ASHE KAINE MIJINA..?21
Na HAUWA M. JABO.
Mamaki ya kama sista khade, taga yanda na mari ganin mahaifinta, wanda yake ji da ita, kuma a gabanta a gidansu.!! Lallai koda uncle ne bahida gaskiya dole ta nuna ma naziah kuskurenta dan gaba...!!
Sista khade ta kalli nazia tace, ke dama yar akuyace??? Wacce batasan darajar na gaba da itaba?? Wallahi da nasan ke butuluce da bazan taba qawance da yar qauye irinkiba.!!
Mamakin duniya ya cika nazia dama haka sista khade take mara mutunci to ba gyaleta zanyiba, wata zuciyar tace ki gyaleta gidansu kikaxo, sista khadee sai masifa takeyi, inda take shiga ba nan take fitaba, zuciya ta rufe naziah uncle yayi Sokoko yana saqa Wulaqancin da xai mata, ni kuma ga mugun jirin da ya qara tasomin ga sanyi inaji ga yunwa, na dunqule hannu nakaiwa sista khadee wani wawan nushi, kuma na kamata da duka baki, sai jini, unle yana tsaye riqe da kumatu yana dada kallon wai almajirace zata mishi wannan wulaqanci yana chi gaba da saqa sharrin da zai mata kuma yasa a ma danginta wulaqanci, sai ganin yayi ana kokowa, tuni ya hanbare ni a wurgar dani gefe, ina miqewa na kama hanyar dana ga na biyo mun shogo na samu na fita gidan nakama hanyar titi kamar mahaukaciya, ga warin kwata gashi ina layi kamar yar maye, gashi banida ko kwandala na shiga taxi, ina tsaye idona sun fara rufewa naji qarar mota gabana, sai jin nayi yace ina zuwa na fada mishi unguwarmu tuni ya bude min nashiga........
ASHE KAINE MIJINA. 22
Na HAUWA M. JABO.
ya bude min nashiga, ina shiga motar ban qara sanin inda nakeba, suma nayi mi nayi Allah masani, sai farkawa nayi na ganni a wani makeken gado an saka min ruwa, na bude ido a hankali, na jujjuyasu bansan inane nan ba, nayi qoqarin tashi amma nakasa tashi kaina yayi nauyi, naduba sai naga ashe ruwa ake qaramin, iya tunanina gidan su sista khadee ne tunda daga chan nafito, my be faduwa nayi aka maidani chan.! Kawai sai na daure fuska dan kuwa banason ganinsu. Banason taimakonsu, banason duk wani abu daya shafesu, ina kwance sai ga wani saurayi gajere fari ya shigo, ina ganinsa, na fara surutai, miyasa kuka maidani gidanku, miya dameku da lafiyata da ciwona?? Kumaidani gaidanmu banason ganinku ko kadan, haka nayita surutai ina qoqarin cire drop dinda aka sakamin sai naji ya riqe hannuna, na daga ido na kalleshi baice min komai ba saima bina da ido da yayi ina balaee na, naso in ci gaba sai kuma na fasa sabida kaina yayi nauyi Sosai ihun da nayi.. namaida kaina, na rufe idona, bacci mai nauyi ya qara daukeni banfarka ba sai tsakiyar dare, abin mamaki.........
ASHE KAINE MIJINA.?23
Na HAUWA M JABO.
Abin mamaki gajerin qaton da na gani daxu shine na gani kwance a gefena yana sharar bacci abinshi, dayake qadon qatone Sosai, kuSan gadon ya cika dakin, har yasa ko gurin sallah babu, na tashi ina dube dube ga dukkan alama nan dakin mazane, amma sista khade ta cuceni maimakon ta kaini dakinta sai ta ijiyeni anan? Dakin uncle dinta Wallahi nida ita har abada ta xubar min da mutunci yanxu idan yaya da inna suka ji na kwana daki daya da qato mi xasu kalleni,.....!!??
N qare tunane tunane da bala'eena cikin xuciya, nayi niyyar in tayar dashi ya kaini gida amma kuma na fasa, na dago kaina na hango qofa biyu naje a hankali na murda daya najita gam a kulle na murda ta gefenta sai ta bude na leqa sai naga ashe toilet ne, ko nayi wanka bnida tufafin sakawa gwanda in haqura nayi fitsari nafito, raina duk a bace, ina dubawa naga ledar DAY TO DAY, kuma ledar ta clothes ce sai na buda ina dubawa naga tufafi da brush da duk abin buqatar mace hadda pad ko sista khadee dan uban tace mishi bana sallah ohon mata!!!??
