Pages

6 Jun 2016

ABIN AL'AJABI

ILIYA DAN MAI KARFI


ABIN   AL AJABI


A wani gari can cikin kasashen Gabas, an yi wani ana kiransa Sahabi, da matarsa wai ita Murjanatu.  Suna zaune cikin gidan gona.  Ba wadansu wadatattu ba ne sosai, amma kuma ba matalauta ba ne.  Suna da yan dabbobi da gonaki.  Abin da dai ya rage musu jin dadin zaman duniya shi ne rashin magaji kawai.  Allah bai nufe su da samun da ba.

            Shekara da shekaru suna ta neman haihuwa, amma ba su samu ba.  Ran nan kwanci tashi, sai Murjanatu ta sami ciki.  Wai kada ka so ka ga irin murnar da Murjanatu da Sahabi suka yi.  Tun cikin yana da wata hudu, Sahabi ya soma tanadin iccen biki.

            Ran nan da rana tsaka, Sahabi yana aiki a bayan gida, cikin gona, sai ya ji an rafsa guda, Ayyururui! Ayyururui! , har sau uku.  Sahabi ya jefad da fartanya, ya sheko da gudu cikin gida.  Da zuwansa kuwa ya tarar da abin da ya ke fata ya gani.  Murjanatu ta sauka, ta sami da, namiji, santilo.  Da ranar ta kewayo, jama a suka taru, aka rada wa jaririn suna Iliya.

            Ana nan har yaro ya kusa isa yaye, sai rashin lafiya ya same shi, kafafuwansa duka biyu, da hannu guda, suka shanye.  Shi ke nan ya zauna a haka, har ya girma.  Daga kan dan gadonsa ba ya iya fita ko ina, sai dai am fita da shi.  Iyayensa suka yi bakin ciki kwarai, suka hakura.

            Wata rana iyayen Iliya sun tafi gona, ba kowa gidan sai shi kadai, kan gadonsa, yana ta tunanin yadda duniya ta ke, yan kulle-kullen abubuwan da zai yi, da yana da kafafu.  Kwanfa, sai ya ji an yi sallama, Salamu alaikum, salamu alaikum!    Sai Iliya ya amsa, Alaikas salamu.  Kowane ne ya shigo!    Sai ga wadansu mutane su uku, suna sanye da tufafi irin na aLarabawa, sun yi shigar alhazai.  Ko wannensu yana rike da doguwar tasbaha, yana ja.  Suka zauna.  Iliya ya yi musu maraba, suka amsa masa da murna.

            Iliya ya dubi mutanen nan da kyau, ya ga ba irin mutanen da ya saba gani ba ne.  Sai ya zaci ko irin mutanen nan ne da ya kan ji ana cewa suna bi gari gari suna wa azi.

            Malaman nan suka tambayi Iliya ko akwai wani abinci ya ba su su ci.  Iliya ya ce, Ba za a rasa ba, ku duba, inda duk kuka gani, ku dauka ku ci.  Ba ni iya tashi, balle in duba muku." Suka tambaye shi abin da ya same shi.  Ya ce, "Wurin nan da kuka ganni, tun da aka haife ni a nan ni ke.  Ban taba leka ko kofar gida ba.  Ko bayan daki ma sai an kai ni.



            Allah Sarkin jin kai!  Ashe malaman nan ba mutane ba ne, Mala iku ne aka aiko su jarraba Iliya, kuma su warkad da shi.  Sai dayansu ya debo ruwa cikin kwarya, ya yi addu a ya ba Iliya, ya ce, Wanke fuskarka da jikinka.    Iliya ya karba da hannunsa mai lafiyar, ya wanwanke.  Kamar kiftawar ido, sai ya ga jikinsa sarai, kamar ba nasa ba.  Kafafunsa da hannunsa shanyayyu duk sun mike, har im ba wanda ya sani ba, ba wanda zai zaci Iliya ya taba tawaya.

            Ya miko kafafuwansa kasa daga kan gado, ya gurfana gaban malaman nan, ya yi musu godiya.  Cikin murna ya je ya dauko madara, ya durkusa ya ba su.  Wannan ya kurba, ya mika wa wancan, har ya kewaya dukansu.  Sa an nan babbansu ya mika wa Iliya ya ce, Kai kuma sha, Iliya.    Iliya ya karba ya sha.  Jim kadan, daya daga cikin malaman ya ce wa Iliya Yaya ka ke jin jikinka yanzu?    Iliya yace, Na ji wani sabon karfi ya zo mini, har ina jin kamar kasa ba za ta iya daukata ba.

