da Zainabu yanzu sai taji kunyarta ta kamata, balle 'yan kyawawan 'ya'yan da take tafe dasu masu kyau da hankali, ta jima a gurinsu sannan ta nufi gurin Asma wacce tsautsayi ya hau kanta, domin garin tafiya yawon kwanan gidanta ta hadu da wani mai kudi ya dauketa tana murna don tana ganin zata yi samu sai dai da suka je gidan nasa sai ga wani katon mutum ya fito daga wani dakin tana ji tana gani suka kwantar da ita suka yanki nononta guda daya, bata dai farka ba sai a gadon asibiti, shine da ta dan fara dawowa hayyacinta aka ce ta fadi inda 'yan uwanta suke ta fadi Zainabu, domin dai da kunya ta ambaci Iyayanta dake garin Zamfara wadanda ta gudowa don zasu yi mata auran dole ta fada karuwanci, inda a nan ne suka hadu da Zainabu a wani club, sai dai ta sami kudi a karuwanci don gidan da take, amman yanzu sun zama mara amfani a gurinta domin ta lafiyarta take yi yanzu.

 Sanda su Zainabu suka isa asibitin sun tausayawa Asma don ciwon bana wasa ba ne, su suka cigaba da jinyarta anan sai dai daga karshe an gano ashe tana da cancer ma ta nono don haka dole su Zainabu suka sauya mata asibiti zuwa na Malam suka cigaba da dawainiya da ita. Alhaji Abdullahi ya zauna da Mustafa yana kuma yi masa nasiha yana fadin, "Ka ga dai yanda Allah yayi da diyarka, na san kuma abinda ka aikata ga diyan wasu ne kana gani ka yi wayo ka na mata addu'ar kariyar zina a farjinta tun tana karama sai gashi Allah ya nuna maka karshen wayonka, ya amshi addu'arka amman kuma magana ta tabbata a kanka duk wanda yayi zina da diyar wani sai anyi da tasa, sai dai taka fyade aka yi mata bada kanta tayi ba tana so, sai ka cigaba da neman yafiyar Allah da kariyarsa." Ko ba a gaya masa ba shi da kansa ya san duka abinda Babansa ya fadi gaskiya ne, don haka zai nemi yafiyar Zainabu don ya sain itace wacce ya lalata da kuruciyarta. Asma kam da taga jikin nata ya matsa babu alamun sauki ta ce ita dai su taimake ta su kaita ta nemi yafiya ga iyayanta don ta san abu mawuyaci ne ta tashi, don ance daya nonon nata ma ya harbu sai an yanke ta ce a barshi kawai lokaci ne ya yi, ana kokarin daukarta a sanya a mota ne kuma ambulance ta fara kuka da kokarin fita, Hajiya Saratu tana ta kuka da burari, Zainabu ta tsaya tana kallonta cike da tausayi domin ta san Zubaida ta cika kenan, don rannan suka hadu da Sumayya lokacin an sallami Zainabu ta warke ta ce Zubaida kuma aka kawo jikin yaki dadi ta jima tana jinya. Sanda suka isa dakin ta gane abinda ke damunta, domin tun daga farkon gurin ta gane don sambal na kunguyoyin da ke basu taimako don haka ko babu tambaya ta san ciwon kanjamau ne ga Zubaida, shi kenan dai duniyar mutum yayi ta daukarta da zafi kamar ba zai koma ba. Sanda suka isa garin su Asma kam iyayanta cewa suka yi ba zasu karbe ta ba sam, ai su tuni sun sallamawa duniya. Da yake Zaid yana da ilimi da kalami mai kyau ya dinga gaya musu fadin Allah da na Ma'aiki har dai suka hakura suka ce sun yafe mata, tana kuka tana godiya ga su Zainabu da Zaid din, daga karshe dai anan suka kwana rabon za'a yi a gabansu don asubar fari itama Asma ta ce ga garinki nan, ta amsa kiran Allah. Zainabu ta yi kuka matuka ji take yi kamar wata 'yar uwarta ta jini ce ta mutu, domin shakuwarta da Asma ko da Karimatu ba suyi haka ba, Zaid ya dinga lallashinta da kyar ta yi shiru, sai ta kuma tsinkewa da lamarin duniya ta tabbatar lallai ita din abace mara amana. Sai da aka yi sadakar uku sannan suka juyo Kano cike da kewar Asma da tsananin addu'a a gareta 