Na dauki ledar na shiga bayi na kulle nayi wanka da yake kaina adaure yake, amma dai gashina anyi sama dashi hakan ya bani damar wanke gashina tsab, nayi wanka kamar ban taba wankaba, ga ruwan da zafi Sosai, duk sanyi da kasalar da suka rage naji sun tafi, nayi brush, amma yunwa ta addabeni, na saka kayan top ne da jeans, nafito kamar baniba, amma zuciyata cike da haushin su sista khadee, ina fitowa naji ana kiran sallah, na tuna inna tace kada inkai maqreeb.......
ASHE KAINE MIJINA.24
Na HAUWA M. JABO.
Kada inkai maqreeb, naje na tayarda wannan gajeren yana wani mutsuke ido, mlm ka tashi kaje ka kira sista khade akaini gidan mu ko a budemin qofa inje gida... na fada cike da qadara, wani kallo yakemin, kallon baisan alqiblar maganataba, kallon mi kike nufi??, ya tashi zaune, amma kya bari gari ya waye sannan akaiki gida ko,?? wane gari zan bari ya waye? Yace Bakiji ana sallar asuba bane??Asuba!?? Dama asubace ba maqreeb ba?? Kuka ya kubucemini ba tare da nasaniba, miyasa sista khadee tamun hakane? Miyasa zata bari ihar in kwana gidansu kuma ta ijiyeni a dakin uncle dinta??
Lallai khadija ba qawar kirki bace, wannan duk araina nakeyi, na dago na kalli mutumin nan,na rasa irin rashin kunyar da xan surfa mai, kawai, nace uncle to sista khadee ta gayawa inna da yaya ina gidansune??, sabida inna tace kada in kai maqreeb gashi har gari ya kusa wayewa?? Yayi kasake yana kallona, kayi magana mana uncle, yaji dadin sunan data kirashi dashi, har yana maimaitawa a fili uncle.!!! amma kuma shi wacce sista khadee ce take fada haka, Lallai idan yagaya mata baisan sista khadee ba wannan rudaddiyar zata daga mishi hankali fiye da na yanxu, amma zai lallabata har gari ya waye sai ya mata bayanin komai, da sanyin murya yace ki zauna in miki bayani, kinji sister na, da jajayen idona na dago na kalleshi jin ya fadi sunan da yaya yake kirana dashi, sai na sami kaina ina maibin umurninsa, na zauna girmn kai ba nawa bane na xauna.,........
ASHE KAINE MIJINA 25
Na HAUWA M. JABO.
Na zauna, kiyi haquri zuwa wayewar gari zan gaya miki komai, kinji? na daga kai alamar shkenan ba komai, na zauna jigun, chan natuna banyi sallar ko azzahar bare magreeb gashi har an kira asuba, na miqe naje na dauro alwula nazo nayi sallolin da suka hau kaina bayan na kammala nayi sallar asuba nayi addu'a Allah ya fitar dani wannan qangi da sista khadee ta jefani, ya tsareni da sharrin uncle dinta,!
Anan zaune bacci yayi awon gaba dani ban farkaba sai guraren tara na safee, ina farkawa na duba bashi ba labarinshi, na tashi na murda qofa najita kulle gam, ga BF nan an hadamini an ijiye mini, wasu zafafan hawaye suka gangaro a kumatuna Lallai sista khadee ta cika yar iska! Wato haka zata min ko? Ba wata mafita illa in danne abincina in barwa Allah ko na mutu in tafi ciki da nauyi.!!
A bangaren iyayen nazia kuwa tunda inna taga an kira maqreeb bata dawo ba ta kira wayar nazia, tana ringing amma ba'adauka, tayi ta kira har ta qufula ta daina kira ta dauki alwashin idan ta dawo zata gane kurenta, shiru nazia har qarfe goma bata dawoba, sai hankalin inna ya fara tashi, ta dauki waya kena zata kira yaya hafeez sai gashi yazo, kasan fa har yanzu nazia bata dawo ba!??, haba dai,? Allah kuwa! Kuma nayita kiranta bansametaba, to baki kira qawar tataba? Eh ban kiraba, to bari in kirata.
Saida ya kira sau uku ana hudu aka daga, batayi maganaba shi ya fara sallama aka amsa mishi sama sama, yanxu inna take gayam nazia har yanzu bata dawoba! Kuma tace gidan ku xataje kamar yanda kika roqa na amince ta tafi, tace Nazia kuma?? Ai batazo nan ba!! What???.......
ASHE KAINE MIJINA.26
Na HAUWA M. JABO.