            Sai babbansu ya ce wa Iliya ya kara kurban madarar.  Bayan da Iliya ya kara sham madaran, sai malamin ya ce, To, Iliya, ka gaskata Tsarkakken Sarki, ka bi umurninsa, ka yi dukan abin da ya hore ka da shi,  Za ka fifita daga dukan mutanen kasan nan.  Za a ji sunanka ko ina cikin duniya.  Kome wahala, kome hatsari, kada ka yanke kauna ga Ubangijinka.  Kuma wannan abu tabbatacce ne, kuma rubutacce ne, cewa ba za ka mutu a wurin yaki ba, kome tsananinsa.

            Duk cikin duniyan nan ba wanda zai sami nasara a kanka, sai mutum daya tak, ana kiransa Wargaji, za ka hadu da shi, amma ko kadan kada ka yi fada da shi.  Yanzu ka dauki aniya, ka tafi Birnin Kib, kada ka ce za ka tsaya ka bata karfinka a gona, ko a lambu, ko a daji.

            Suna kare magana, sai Iliya ya nemi malaman nan ya rasa.  Ya dimauta, hankalinsa ya tashi, domin bai san dalilin da za shi Birnin Kib ba.  Ga shi kuwa malaman sun bace balle ya tambaye su.  Ya ga abu duk kamar cikin mafarki.  Zuwa can, hankalinsa ya dawo, ya yi godiya ga Ubangiji. Ya nufi gona wurin iyayensa.  Ya tarad da su, sun yi aiki, sun gaji, suna kwance, suna ta sharar barci.  Ya yi sallama, ba su farka ba.  Sai ya matsa, ya dauki gatari, ya dubi wani katon reshen kuka ya sare.  Cikin inuwarsa kuwa iyayensa ke kwance.  Da karar saran, da ta faduwar itacen duka ba su sa iyayen Iliya sun farka daga barcinsu ba.  Sai ya dauki sauran gaturansu ya kafe su a jikin itace,  ya koma wani wuri ya boye, yana dariya,  Ya ce a ransa,  In sun farka za su yi aiki, ba su ga gaturansu ba, ai sa nema.

            Can da zafin rana ya buge su, sai suka farka firgigi.  Suka duba sama, suka ga an sare reshen kukar, suka yi mamaki.  Don sun tabbata sare wannan ice cikin dan lokaci haka, sai dai kamar katta goma.  Suka duba ba su ga kowa ba, sai gaturansu kafe ga itace.  Suka yi, suka yi, su cire, suka kasa.  Da Iliya ya ga sun kasa sai ya fito yana dariya, ya sa hannu daya ya acire musu gaturansu.



            Garin Iliya haka, sai suka bar mamakin sare ice, da na kafe gatura.  Suka koma mamakin Iliya.  Duk wuri ya yi tsit, da uwar Iliya da ubansa suka kafa masa ido kuri, amma ba su gane shi ba sosai.  Don kuwa sun san irin halin da suka bar shi a gida.  Uban dai sai dubansa ya ke daga kasa har sama.  Can suka gane dai dansu ne, Iliya. Ya zama haka.  Sai uban ya ta da kansa sama, ya yi wa Allah godiya.

            Saboda mamaki iyayen Iliya suka kasa ce masa kome.  Sai Iliya ya durkusa gabansu, ya ba su dukan labarin abin da ya faru.  Ya kuma nuna musu zama irin nasu ba zai yi masa ba.  Ya ce an umurce shi da ya tafi Birnin Kib.

            Iyayensa suka yi ta murna ganin dansu ya mike, amma kuma suka yi juyayin, da bakin ciki saboda rabuwa da shi.  Iliya ya sake durkusawa, ya rausasa murya, ya be iyayensa hakuri, ya yi musu magana mai dadi, yadda ransu zai yi dan sanyi.  Sa an nan ya roke su gafara, ya yi ban kwana.  Tun daga nan wurin ya kama hanya zuwa Birnin Kib.

            Yana ckin tafiya, sai ya fgamu da wani mutum yana jaye da dan dukushin doki.  Iliya ya tambayi mutumin ko zai sayar masa da shi.  Abu kamar wasa, mai dukushi ya yarda, suka yi ciniki.  Iliya ya sani ba ya da kudi, amma don kada a kure shi, sai ya sa hannu kawai cikin aljihu, kamar da wasa, sai ya ji kudi a ciki.  Ya dauko ya biya doki.  Daga nan sai wani tunani ya zo masa, ya ga ya fi kyau ya koma gida, ya kiwata dokin, sa an nan ya sake fita.  Sai ya juya ya koma gida.
            Iliya ya sa wa dokinsa suna Kwalele.  Ya shiga kiwonsa yana horonsa yadda zai saba da wahala, da jure yunwa.  Kafin wata uku dukushi ya cika, ya zama ingarma, wanda ba kamarsa a nan kurkusa.  Ya zama sai harbin iska ya ke yi aturke, har ya fi ubangijinsa kosawa a tafi.

No comments:

Post a Comment