*********************

Yana zaune a gabanta ya wani shagwargwabe kamar zai yi kuka yana fadin, "Umma ke ce kadai kika rage da zaki sanya Baba ya amince ya fasa auran nan, wallahi ina da wacce nake so ba wai naki zabinsa ba ne, ga yarinyar tana sona matuka duk (family) danginsu kowa ya sanni musamman kakarta da na zama dan gida a gurinta." Zainabu ta yi dariya ta ce, "Kai yarona wannan budurwa ta tafi da hankalinka shekara nawa kenan kana ta nanata zancanta zan so na ganta,da sauri ya zaro wayarsa ya nuna mata yana fadin, "Kin ganta Momi don Allah bata yi ba?" Ta amshi wayar tana dubawa, gabanta ya yanke ya fadi domin dai kamannin Mustafa ta gani sak babu ko tantama diyar Mustafa ce, ta ji wani abu yana dawo mata amman don ta kara tabbatarwa ta sanya ta ce, "Wannan kuma a ina take yarona yaya kuma sunanta...Yayi dariya yana sosa keya ya ce, "Ummana ai takwararki ce, jikar kwanishinar ilimi ta yanzu Hajiya Kubra Abdullahi, sunan Mahaifinta Alhaji Mustafa yana aiki a kamfanin NNPC dake kano Hotoro depot, mun hadu da ita sanda na koma karatun digiri na biyu a BUk, irin kamun kanta da tarbiyyarta ya sanya naji ina sonta wallahi Umman mu." Zainabu ta yi dan yake ta ce, "Na san Zainabu, amman in dai da yawuna ne ba zaka aureta ba domin ba cikakkiyar budurwa ba ce, amman idan kaje ka tambayeta ka ji." Gabansa ya yanke ya fadi ya dinga jin wani iri a ransa kamar ya sanya hannu bisa kansa ya kama kwala ihu, sai yake ganin kamar da gangan Umman sa ke fadin Zainabunsa ba cikakkiyar mace bace, amma dai ya gaza yi mata musu ya tabbatar dai ya rasa ta din kenan, don daman ita ce kadai zata shawo masa kan baban nasa, haka ya tashi jikinsa babu laka sai gumi yake yi. Ta bishi da kallo cike da tausayi sai dai dole yau ta rama abinda Hajiya Kubra tayi mata ko don ta huce abinda itama ta yi mata. Sanda ya isa ya tambayi Zainabu maganar da Mamanshi ta fadi suma ne kawai bata yi ba domin dai ta boye wannan magana don tana ganin sirrin ta ne sai gashi yau asirinta ya tonu, sai kawai ta kama kuka ta gaza cewa komai. Hakan ya tabbatarwa da Shahid gaskiyar maganar ransa ya sosu ya ce, "Amman kin ji kunya Zainabu (Yau babu Momin tawa)." Ya dora da cewar "Yanda nake zatonki ashe ba haka kike ba, gwara da Allah ya sanya na fahimta don haka duk son da nake miki na hakura da ke." Daga nan kawai sai ya fice daga falon a zuciye, ta bishi da sauri tana kiran sa amman ko waigowa baiyi ba ya fice daga gidan a guje kamar wanda aka koro. Zainabu ta yanke jiki ta fadi anan kofar falon, Maigadi ne ya hangota ya taho a guje yana salati sannan ya sanar da 'yan gidansu. Gaba daya kowa ya rude aka kwasheta aka yi asibiti, an samu ta farfado amman da kuka ta farka, hankalin Mustafa ya tashi matuka ya zauna gefenta yana fadin, "Haba my daughter ki sanar dani abinda aka yi miki, tun dazu cewa kike Shahid ne kawai, me Shahid din yayi miki?" Hajiya Kubra ta ce, "Kaga tashi ni zata gayawa ko ma meye.