What..!!!?? Eh batazo ba nace, ai kuwa tun safee tafito gida tace zatazo gidanku, kamar yanda kika buqata inna ta barta tazo, hmmm to kuwa banan tazoba, sai ku kira wayarta kuji ina yarku take.! Ban..... yaji ta katse waya bata ma saurari abinda zai ce mataba, ya juyo yayiwa inna bayanin abinda khadijar ta fada hankalinsu duk ya tashi, suka fito aka fara chigiya unguwa unguwa har kofar rini unguwar su sista khadee saida akaje nemanta, amma bata ba labarinta, gashi dare yayi, haka suka kwana zaune, ga wayarta na ringing amma ba'adauka guraren asuba ma wayar saita daina ringing hankali ya qara tashi, tunda asuba yaya ya koma police station aka kai hotonta ana cigiyarta, aka kai gidan tv gidan radio jarida duk aka baza ana nemanta, amma har guraren 12 na rana ba ko karenda yace ya ganta,
Tana zaune ta tanqware gafafu, taji ana murda qofa, tuni ta miqe tsaye tana jiran shigowarsa, yana kunno kai dakin da sallamarsa da murmushin sister har kin..... sai saukar mari yaji a fuskarshi, kai mahaukacin inane da xaku kawo gidan maxa ku ijiye, idan ita khadijar yar iska ce to ni ba yar ita bace kuma ka gaggauta maidani gidn mu...!!! ya dago da sauri ya kalleta, ya daga hannu zai mareta kome ya tuna kawai ya sauke hannunsa,ya dunqule hannu rai bace ya mata wani kallo ya wurga ledar da ya shigo da ita ya ja qofa ya kulle ya tafi abinshi, sai tafara dana sanin hukuncin da ta mishi, tafara Allah wadai da zuciyarta,da kuma rashin kunya irin tata, miyasa ta mishi haka?? Lallai bata kyauta ba gashi ya tafi ya barta,jiya ta mare shi yauma ta mare Shi, itako haka xata qare da dukan maxa..!!!!?
qeqe idonta ba kuka ba alamunsu ta miqe ta janyo ledar Abincine take away guda biyu komai dai guda biyu, da alama da nashi da nata dasu drink da ice cream duk a ciki, ta bude ta sa abincin gaba amma ta kasa chi tayi tagumi ta tashi tayi sallah azzahar tananan zaune har la'asar tayi sallah taga cikinta ya fara ihu, ta janyo abincin taci ta qoshi,a haka bacci yayi awon gaba da ita.......
ASHE KAINE MIJINA..27
Na HAUWA M. JABO.
Gaba da ita har dare yayi bashi ba labarinsa guraren sha biyu ta dauko abincin dazu, dayan da ya rage ta chinye, shiru shiru har bacci ya dauketa bata farka ba sai guraren biyar, bashi ba labarinsa, amma kuma ya ijiye mata ledar BF.
hakadai wasa wasa har saida Nazia tayi kwana hudu a gidannan bata qara ganin saba, kuma kamar aljani sai tayi bacci yake kawo mata abinci abin yana daure mata kai, yau ta dauki alwashin bata ba barci, har kusan maqreeb ba'a kawo mata abinci ba, data gaji da jira sai ta dan gyangyada baccin da tashinta duka minti hudune amma har ya kawo abinci ya fice abnshi, tunani kala kala takeyi, ta fara tunanin ko ta daina cin abinci ne, wata xuciyar tace ki danne abinki ko kin mutu kije da nauyi..
Duk tayi wani iri da ita ammafa bata rameba ko kadan dan kuwa bata wasa da abinci saidai akwai alamar tashin hankali tare da ita,
Iyaye anyi sanarwa har an gaji bata ba labarinta, anje gun malamai suna ta addu'a anata sauke qur'anai Allah ya bayyanata amma shiru.. sister khadee kuwa bata ma san cewa har yanzu ba'aga nazia ba, hankalinta kwance tana al amarrunta, ko a skull da andauko zancenta sai tabar gurin batason zancen, bata San xancen batanta akeyiba, su kuma sauran sun dauka haushin rashin qawane yakesa bata zama cikin mutane musamman da ake cewa garin zuwa gidansu ta bata..
Yaudai baxanyi bacci ba sai naga aljanin da ke ijiyemin abinci,baccin qarya nayi ya dauka nayi bacci ko minti uku ba'ayiba naji ana buda qofa a hankali bayan ya bude sai kuma ya tsaya kamar bayan minti daya sai aka turo qofa ina jin ya turo qofa nayi zubur na miqe dama akan dadduma nayi baccin gefen qofane........
No comments:
Post a Comment