Pages

12 Jun 2016

AURE KO ZAMAN GIDA ? 11 -

AURE KO ZAMAN GIDA ?





AURE KO ZAMAN GIDA ?

**PART 11**

… Ina gaya miki jabo kullum idan abdul azeez ya fita
sai tayi wata baquwa da qaton hijabinta kinsan
Iranian akwai saka hijabi kaman larabawa to haka
baquwarta take zuwa kullum, Kuma sai mijinta ya
fita ranar ina wajen swimming pool ina kallon ruwa
sai kawai naji maganar namiji amma da farsi suke
magana tana cemishi.... Kaima kasan ina sonka
kuma nafisonka akan Wannan mutumin wllhy abu
kadan nake jira in kama gabana dan nagaji da zama
dashi,Nidai duk wuya duk dadi karki manta dani
kinsan idan baki bazan iya rayuwa ba, Duk wannan
maganar da yaren farsi sukeyi, Basusan inajinsuba,
Abinda yasa ban gara tantacewaba kuwa shi yaren
farsi bashida mace ba namiji suna zuwa tace mishi
karyayi magana ga yar iskar yarinyar nan sukayi
dariya a hankali suka wuce kinga zargi bashida
kyau jabo, So banyi saurin zarginsuba duk da haka
amma abin ya dauremin kai matuqa dan kuwa
muryan namiji sosai naji, Bayan kwana biyu yaqara
zuwa ita kuma tadan fita sai nace masa batanan
yayi kaman bayajin hausa inata magana ba amsa sai
kawai namishi na kurame najawo hannunsa nashigo
dashi sassana na zaunar dashi a parlour har
tadawo, Tunda muka shigo parlour na yake bina da
kallo duk inda nayi, Naji tsoro sosai dan kallon da
yakemin kallon da saurayi yakema budurwarsane,
Nashare kar yagane, Ya miqe tsaye yamin alamar
zai tafi inda nayarda namijine takalminsa dana gani
number 46 nasan ba qafar maccen da zata saka
wannan takalmin nakwashe dadariya nashe da
shigiyar qafa taki kamar ta masu kwasan kashi,
Yajuyo ya kalleni rai abace amma baicemin komaiba
na sake cewa kinsaka hijabi kin rufe rabin fuskarki
kamar munafuka daganin yanda yakeyi nasan
yanajin abinda nake cewa amma ba halin yamin
magana asirinsa ya tono naqara cewa tsawo kamar
palwaya nace duk mijin da ya aureki yayi asara
mace kamar namiji ga munin bala'een dagani kin
hada dangi da bare bare wannan uban muni haka kai
amma duk yayi qawance dake yaji haushi itama
maryam din asara ne yasa tayi qawance dake,
Wannan magan ganun da nake masa inayine dan
kawai yayi magana inji shin namijine ko mace amma
yaqi yayi saima daure fuska da nayi muka kawo
kofar shiga gidan ta nace mishi (khuda hafee) Sai
anjima yanda nafada irin nayan koyo kar yayi
tunanin na iya yaren, Yamin murmushi ya daga
hannu araina nace kinga gardin banza wllhy wannan
namijine kuma saina tona musu asiri abin duniya ya
isheni sai wata dabara tazomin kamin suzo lambu
suyi hira sai insaka wayata agurin inyi recording din
abinda suke cewa hausa da farsi duk ina ganewa
ranarda nasami abinda nakeso kuwa ranarda sukayi
maganar cewa shi ya gaji gaskiya zai sace mustafa
(sunan yaronta kenan) Dan yana buqatar dansa
agidansa tanata faman roqon ya rufamata asiri har
taqare hada dukiyarta sugudu tare sun saka ranar
da zasu gudu nikuma nashirya tona musu asiri
karkiyi tunani cewa wani abu yana shiga tsakanina
da Abdul azeez aah ba komai tsakaninmu dashi sai
sallama, Sai sannu da zuwa, Ranar da safee natashi
yana fitowa nace masa inada magana dashi yau
misalin qarfe biyu na rana yazo gida kuma banason
idan zaizo yagayawa uwar yayansa zaizo kawai
idan lokacinda nakeson ganinsa yayi zan kirasa
yakuwa amince yanajin dadi, Yadauka wani abune
kwarton maryam yana zuwa, Da kamar awa daya
nakira Abdul azeez nace yazo da sauri kuma kar
yazo da motarsa…………


AURE KO ZAMAN GIDA ?