" Ta koma kusa da Zainabun ta zauna tana rarrashinta, diyar so kenan a dangi da Iyaye, da kyar ta gaya mata yanda suka yi, hankalin kowa ya tashi don sunyi tsammanin su kadai suka san maganar sai gashi yau ta fasu duniya ta sani, nan suka dinga lallashinta akan ta hakura da Shahid din kawai. Abu kamar wasa sai ga Zainabu ta ki ci ta ki sha kullum sai kuka, duk ta rame ta lalace kowa hankalinsa ya gaza kwanciya don dai tana son Shahid matuka, shi kansa dauriya kawai yayi amman idan ya kulle a dakinsa har kuka yake yi. Daga karshe dai Hajiya Kubra ta ce ita dai zata je ta yiwa Iyayansa bayani kaddare ce ta hau kansu wacce bata wuce kan kowa ba, don haka ta sanya Zainabu ta basu kwatancen gidan suka tafi ita da Sumayya. Tun daga harabar gidan suka san lallai ba kananan masu hali bane ga komai a tsare, balle da suka shiga falon manyan hotunan Ayatul Kursiyyu da Yasin da Amanarrasulu, daga ganin yanayin falon kasan gidan masoya addini ne. Sanda matar gidan ta fito duk sai da suka yi mutuwar zaune, ita kam Zainabu dadi ne ya cika ta ta sami guri ta zauna tana musu marhabin, fuskarta a sake ta gaida su ta kawo musu abin motsa baki. Dukkansu kasa ci suka yi, Sumayya ce ma ke karfin halin yin magana, amman Hajiya Kubra kam kunya ta hanata cewa ko uffan. Zainabu ta gyara zama ta ce, "Ai ba daga ni bane, kin san kowa yafi son ace ya auri budurwa cikakkiya ba saura ba balle shi, don haka sai dai na lallabashi na sanar da shi muji yanza zai ce, amman don tani ne babu matsala ba zan matsa masa ba na cuce shi na raba shi da abar son sa ba." Su duka sun san magana ta gaya musu amman sun san bata da laifi ramawa ta yi, tun da dai da can da suke da iko yanzu kuwa itama tana da irin wannan damar, duk da ba itace ta haifi Shahid ba tafi kowa iko a kansa yanzu don ta rike shi da amana da gaskiya. Haka nan suka yi sallama jikinsu babu kwari domin babu wata kyakykyawar magana da suka ji daga garesu, don haka da suka koma gida suka rasa yanda zasu yi da Zainabu sai suka ce yana tafe yace komai ya daidaita. Sanda Mustafa kuma ya ji wai Zainabu ce uwar goyon nan hankalinsa ya tashi, duk da dai yasan ba ita ce ta haife shi ba, sai tsohuwar soyayya ta tashi sai yaji kamar ya nemo Zainabunsa a yanzu, a dai lokacin gaza cewa komai yayi ya shige daki kawai ya kullo kansa, ciwon dake damunsa tsahon shekaru ya dawo sabo fil. 

Bayan sun tafi Zainabu ta kirawo Shahid ta sanar dashi gaskiyar abinda ya sami Zainabu, ta roke shi ya kau da kansa ya aureta a haka domin dai kaddara ce ta hau kanta, ta kuma nuna masa in dai ya amince zata sanar da Babansa tasan ba zai musa ba. Ya ji sanyi a zuciyarsa domin dai zuwa yanzu ya yanke shawarar Zainabu ko ya take zai aureta idan Allah ya so ta shiryu a hannunsa sai gashi ya gane tun tana yarinya ne ma, ya dinga yiwa Umman nasa godiya. Ranar wata Juma'a kawai sai ganin mutane suka yi ana ta sauke akwatina a kofar gidan Hajiya Kubra abinda mamaki balle da aka fara shiga da su cikin gidan. Bayan sun gaisa da Hajiya Kubra suka ce Iyayan Shahid ne, ga kayan lefensu da sadakinsu, kamar Hajiya ta shide don murna ta shiga godiya da shi albarka, don haka ta ce sai dai idan sun yanke shawara su sanar da su, su dai suka ajiye lefensu mai kyau da tsada da sadakinsu dubu hamsin, dukiyar aure dubu hamsin, kudin kayan zance dubu hamsin. Suna fita Hajiya ta zari wayarta ta fara nemo Mustafa wanda ya ce shi zai je ya sami Zainabun da kansa ita har tana da bakin da zata hana auran, sai da ita Hajiyar ta hana shi tace ta san ramawa ta yi sannan ya hakura. Daga karsh an daura auren Shahid da Zainabu, sannan duka families biyun sun cigaba da kyakkyawan Zumunci tare da mutunta juna. Alhamdulillah, Karshen littafin kenan. Mai kaunarku da yi muku fatan alkhairi koda yaushe. FAUZANKU CE! (Matar Bello Q for Q),nidinma danayi jimirin kawomuku akidayaushedai fatana mudinga anfani da darussan dake tafe cikin wadannan kayatattun littattafan da shahararrun marubutanmu ke kawomana.Godiya da jinjina gareku makaranta,fatan zamucigaba da hakuri da juna da haka nakemana fatan sake gamuwa a wani Littafin nan gaba

No comments:

Post a Comment