ASHE KAINE MIJINA ?
ASHE KAINE MIJINA ?? 52.
Na HAUWA M.JABO..
Hello deen,
Hello...Kanajina kuwa?
Eh inajinki.!!
Ya naji kana magana fada fada.??
Waya tabamun kaine??
Kedai ki fadi abin da xaki fada kawai.!!
Tayi shock dajin wannan maganar a bakin deen, wanda daidai da rana daya bai taba mata koda gaddama ba bare ya mata baqar magana.!!
Tayi ajiyar xuciya,
Allah ya baka haquri, dama maganar cikinnan ne nace ya xa'ayi dashi.??
Kuma dama inason in gayamaka na karbi takarda sakina..!!
Deen yayi duuum jin wannan maganar ta hulwaty, Lallai maisha ta riqa tasha ba abinda yafi illa ya fatattaketa ta rabu dashi, amma ya mata adalci kuwa? Anya yiyiwa kanShi da son da yake mata adalci kuwa?
Anya xai ma iya rayuwa ba hulwar sa, xaka iya mana dayan xuciyar ta bashi amsa....
Takeshi daga dogon tunanin da ya tafi, deen kayi shiru deen!! ,
Yanda ta fadi maganar da murya mai Sanyi sai ta qara bashi tausayi.!!
No Inajinki ci gaba..
Ai na fadi duk abinda xan fada.! Kai nake jira...
Dama ke duk abinda mukeyi dake kinSan bakiyi planing ba??
Dan ki xubar min da mutunci yasa kikayi tarayya dani?
Akan me xaki bari ciki ya Shiga,??
Ta yaya xan aureki da ciki??
Sam bakiyi tunaniba kuma bakiyi naxariba, ni Muslimine baxan taba yin shirka gurin xubar da cikiba, Sabida haka kisan yanda xakiya da cikin ki, ki nemi mijinki kuyi Sulhu ya rufa miki asiri ba hannuna ac......
Deen kaine kuwa..!!? Ta Katse shi cike da mamakin abinda yake fitowa daga bakin deen mi yake Shirin faruwa da itane abin kamar a mafarki...
Ki saurareni ya fada yana mai daqa murya.!!
Daga yau Sai yau kada ki qara nemana..!! kadama ki qara nuna kinSanni.!! jahilar banxa wacce batada tunanin....
Bansan lokcin da wayar hannuna ta subucemin ba cikina ya fara juyawa na fadi qasa na fara rero kukan nadama...
Tabbas na jahilace tana kuka tana surtai,banida ilimi gaskiyan ka deen ni jahilace ina matar aure namaida wani namijin mijina ina xankai haqqin aurene??
Kadan daga axabar da Allah xaimin kenan kamin inje qiyama inchi ubana...
Chikinta yaci gaba da juyawa, sai ta fara xubar da jini,
Ta tabbatar da idan har ciwo yakamata anan sai dai ta mutu ba wanda xaikaita asibiti,
Ta rarrafa tun tana ganuwa taja mota sai hospital, kamin ta Isa ta jiqe sharkaf da jini, bayanta kamar ya bude..
Takasa qarasawa cikin sai kwasarta akayi akayi ciki da ita,
Likitoci sukayo kanta, aka mata allurai....
Lokacinda ta farka taji ana qara mata ruwa, Dr yaxo yana mata sannu,
Hajia naziah sai dai kiyi haquri munyi iya bakin qoqarinmu na ganin mun tsayar da xubar cikin amma abin yaci tura, qarke ma Sai mukaga idan mukayi wasa xaki iya rasa rayuwar ki, sai kawai muka miki allura cikin ya qarasa xubewa...
Wata hamdala tayi hadi da jin dadi, lallai Allah ya rufa mata asiri da ya xubar da cikinnan...,
Dr yace
Yanxu xamu baki allurai da yan magunna kuma yakamata ki sanar da mai gidanki halin da ake ciki, kamin mu sallameki,
No Dr maigidana baya gari kuma ni ba yar nan bace.! Tafada muryanta yana hadewa,
Dr ya kalleta yace to shikenan xaki xauna anan har zuwa gobe ko jibi idan kin qara Samun lafiya Sai mu sallameki...
Dr kayi haquri ka sallameni yanxu kaga banxo da phone dina ba kuma nasan mijina da iyayena xasuyi ta nemana hankakin Su xai tashi ataimaka min please Dr...!!