*PART 13*

Na Hauwa M Jabo.

Tunda muka iso nake tunanin yanda zan bullowa
plane in mishi magana amma nakasa saboda banga
fuskaba sai nayanke shawarar bari in toneshi ingani
haushi zaiji idan yaji haushi sai inbashi haquri haka
kuwa akayi bayan sallar isha yana zaune kamar
wani gunki nazo ina kur6ar tea ahankali nace masa
kana tunani uwar yayanka maryam ne...!??? Ya
waigo ya kalleni cike da mamaki da al'ajabi nasake
maimaita abinda nace naqara da cewa ko in samo
maka pic dintane ka kalla ko kaji sanyi,? Namiqe
tsaye nace ko kawai kabita qiyama ku soye acan
zaifi kazo nan kana tunaninta ko ka kar6o yaronka
agurin kwarton matarka nasan shi yake damunka.!,
Na kama hanyar dakina naji an kamoni ta baya da
qarfi wllhy jabo saida cup din da yake hannuna ya
fadi, Kinsanni akwai iskanci amma akwai tsoro, Ya
jawoni daf dashi ya d'ago kaina da qarfi yana
kallona har inajin nunfashinsa yana dukan fuskata
yace wllhy wllhy Wllhy..!!! Idan kika qara yimin
maganar maryam da mustafa sai kingane baki da
wayo a gidannan ya dallamin wata muguwar harara
sannan ya sakeni, Nace nasan zaka iya kasheni ma
tunda na rabaka da uwar yayanka da danka da kake
tunanin ita kadai zata iya haifa maka yaya, A fusace
na fadi maganar ashe mutumin yagane kishi nakeyi,
Sai yayi murmushi kawai yaje yazauna, Nasha jinin
jikina na wuce daki sumuy sumuy kamar munafuka,
Bayan kamar awa uku sai gashi yashigo dakina naji
tsoro sosai, Yazo daf dani yazauna ya sunkuyar
dakanshi yacemin zaki'iya zama dani zainab.?
Araina nace miya kawo wannan tambayar? Kinyi
shiru ina tambayarki zaki iya zama dani ko yaya??
Nanma ba amsa ba, Ya d'ago kai ya dubeni yace,
Zainab arayuwarki na cutar dake fiye da tunanin duk
wani makhluqi, Zainab banta6a son wata ya maceba
sai akanki, Tun kina yar shekara tara na nemi
mahaifinki ya bani aurenki kuma ya amince inda na
fara ganinki kinje wani gida kina talla sai wasu yara
suka qwace miki cinikin da kikayi duka suka gudu
kina kuka na hadu dake natambayeki kikamin
bayanin yanda akayi na biya kudin nakuma rakaki
har qofar gidanku idan zaki iya tunawa, Wllhy tun
lokacin Allah ya dasamin sonki azuciyana nagayawa
babanki yace yamun alqawari zai bani ke da yake
lokacin ina boarding school nakoma makaranta duk
abokaina sun san sunanki har naqare karatu naje
university ina university Kullum sai inzo da mota inyi
parking inda kuke tsayawa talla inyi ta kallonki har ki
saida waranki har nazo nafara sayen waran ina
cewa kiyi sadaka amma darana daya baki ganni ba
bakiga fuskataba lokacinda naga kinfara tasawa nayi
tsoron kar wani ya kwaceminke nayi magana da
iyayena dagyar suka amince kuma nagayamusu
yanda nashirya za'a dauramin aure dakene dan kar
wani ya gwacemin ke nacewa babanki ki riqa saka
hijab hadda niqab kuma duk suka amince da hakan
akan zanje wani.....



No comments:

Post a Comment