ILIYA YA HADU DA FALALU
ILIYA YA HADU DA FALALU
Can wajen asuba, sai suka ji motsin
Falalu tafe,
yana keta itatuwa kamar toron giwa.
Yana tafe
yana shakar iska abinsa, don ya san ba mai iya
tarensa da fada. Ya zo ya wuce ta
kusa da inda
su Iliya su ke boye, bai gan su ba.
Sai Iliya ya
ce da jaruman nan, Wa zai iya binsa ya ga inda
ya nufa? In kuma ya ga da dama, ya
tone shi da
fada? Duka sai suka yi shiru, aka
rasa wanda
zai ce zai bi shi. Sai wannan ya dubi wannan,
wancan ya dubi wancan. Iliya ya dubi
babbansu
ya ce ya tafi. Jarumin nan bai yi
gardama ba,
ya tashi ya kara jan majayin dokinsa, ya hau, ya
bi sawun Falalu. Amma duk
zuciyarsa tana dar
dar, yana tafe yana kulle kullen
yadda zai yi, a
zuci. Ya dai tabbata isan suka yi ido da ido da
Falalu, shi ba zai kwana ba. Ya yi ta
tafiya har
ya fara hangen Falalu. Can sai ya
hangi Falalu
ya tsaya ya dubi kansa ya dubi kayan fadansa,
ya dubi dokinsa, ya yi dariya, ya
zaburi dokinsa
kadan, ya yi tabi, ya jefa mashinsa
sama, ya bi
ya café, yana kirari yana cewa, Yau ko da Iliya
ta hada mu ma kara! Yau ina zan
gamu da
Iliya!
Sa ad da jarumin nan ya ji Falau ya
ambaci Iliya sai ya tuna shi ma jarumi ne,nan
da nan
zuciyarsa ta motsa. Daga can nesa,
ya ce,
Falalu! Kayarka ta sha karya, maza
bisa kanka. Idan ka sake kuka yi arba da
Iliya, sai
dai wani ba kai ba!
Falalu fa ya juyo a fusace ya ga mai
magana. Ya yi, wata irin kururuwa
mai ban firgici, kamar aradu ta fadi. Sai
hayaki ya rika
fita daga bakinsa, har da wata irin
walkiya
makar hadari ya taso. Akwai wata
korama kusa da shi, nan da nan sai ruwanta ya
kada yana
kumfa. Ya nufi jarumin nan a
sukwane, shi
kuma ya juya a guje ya koma wurin
su Iliya. Saboda sauri har dokinsa ya yi
sassarfa ya fadi.
Ya dai tashi da rawar jiki ya sake
hawa ya ci
gaba da sukuwa har ya kai wurin
Iliya, yana haki kamar ransa zai fita. Da ya farfade
kadan, ya
fada wa Iliya abin da ya faru.
Duk abin nan Iliya zaune ya ke. Ko
da ya ji
labarin kuwa sai ya yi murmushi, ya kara
kishingida, ya rika wasa da kafarsa.
Ya dubi
jaruman nan ya ga duk sun rude
kowa ido ya
fito. Ya ce, Allah Sarki, tsufa ya zo mana ga
shi kuwa ba mu da magada. Sai ya yi
wuf ya
tashi ya tafi wurin Kwalele, ya shafe
shi ya yi
masa kirari, Kwalele dokin Iliya, Kwalele dokin
yaki. Ba ni saishe ka, ba ni kuwa ba
da aronka!
Kwalele ya yi haniniya kamar ya san
abin da
Iliya ke fada. Daga nan Iliya ya gyar, ya dauko
sirdi ya aza ya daura tamau. Ya sabi
kulki ya
rataya takobin Wargaji, ya dau
mashi da kwari
da baka, ya zabura ya nufi Falalu. Da suka kusa haduwa shi Iliya ya
fara
hargowa, ya na cewa, Kai
lalataccen maridi,
barawo. Don me ka shigo kasarmu
ba da izimmu ba! Falalu ya kara harzuka, ya cika
da haushi.
Ya zaburo dokinsa, Iliya kuma ya
kwarari
Kwalele, za a yi karon battar karfe.
Suka hadu suka ja baya, ko wannensu ya jawo
kulkinsa,
suka yi ta rusa wa juna. Kowane aka
buga sai
ka ji kamr ana fasa dutse da nakiya.
Dajin wurin duk ya rude da amon duka, da
rurin
mazaje. Itatuwa kewayen wurin duk
aka tattake
su. Suka yi ta yi har duk kulaken suka
karye, babu wanda aka yi wa rauni. Kana
suka jawo
takubba. Ji kake kakas, kakas, suna
sarar
juna. Idan takubba suka gamu sai
tartsatsin wuta ya tashi ya yi sama kamar
walkiya. Kafin
a jima takubba suka lalace. Ko
wannensu kuma
ya sunkuci mashi suka yi ta sukar
juna, har masun suka karairaye. Daga nan sai
suka yi
tsaye cirko cirko, suna kallon juna
kamar
zakaru. Da suka huta, sai suka kama
fada hannu da hannu, suka yi ta yi har
dare ya yi, gari
ya waye, rana ta fito ba su rabu ba.
Suka sake
wuni suna ta dambe da kokawa, har
dare ya yi, ba su rabu ba, sai da suka kwana
uku.