Hajiya baxai yiWu ba, duk da kinada cikakkaiyar lafiya amma ya dace kidan qara samun rest....
ASHE KAINE MIJINA?? 53
Na HAUWA M.JABO...
Samu rest, duk yanda Dr yayi akan naziah ta bari har gobe idan taqara jin sauqu a sallameta ta tafi gida amma abin yaci tura, ta nace akan tunda tanada lafiyar ta gida xata tafi...
Ya rubuta mata magunguna da kuma allurai , kuma yace tana buqatar hutu da natsuwa, yace mata mahaifarta ta sami matsala xata riqa zuwa ana dubata har ta Sami lafiya,kuma idan tayi wasa xata iya rasa haihuwa har abada, ya qara bata haquri akan Kasa war da yayi na ceton yaron dake cikinta kamar yanda ya mata alqawari anan dai ya qara mata bayanin cewa dama cikin xai xube dan ba daidai yakeba, haka ta dawo gida guraren 11 na safe, tanata saqe Saqe aranta har ta iso gida,
Nidai banyi dacen rayuwa ba, na cutar da kaina na cutar da mijin aurena, nakasa kare darajar aurena, qarke ga yanda deen dina yamin, Lallai maxa ba abin amince wa bane, anya kuwa deen dinane yamin haka??
Dayan xuciyar ta ya bata Amsa Eh deen dinke malam naziah...
Any how mun tashi 1__0, tasha alwashin sai ta rama abinda ya mata...
"Kinji hauka ko ina xata Ganshi ta rama ohoooo"
Ta iso gida ba qarfin jiki, ta Samu tayi wanka da ruwan dimi ta qasa jikinta Sosai tasha tea ta nemi guri ta kwanta, a baccin ma dai mafarkin deen ta riqayi, tana taShi ta tsine ma baccin da mafarkin gaba daya..
guraren qarfe hudu na yamma sms ya shigota, taji duuum nurane
"JIBI NIHAL XATAXO KI GYARA MATA DAKINDA XATA SAUKA" ....
Tayi duum ita kadama suxo Suga halinda take ciki su ganota,
Hakanan ta lallaba taje dayan banqaren ta dan gyara sama sama, ta koma dakinta, dama naziah akwai xama daki "kamar jabo"
Yauce ranar da nihal xata iso guraren 4:pm xata iso,
Nura yasa an yo siyayyah abubuwa kala kala duk na tarbar nihal,
Naziah aranta taji tana son gani wannan yarinyar da ake axarbarbabin zuwanta...
kamin qarfe biyu ta kammala hada komai gida yayi fes dama fes yake girki kala kala ta hada duk na tarbon nihal, itama dai tadanyi wanka duk da yanayin yanda ta kode ta chanxa tayi wani iri da ita amma dai tayi kyau, abinka da kyakyawan mutum...
ASHE KAINE MIJINA.?? 54
Na HAUWA M. JABO..
Tana xaune parlour tana kallo har guraren biyar basu isoba,lokacin shan maganinta yayi ta shiga daki kenan taji qarar mota haka qirjinta ya riqa dukan uku uku, ko miye haka ohoo..!!, tanajin maganar Su sama sama, abinda yafi bata mamaki muryar wacce takeji kamar tasan muryar amma ta manta inda tasan muryar,
Aunty..!
Aunty..!!
Auntyyyyyyy..!!!
Ina kike gamu mun iso, muryar da taji kenan ana gwalla mata kira,
Shikam nura yana ijiye nihal ya fita dan kada naziah ta kwafsamai gaban m nihal....
Na'am ina zuwa... naziah ta bada amsa a taqaice..
Ta fito qamshin da taji Lallai tasan qamshin, amma tasan hancin tane yake yaudararta...
Tafito da Walwala abinda take gani gabanta yafi bata mamaki akan komai, ba kowa bace face tsahuwar qawarta da tafi tsana a rayuwar ta itada mugun uncle dinta wacce Sanadiyar su ta bata wato sista khadee, tuni ko wacce ta daure fuska naziah ta kalli s...khade a wula qance ina nihal take??
Nihal ta kalli naziah cike da mamaki da al'ajabi Lallai wannan naziah ce kuma itace matar uncle dina dama ance mata sunanta naziah...!!
Kuuut yau ake yinta..
