Pages

8 Jun 2016

AMINNAN JUNA 151 - 160

,AMINNAN JUNA




AMINNAN JUNA


Na Xarah~B~B

~151-155~


"BAYAN KWANA BIYU"

Abubuwa da dama sun faru daga ciki harda amincewar soyayyar ya Affan da zarah tayi, tun daga tym din soyayya mai qarfi da shaquwa suka shiga tsakanin ZARAH DA YA AFFAN, ammi kuwa tafi kowa jin dadin faruwar hakan sbd ta yaba da hankali da natsuwar ZARAH

Su Amrah na hango sun shirya tsaf kowanan su yayi kyau bama kamar zarah ba, wayar zarah ce ta dau ruri ganin ya Affan ne yasa ta yin murmushin da ke qara fitar da kyan ta "Assalamu Alaikum", naji ta fada, adayan bangaran aka ansa da "wa'alaikun salam y kk tauraruwata?" ta ansa da "lafiya qlw nd u?" "D same" yabata ansa a taikaice", " idan kun shirya ku fito muje ina parking area" "ok gamunan fitowa "tou sai kun fito" tare da tsinke wayar"

"My futha ya Affan yace fa mukadai yake jira" zarah ta fada, dariya sukayi sa'annan sukace "tou matar yaya" tare da fita daga dakin, a palour suka same ammi tana kallo a TV, "ammi zamu tafi fa" inji Futha, "au kuce har kun shirya ma" "eh ammi mun shirya", "ok Allah ya kiyaye hanya ku gaida NABEELERT din" "zataji Amii" tare da yimata sallama suka wuce, a parking space suka tarar da ya affan bayan sun gaida shi suka shiga mota zarah zata shiga baya ya affan ya harare ta "ohhhhh kuce na zama driver dinku kenan", "uhm aa" ta fada "tou oya shiga gaba mu wuce" "ok" sa'annan ta shiga su Futha kuwa ba abunda sukeyi inba dariya bt basu bari ta fito ba.

Haka suka dau hanya sai GRA unguwar su aunty BEELERT kenan, anan ya barsu tare da shaida masu da cewa anjima zai zo ya dauke su, daganan ya wuce.....

Urs
Zarah~B~B.


AMINNAN JUNA


~156-160~




A parlour suka same ta kwance kan 3 seater tana kallo mbc bollywood da fara arta ta tarbesu bayan sun zauna ne take cewa "ni nayi fushi kwanan ku nawa a garin nan sai yanxu zaku zo?,, "aunty beelert plz we are sorry wlh muna son zuwa kin san komai sai Allah yasa" Amrah ta fada, " ai yanxu gashi munzo ko?" inji Futha "ni yiman shiru daman nasan kece kika hana su zuwa dan daman kema ba son zumuncin ne Dake ba", "aa fa aunty nifa ba ruwana" tana wata dariya can kasa2, " Amrah wacece wannan bangane ta ba" futha tai carab tace "zarah ce qawar amrah tare suka zo kuma........

 " kallonda zarah ta mata ne yasa takasa qarasawa, "kuma me?" inji aunty beelert, "no aunty zan fadamiki bt ba yanxu ba" ta qarashe mgnr cikin zolaya, sun jima suna fira kiran sallar azahar ne ya tada su, bayan sun qare sallah ne wayar zarah ta dau ruri tana dubawa taga dai wannan sababbiyar number ce da ake damunta da shi saidai yanxu ta san mai number ba kuwa bane illah FAROUK har ta tsinke bata daga ba qara kira akayi ganin batada niyar dagawa yasa amrah daga wayar "ajiyar zuciya ya farayi kana yace "haba my zarah meyasa bakya son daga wayana? Kiyarda dani plz wlh zarah INA SONKI son da ban tabayiwa wata ya'mace ba, duk wata soyayya da nakewa Amrah wlh duk shirme ce, kece madubin dubawa na", jin batayi mgn ba yasa shi cewa "talk plz zarah" Amrah da tun da taji muryar hubbin ta ne tayi mutuwar zaune tuni hawaye suka wanke mata fuska ta kasa fadin komai sai rawar jiki da takeyi.........

Urs Zarah~B~B

No comments:

Post a Comment