Can Falalu ya tuna shi yaro ne, ya
kwashi
Iliya ya yi sama da shi, ys fyada
kasa ya bi ya danne, ya zaro wani gajeren gatari
ya kirba
masa a kirji. Saboda zafin naman
Iliya da iya
yaki ya goce, gatarin ya sari kasa.
Ya yi wuf ya rike hannuwan Falalu da kyau, ya
dube shi ya yi
dariya ya ce, Kai, yaro manya
gabanka! Kura
ba farkar kare ba ce, Rubutaccen al
amari ba shi canjuwa. Samari daga ina ka fito,
mutumin
wace kasa ne kai, wa ya haife ka!
Falalu ya ce, Yaro yana bayan
uwarsa.
Kuma ba ruwanka da kasarmu, ko iyayena!
Wohoho, ai sai ka ce ya watsa wa
Iliya wuta. Ya
fusata, ya sunkuci Falalu ya
wujijjiga, ya kwala
da kasa, ya bi ya take. Tsofo mai daka wa yaro
kashi. Ya ce, Manya ke magana da
kai yaro.
Ka fada mini abin da na tambaye ka
ka huta!
Falalu ya cira kai ya dubi Iliya ya ce, Kai
dattijo ko giwa ta san zaki! Ai ba
kamata ke
magana biyu ba. Abin da na fada
maka da
farko, shi ne. Iliya ya kara fusata. Ya tallabo kan
Falalu
zai yi masa fashin albasa da wari irin
mulmulallen karfe, wanda aka yi don
irin wannan
rana. Falalu fa ya ga halaka a fili, sai ya ce,
Tsaya! Ka yi mini rai, zam fada
maka. Sa
an nan Iliya ya saki kan. Tilas ba
hakuri ba.
Bugu mai kashe kura! Baban Falalu sai dubu ta
taru.
Muryar Falalu na rawa, ya ce, Uwata
Sarauniya ce, amma ubana wani
mayaki ne
shahararre, ya kuwa mutu. Da na girma ni kuma
na ce sai dai in mutu wurin yaki
kamarsa.
Lokacin da zan fito daga gida, ta yi
mini addu
a, ta kuma yi mini wasiyya cewa duk inda na
gamu da wani da ke kira Iliya-dam-
mai-Karfi in
roke shi gafara in wuce, kada in yi
fada da shi.
Wai shi kadai zai iya halaka ni cikin duniya.
Wannan shi ne iyakar abin da zan iya
fada maka
game da labarina.
Da jin haka sai jikin Iliya ya yi sanyi,
ya gane lalle Falalu dansa ne. Sai ya
tasa shi,
rungume shi yana kuka. Ya sumbace
shi, ya
ce, Dana, Allah ya ba mu hakuri mu
duka. Wannan abu rashin sani ne. Na
gafarceka
duniya da lahira. Na kuma yi murna
kwarai tun
da na sami mai gadona. Sa an nan
kuma ya fada masa yadda aka yi har ya auri
Sarauniya da
irin halin da ya bar ta, ya shigo
duniya. Daga
nan ya ce, To, yanzu sai ka yi shiri
ka tafi gida. Ka gaishe ta kwarai. Ka ce idan
Allah ya
yarda wata rana zamu hadu da ita.
Falalu ya
tashi ya kakkabe kura, ya durkusa
ya yi ban kwana da ubansa, ya hau dokinsa ya
tafi.
To, abin da Sarauniya ta gudu ya
faru. Da
ma ba ta so Falalu ya gane Iliya ne
ubansa, ba wani Sarki ba. Ga shi kuwa yanzu ya
gane
haka. Da isarsa kofar gidansu, ko
sauka bai yi
ba, sai ya yi kira da karfi ya ce, Ya
ke wannan tsohuwar banza, munafuka, ashe
wani
matsiyacin talaka kika aura aka
same ni, ba
Sarki ba? To, fito, asirinki ya tonu
yau! Ta fito da rawar jiki, tan kuka, ta
durkusa gabansa
ta ce, Ga ni. Falalu bai yi wata-wata
ba, sai
ya dauke kanta da takobi.
Duk abin nan bai sa zuciyar Falalu ta yi
taushi ba, balle ya ji tausayi. Sai ma
ya juya ya
ce, Bari kuma in koma in kashe Iliya
shi kuma
daya munafikin. Ya juya linzami ya kama
hanyar da ya fito, ya yi ta tafiya
kwana da
kwanaki har ya isa gain da Iliya ya
ke. A
lokacin ya tarad da Iliya yana kwance yana
barci. Sai ya shiga ya dubi kirjin Iliya
ya kafta
masa gatari. Fadi zan dutse, ba shi
shafuwa!
Manya maganin karakar kasa! Ko da Falalu ya
sari Iliya, sai ya sami wata damara
ta karfe da
ke kirjinsa daure, kamar gaba-gaba.
Gatarin ya
yi tsalle sama kamar an sari dutse. Iliya ya farka daga barci, ya ga
Falalu ne
tsaye yana rike da gatari. Ya yi wuf
ya kama
kafadarsa guda, ya yi hajijiya da shi
ya fyada shiga bangon daki, kwam! Nan take
Falalu ya
mutu ko shurawa bai yi ba. Shi kuma
iyakarsa
ke nan.
Da ya ke mutanen kasar ba su san kamar Falalu dan Iliya ba ne, sai
suka yi ta
murna suka kara daukaka shi
saboda ya
kashe shi. Nan ta Falalu ta kare,
Iliya kuwa ya ci gaba da yaki da gwagwarmaya
cikin
duniya.
No comments:
Post a Comment