Ko wacce na kallon yar uwar ta, nihal cike da mamaki tace nicefa nihal din,naziah tace miya kawoki nan gidan, suna cikin magana kawai sai ga nura ya shigo...
Nihal..!!
Nihal...!!
Ya Shigo da kaya niqi niqi a hannu yana kwalawa nihal kira..
Abinda ya gani shine ya bashi mamaki hade da daure kai, ledodin hannun sa duk suka xube,
Jikin Sa na rawa hadi da sarqe war murya ta tashin hankali hadi da tsori ya kalleta murya na dancing, ke miyaa miyaa kawoku gidanaaa.!!??
kinxo dan ki tarwa tsamin iyali na hadi da jin dadina ko??, waima uban wa ya baki address din gidana...!!! Naziah ta gama raxana jin yace miya kawota gidan sa, idan dai nan gidan sane to Lallai mijintane!!
Kuma shine uncle din sista khadee da yace mata almajira kuma ya mareta, shine mutun na farko data tsana a tarahin rayuwar ta.!!
Shine sanadiyar batanta.!!
Kuma shine mutumin da ta qara tsana second time a rayuwarta wanda yayi sanadin shiga tashin hankalinta..!!
Jin tayi an katsata da wata irin tsawa ke hulwa badake nake magana ba??
Nura ya kalli nihal yace ke ina naziah ta shigane??
Nihal ta kallu uncle dinta cike da mamaki tace uncle wannan ma ai sunanta kenan fa naziah .. WHAT???
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA.? 55
Na hauwa m. jabo...
What???
Eh uncle itama sunanta nazia....
itace qawata da nake baka labari lokacin,
kuma itace wacce ta maka rashin kunya lokacin da taje gidan mu,
No bashi nake neman saniba nihal.! wai itace matar tawa???
nihal da mamaki ta kalli uncle dinta.! tace kaman ya uncle dama bakasan matar taka ba???
yayi shiru yarasa abinda xai fada...
ita nihal mamakinta shine wata hudu dayin auren baima tama sanin matar ba to ya akayi akace mata tayi ciki?? kuma uncle yace mata bai santaba baima taba ganintaba amma batayi tunanin abin yakai hakaba!!!
nazia iya tunaninta ta gane cewa lallai wannan nura shine mijinta, kuma shine uncle din sis khadee, kuma shine deen dinda ya yaudareta yaci mata mutunci....
Dukansu sunyi churko churko kowa ya rasa abinda xai fada.!!
nazia taji tsoro matuqa tayi tunanin kada su mata wulaqancin dayafi wanda deen ya mata da wanda wannan tsohuwar qawar tata ta mata, tajuya xata koma dakinta ta tattaro kayanta ta wuce gida tunda dama ya saketa..
tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki dama batada lafiya cikinta daya xube...
tayi taku biyu uku kikajita lauuuuu... ta fadi "nima jabo bansan miya sa ta fadiba" duk sukayo kanta nura jikinsa na rawa yake bubbugata amma ko motsi batayiba hankalinsa ya tashi matuqa suka yayyafa mata ruwa amma inaaa shiru da sukaga xasu bata lokaci sai suka dauket
sai asibiti....
a hanyar asibiti kamin a isa ta farfado taganta a mota tayi yunqurin miqewa xaune taji an dan daneta irin ta kwanta dinnan a jikin wani qamshin da takeji yana dukan hancintane ya tabbatar mata cewa tana tare da deen ne ta daqo dagyar tana dubawa taganta ashe jikin deenma take kwance...
dukda rashin qarfin jikintanba bai hanata tashi a jikinsa da qarfiba hadi da dalla mai harara da wani uban tsakiba, ko ajikinsa shidai ta samu lafiya itada dan cikin da ke jikinta!!! "kunji wawa baima san cikin ya xubeba koni jabo da masu karatu munsan cikin ya xube ko baku saniba????"
kusaukeni anan.. !! ta fada a taqaice dan bata iya magana sosai. deen ya bude baki xaiyi magana...
Nace a saukeni anan!! Wannan karo da gadara hadi da isa ta fada tare da tsiwa irin tata,
komai ta fanjama fanjam...
ta murda marfin motar wallahi idan baku tsaya ba xan sauka, kuma motar tana tafiya ne...
deen ya tabbatar da xata aika yacema nihal ta tsaya tafita ta basu wuri...
nazia tamai kallon banxa. dawa xa'abarka???
No comments:
Post a Comment